Wasiyyar Ameerul-Muminina Imam Ali (As) ga ɗansa Ibn Hanafiyyah !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


CIKAR KAMALAR MUTUM IRI BIYU CE 


Duk mai neman shiriya da kuma ilimi na haqiqa za ka tarar da shi ba yassauci wajen saurare ko karanta zantuka da suka fito daga Imam Ali (A. S), domin duk abinda ka ji daga gare shi in kaga dama za ka iya cewa daga Manzon Allah (S. A. W. W). 


Ya zo cikin KHISAAL, inda Imam (A. S) ke yin wasiyya ga dansa Muhammad Bn Hannafiyyah, ga wasiyyar nan kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


الخصال أَبِي عَنْ عَلِيٍّ عَنْ أَبِيهِ عَنْ حَمَّادِ بْنِ عِيسَى عَمَّنْ ذَكَرَهُ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع فِي وَصِيَّتِهِ لِابْنِهِ مُحَمَّدِ بْنِ الْحَنَفِيَّةِ :



Daga Aliyu, daga babansa, daga Hammad Bn Isah, daga wanda ya ambata masa, daga Abu Abdullahi (A. S) yace, Ameerul-Muminina (A. S) ya fada cikin wasiyyarsa ga dansa Muhammad Bn Hannafiyyah, 


وَ اعْلَمْ أَنَّ مُرُوءَةَ الْمَرْءِ الْمُسْلِمِ مُرُوءَتَانِ مُرُوءَةٌ فِي حَضَرٍ وَ مُرُوءَةٌ فِي سَفَرٍ أَمَّا مُرُوءةُ الْحَضَرِ فَقِرَاءَةُ الْقُرْآنِ وَ مُجَالَسَةُ الْعُلَمَاءِ وَ النَّظَرُ فِي الْفِقْهِ وَ الْمُحَافَظَةُ عَلَى الصَّلَاةِ فِي الْجَمَاعَاتِ وَ أَمَّا مُرُوءَةُ السَّفَرِ فَبَذْلُ الزَّادِ وَ قِلَّةُ الْخِلَافِ عَلَى مَنْ صَحِبَكَ وَ كَثْرَةُ ذِكْرِ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كُلِّ مَصْعَدٍ وَ مَهْبَطٍ وَ نُزُولٍ وَ قِيَامٍ وَ قُعُودٍ


" KUMA KA SANI, LALLE CIKAR KAMALAR MUTUM MUSULMI IRI BIYU CE, AKWAI KAMALA YAYIN ZAMAN GIDA, DA KUMA KAMALA A HALIN TAFIYA. 


AMMA CIKAR KAMALA A HALIN ZAMAN GIDA SHINE;


-KARATUN ALQUR'ANI, 


-DA ZAMA DA MALAMAI, 


-DA YIN NAZARI CIKIN (ilimin) FIQHU, 


-DA KIYAYEWA AKAN SALLAH CIKIN JAMA'AH.


AMMA CIKAR KAMALA A HALIN TAFIYA KUWA SHINE; 


-YIN KYAKKYAWAN GUZURI, 


-DA QARANSA SABAWA GA WANDA KUKE TAFIYA TARE, 


-DA KUMA YAWAITA AMBATON ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN KOWANNE BIGIRE, DA GURIN DA AKA HAU, DA GURIN DA AKA SAUKA, DA KUMA HALIN TSAYUWA KO A ZAUNE ."


Wannan wasiyya ce wacce ta shafi kowanne mumini ya kiyayeta ko ya aikata don samun kamala/mutuntaka. Babu wannan zai kiyaye wannan ba tare da ya sami yardar Allah ba. 


Sannan kuma duk wanda ya damfaru da wannan wasiyya zai zama mutum mai mutunci da karama cikin al'umma. 


ALLAH YASA MU DACE WAJEN AIKATA WANNAN WASIYYAH. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


          (08137925034)


8th December, 2020/ 23rd Rabi'us-Sani, 1442.


-

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post