Ya Ammar! Ma'aunin gane inda gaskiya take shine; duk inda ka ga Ali yayi, ka bishi, don bazai kaika ga halaka ba... — Inji Manzon Allah (S)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Ammar Bn Yasir (R. A) bawan Allah ne salihi wanda ya kasance cikin na farko-farkon wadanda suka amsa kiran Manzon Allah (S. A. W. W) yayin da aka aiko shi a matsayin Manzo. 



An azabtar da shi tare da mahaifansa kan wannan addini amma hakan bai sa sun juya baya ba , kuma mahaifiyarsa ce farkon shahidai cikin da'awar Manzon Allah (S. A. W. W). Saboda ganin irin azabar da suke sha wata rana Annabi (S. A. W. W) yake ce musu, 


" KUYI HAQURI IYALAN YASEER, LALLE MAKOMARKU ITA CE ALJANNAH ."


Ya kasance Sahabi mai biyayya ga Annabi (S. A. W. W) cikin sauqi ko qunci, kuma bai taba saba masa ba har suka rabu lafiya. 


Kafin wafatin nasa (S. A. W. W) yayi masa wasiyya wacce za mu ganta biye cikin wannan hadisi. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


Ya zo cikin Manaqib na Ibn Shaharan Shaubi Abu 'Dalib Al-Harawiy da isnadinsa daga Alqamata da Abu Ayuba cewa yayin da aka saukar, " ALIF LAAMEEM. SHIN MUTANE NA TSAMMANIN....... " (aya). 


Sai Annabi (S. A. W. W) ya cewa Ammar, 


27- قب، المناقب لابن شهرآشوب أَبُو طَالِبٍ الْهَرَوِيُّ بِإِسْنَادِهِ عَنْ عَلْقَمَةَ وَ أَبِي أَيُّوبَ‏ أَنَّهُ لَمَّا نَزَلَ‏ الم أَ حَسِبَ النَّاسُ‏ الْآيَاتِ قَالَ النَّبِيُّ ص لِعَمَّارٍ


" DA SANNU RIGINGIMU ZA SU KASANCE A BAYANA, HAR SAI TAKOBI NE ZAI RARRABE ABINDA KE TSAKANINSU, KUMA HAR SAI SASHENSU YA YAQI SASHE, KUMA HAR SAI SASHENSU YA BARRANTA DAGA SASHE. 


TO, IDAN KAGA HAKA (ta faru), TO, NA HORE KA DA (yin riqo) DA WANNAN DA KE BANGAREN DAMANA ALIYU BN ABIY 'DALIB (A. S). KO DA ACE DUKKAN MUTANE ZA SU TARE A TAFKI GUDA 'DAYA, ALI MA YA TARE A WANI TAFI (shi kadai), TO, KA TARE A TAFKIN DA ALIYU YAKE KA KEFE DAGA (dukkan sauran) MUTANE. 


YAA AMMAR ! LALLE ALIYU BA ZAI KAUTAR DAKAI DAGA SHIRIYA BA, KUMA BA ZAI KAIKA ZUWA RIDDA BA. 


YAA AMMAR ! YIWA ALIYU BIYAYYA YIN BIYAYYA CE GARE NI, KUMA YIN BIYAYYA GARE NI YIN BIYAYYA CE GA ALLAH. 


" إِنَّهُ سَيَكُونُ بَعْدِي هَنَاتٌ حَتَّى يَخْتَلِفَ السَّيْفَ فِيمَا بَيْنَهُمْ وَ حَتَّى يَقْتُلَ بَعْضُهُمْ بَعْضاً وَ حَتَّى يَتَبَرَّأَ بَعْضُهُمْ مِنْ بَعْضٍ فَإِذَا رَأَيْتَ ذَلِكَ فَعَلَيْكَ بِهَذَا الْأَصْلَعِ عَنْ يَمِينِي عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع فَإِنْ سَلَكَ النَّاسُ كُلُّهُمْ وَادِياً وَ سَلَكَ عَلِيٌّ وَادِياً فَاسْلُكْ وَادِيَ عَلِيٍّ وَ خَلِّ عَنِ النَّاسِ يَا عَمَّارُ إِنَّ عَلِيّاً لَا يَرُدُّكَ عَنْ هُدًى وَ لَا يَرُدُّكَ إِلَى رَدًى يَا عَمَّارُ طَاعَةُ عَلِيٍّ طَاعَتِي وَ طَاعَتِي طَاعَةُ اللَّهِ‏ ."[52].



(1) تفسير الإمام: 185- 186.


(2) المناقب (مناقب آل أبي طالب لابن شهرآشوب السروى) ج 3 ص 203، و في مطبوعة الكمبانيّ شى رمز العيّاشيّ و هو سهو


Ammar ya bi wannan wasiyya wacce Annabi (S. A. W. W) yayi masa, domin a lokacin da akayi zabe a Saqeefah kuma aka nemi mubaya'arsa ga wanda aka zaba ya qi yayi, har yake ce musu, 


" NI BA ZANYI MUBAYA'A GA WANDA ANNABI BAI CE AYI MASA MUBAYA'A BA, BAI'AR DA KE KANMU ITA CE TA WANDA ANNABI (S. A. W. W) YACE MU BI SHI ."


Ammar ya kasance tare da Imam Ali (A. S) cikin komai nasa, bai taba rabuwa da shi cikin wahala ko sauqi, har zuwa ranar yaqin Siffin yana dauke da tuta cikin rundunar Imam Ali (A. S), kuma azzalumar qunqiya ta Mu'awiyyah ta kashe shi. 


Ganin wannan kisa da aka yiwa Ammar (R. A) ta qara tabbatarwa mutane cewa Imam Ali (A. S) ne ke kan gaskiya da wadanda ke tare da shi. 


YAA ALLAH KA YABBATAR DAMU KAN WANNAN WILAYA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


30th December, 2020/ 16th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post