A ranar Asabar 6/1/2018 labari ya iske ‘yan uwa, daga dangi da makusanta Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky, cewa jikinsa ya tashi sosai har ma yana fuskantar barazanar shanyewar barin jiki! Wannan yasa hankalin ‘yan uwa ya tashi, a cikin wannan daren na ranar 6/1/2018 aka rika gudanar da Muzaharori a wasu garuruwa, musamman a Bauchi, Kano, Zariya da sauransu.
An cigaba da Muzaharar kira ga gwamnati ta saki Shaikh Zakzaky domin ya je ya nema ma kansa lafiya a safiyar Lahadi, 7/8/2018 a kusan dukkan birane da kauyukan kasar nan, ciki har da Zariya da Kaduna.
A wannan ranar ta Lahadi ‘yan sanda suka bude wuta a kan masu Muzaharar a Kaduna, inda suka jikkata mutane biyar, har biyu daga cikinsu suka samu Shahada; Shahid Muhammad Auwal Kakuri da Shahid Abdulmalik Sani. Wadanda Shaikh Abdullahi Zango ya jagoranci yi musu janaza washe-gari Litini a Kaduna.
Litini 8/1/2018 ne ‘yan uwa suka fara cincirindon shiga Abuja don fara gudanar da Muzaharorin Kira a saki Shaikh Zakzaky na sai baba-ta-gani. A wannan ranar ‘yan sanda sun budewa masu muzaharar wuta, inda suka kama wasu yan uwa, kuma suka jikkata da dama, amma ba a samu Shahidi ba.
Ranar Talata 9/1/2018 ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky sun kuma fitowa Muzaharar kira a sake shi a tsakiyar garin Abuja. A rannan ma ‘yan sandan sun kuma bude wuta a kan ‘yan uwa, inda suka jikkata da dama, suka kama ‘yan uwa masu yawa. A wannan ranar ne ‘yan sanda suka harbi Shaikh Qasim Umar Sokoto a cinyarsa, wanda bayan jinya da ya sha na tsawon kimanin kusan wata guda, ya yi Shahada a ranar 5/2/2017.
Washe-gari Laraba 10/1/2018 ‘yan uwa suka kuma fitowa don Muzaharar Free Zakzaky a Abuja din. Rannan ma jami’an tsaron ‘yan sanda suka kuma bude wuta a kan masu Muzaharar, inda suka datse gaba da bayan Muzaharar, suka rika amfani da wasu mashina suna ratsa cikin ‘yan uwa suna watsa musu Tiyagas, bayan sun galabaitar da ‘yan uwa, sai suka fara harbi da harsasai masu rai, inda nan take suka kashe mutum biyu; Shahid Aminu Ibrahim Gashua da kuma Shahid Usman Dunari, wanda shi sai bayan kwanaki 9 da Shahadarsa sannan ‘yan sanda suka ba da gawarsa akai mata janaza. Sun kuma jikkata gomomi a yayin da suka kama ‘yan uwa masu yawa.
Alhamis 11/1/2018 aka cigaba da Muzaharar, sai dai an tashi lafiya a wannan ranar. Amma a ranar Juma’a 12/1/2018 an yi Muzaharar ne daga Babban masallacin kasa na Abuja, inda ‘yan sanda suka harba Tiyagas a kan masu muzaharar.
Tun daga wannan lokacin aka fara muzaharar kullum a garin Abuja don fafutukar ganin an saki Jagoran Harkar Musulunci daga haramtacciyar tsarewar da gwamnatin Buhari ke masa. Yanzu haka Muzaharar ta kullum, wanda ake kira Fafutukar Abuja ko ‘Abuja Struggle’ a Turance ta cika shekaru uku ba tare da yankewa ba.
Sai dai kuma, yana daga cikin natijojin wannan waki’o’in na mako guda a jere yadda ya zama a ranar Asabar 13/1/2018 Gwamnatin Nijeriya ta yarda ta nuna Shaikh Ibraheem Zakzaky a Talabijin a karon farko tun bayan kama shi da ta yi, inda ya yi bayani a kan ‘yanayin halin da yake ciki, ya kuma yi godiya ga ‘yan al'ummar da suke masa addu’a. Nuna Shaikh Zakzaky a wannan lokacin ya kwantar da hankalin masoyansa da dama, a yayin da makiyansa suka shiga cikin tsananin damuwar ganin tabbacin cewa yana nan a raye.
— Daga littafin MUHIMMAN RANEKU A TARIHIN HARKAR MUSULUNCI, Na Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).