Abubuwan da muslumci ya tanada wurin neman Aure !!!



_ A lokacin neman aure, ka gujewa aikata al'adu, musamman wa'yanda basuda asali a addini,domin yin al'adu a neman aure yana da tasiri wajen haifar da matsaloli a zaman aure.

_ Tun a neman aure ake fara gina zamantakewa tsakanin ma'aurata, yanayin yadda aka nemi auren mace, ta irin wannan yanayin ne zaku rayu da ita inka aureta fa. Don haka yanada kyau ka tsare neman aure bisa irin tsarin da kakeso ka zauna da matar bayan ka aureta.


Kamar yadda namiji zaya iya ganin mace yace yana sonta, haka nan ya halasta mace in taga saurayin daya dace da ita, kuma taji tana sonsa, tabayyana masa cewa tana sonshi, ta hanya mafi dacewa, amma ya dace mace tayi la'akari da mutuncinta wajen yin hakan.


         Idan namiji zaya furta bukatar auren mace, hakan shiya dace a al'ada da Sunnah, domin manzon Allah (saw) shiya nemi auren ummu salama da kansa ( don tausayin halin da take ciki a lokacin).


Haka kuma idan mace ta nuna bukatar aure ga wani kamilin namiji, hakan yayi dai_dai da sunnah, ya kuma dace da ita, domin sayyida Khadija (as) ta nuna kaunar auren manzon Allah (saw), haka idan iyaye sukaga dacewar su nema wa 'yarsu aure da wani mutumin kirki, shima hakan ya dace da sunnah, domin iyayen sayyida Ameenah sune suka gabatar da bukatar aurar da'yarsu ga sayyid Abdallah (as) mahaifin manzon Allah(saw). Don haka kowane tsakanin mace da namiji yanada damar ya nuna bukatar aure ga wanda yaga ya dace dashi, amma dai yafi zama dai_dai namiji ya nemi mace da aure.



Ana bayar da aure bisa sharadin : 

1_ wurin zama (gida)

2_ ciyarwa

3_ Tunatarwa

4_ kula da lafiya

5_ kula da ilimi


Abisa wadannan ake gina aure tun farko, kuma idan har mutum baya iya sauke daya daga cikin wa'yannan nauye_nauyen, to ya halasta a hanashi mace, (saidai idan har wani ne zaya dauke masa).



Allah ya bamu ikon kiyaye dokokinsa acikin kowane aiki namu


✍️ _ zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post