KUZO KUJI SISTERS....
Kyawun ki, Ya Zamto Abokin Fa'da Agareki!
Ki 'dauki kyawun ki a matsayin abokin fa'da agareki,
Domin daga lokacin da, kika daukeshi a matsayin amininki to daga lokacin kika dauki hanyar halakar da kankiiii.
Tabbas kyawu wani ni'imace/baiwa da Allah (t) yake Azurta bawa dashi.
Amma ki sani ba kyawun fuska ake bukata ba.
Kyawun zuciya da kyakkyawar dabi'u ake bukata ga 'ya mace.
Kada ki dauka Allah (t) ya azurtaki da kyau ne, domin ya zamto abin ado agareki.
KYAWU SHINE ABU MAFI HATSARI GA 'YA MACE......
Namiji da Kyakkyawar mace tamkar mayen 'karfe ne, da karfee!
Daga lokacin da namiji yayi ido biyu 2 da kyakkyawar mace to a lokacin zai dauki damarar samun kusanci agareta.
Kuma ba zai ta6a kasancewa duk halin Maza sun zamto daya ba,
Dole zaki kasance mai kar6ar ba'kunci mazaje kala-kala arayuwarki na banza dana kirki.
Kisani indai namiji ya sawa zuciyarshi zai samu abu agurin 'ya mace to gaskiya ba karamin kariya kika samu gurin allah (t) kika tsallake tarkon shi ba.
Kisani Karya takanyi tasiri Azuciyar mutum fiye da gaskiya sai dai ita karya takaitaccen lokaci gareta, daga karshe gaskiya take bayyana sannan tayi aiki.
To kuma acikin kankanen lokacin za,ai amfani da karya/yaudara a 6ata rayuwarki.
Bance kada ki nuna kyawun da allah yayi maki bane
Amma kisani komai akwai muhallin da yake aiki.
Allah ya bamu ikon Tafiyar da rayuwar mu, cikin tsari da kyakkyawar dabi'u.
--Aljawad jibrin kagara (Dan jaridah)
--13-01-2021