WAYEWA KO KAUYANCI: Sam babu wayewa a cikin sabawa mahalicci !!!



Tabbas hausawa sunyi gaskiya, da sukace BABU WAHALALLE SAI ME KWADAYI babu ko tantama akan hakan.


Inaso nadanyi magana ne akan wayewar da muke tunanin wayewa ce a garemu a yanzu, dayawan mutane suna ganin wayewa a matsayin lalacewa ne, kuma bazanga laifinsu ba, tabbas a yadda muka maida wayewa yanzu to lallai lalacewa ce da ci baya, kuma ni a tunanina ai dama duk mutumen da yake da addini ba'a fada masa wayewa ko?, Dan uwa/'yar uwa wayewar addini itace wayewa malamai, a tambayeka bangaren addininka ajika babu wata matsala, babu abinda za'a boye maka acikinsa, a taboka ban garen boko ma ajika babu damuwa, malam shine wayewa. Bawai ka maida boko shine kadai ilimi ba, wato saboda shi idan ka gama kana saran samun aiki, kudi su rika shigo maka, bari na tuna maka, karatun boko a iya nan zaya anfaneka, indai ba kayi anfani da ilimin wurin neman lahirarka ba, shi kuwa ilimin addini guziri ne har kiyama.


Amma a yanzu mun maida hakan kamar kauyanci ma, wanda yayi zurfi bangaren addini ko wanda yake karatu a Bangaren addini shi mukewa kallon bakauye, wanda bai waye ba.


 Mun maida bokon wata abar alfahari, wanda hakan ne yake tasiri ga zukatanmu, wurin lalacewar tarbiyyarmu, tun daga shigarmu har dabi'unmu, wanda wannan ci bayane garemu, zaka samu masu ilimin addini acikinmu sunyi karanci, kuma munada baukatarsu amma kowa yana tsoron yayi ace masa bai wayeba, wasu kuma sunada ilimin amma suna tsoron nunawa, suna gani ana ba dai_dai ba amma basa iya magana, don kar ace yayi yawa.


Mun zabi mu bayyana ilimin bokonmu a ko'ina amma muna tsoron nuna addininmu, kaiconmu da irin wannan WAYEWAR, da muke ganin kamar cigaba ne garemu, tabbas ci gaba ne amma na mai ginar rijiya.


Tabbas munada karancin masu ilimin bokon, kuma suma munada bukatar su sosaema, amma bawai shikenan komai namu ya koma boko ba, mu rika tsoron addininmu saboda shi bai wayeba, saboda shi baice muci haram ba ko mu aikata ta, saboda shi baice mu hole rayuwarmu ta hanyar da Bata dace ba, saboda shi baice mu rika gaisawa da mata ba, saboda shi baice mu rika cakudayya da mata ko maza ba, saboda shi baice mu rika nuna tsiraicinmu ba, saboda shi baice mu rika ma'amala da kowa yadda muka gadama ba, eh mana!! ai wannan shine muke ganin kamar shine idan mutum yanayi to ya gama wayewa, bayan duk abinda Allah zayace ka daina to yasan zaka iya rayuwa ahakan ne, don Allah baya dorawa bawa abinda baya iyawa. 


Amma muna ganin kauyencin addini a yanzu, saboda shi ya suturtamu ya nuna mana kame kanmu daga duk abinda bai dace ba.


Allah ya wadaran wayewar duk da zata saka na sabawa Allah kona bijirewa dokokin sa.


✍️ Zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post