✍️Auwal M Tukur
A ranar Juma'ar nan 4/12/2020 ne, da ta gabata. Wani abu ya faru da yan uwa Musulim almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na garin Babban Rami. Dake cikin karamar hukumar Mashegu dake a gundumar mulkin Masarautar Kontagora ta jihar Neja. Inda Dagacin Yamma na garin na Babban Rami, ya tarar da Wakilin Yan uwa Musulim almajiran Sheikh Zakzaky na garin, yana tsaka da Free-Huduba a Masallacin Sabuwar kasuwa ya rufe shi da *_Duka_*. Tare da kwace Abin magana (Speaker), daga hannun wakilin Yan uwa Musulim almajiran Sheikh Zakzaky.
In da hakan ta sa wakilin Yan uwan dakatar da jawabin sa. Tare da yin tinanin _to meke faruwa ne?,_ Dagacin yayi Wannan aikin. Inda a nan al'ummar gari da ke sauraron jawabin suka fara tofi. Allah ya wadaran wannan aikin da Dagacin ya aikata. Tare da nuna rashin goyon bayan su akan yin hakan. Inda Kuma Dagacin yaci gaba da zage-zage akan Yan uwan almajiran Sheikh Zakzaky. Tare da cewa duk sai yayi Maganin su.
Sai dai bayan hakan ta faru, Yan uwa sunyi kokarin binciken ko menene ya faru da har Dagacin yayi Wannan aika aikar! Alhmadulillah majiyar mu ta shaida mana cewa wasu mutane Uku ne sukaje sukayi wannan kullin, domin ganin an hana yin Free-Hudubar da aka saba gabatarwa a garin sama da Shekaru 28 a garin. Sai dai Mun sakaya sunan su saboda wasu dalilai, Wanda idan bukatar haka ta taso zamu bayyana su.
Sai dai wannan abin ya biyo bayan wani jawabi na jan hankali ne da wakilin Yan uwan almajiran Sheikh Zakzaky na garin Babban Rami, Malam Muhammad Tukur yayi. A wata ranar Juma'ar 27/11/2020. Akan irin bakin Zalinci da Yan Bangan garin suke yiwa al'ummar garin tare da hadin gwuywar wadancen mutanen uku da shi kansa Dagacin da kuna Division of Police na garin Babban Rami suke yi. In da a cikin jawabin Malamin ya bayyana irin gallazawar da Yan Bangan suke yiwa al'ummar garin. Ta fuskacin Sintirin da suke yi na dare a garin.
Inda a garin na Babban Rami an saka dokar hana fita daga karfe 10:00pm na dare zuwa wayewar gari. Saboda halin rashin tsaro da yankin yake ciki. Daga masu garkuwa da mutane, Amma yan bangan suka fara fitowa ne tin karfe 9:30pm a Mai makon karfe 10:00pm Daren. Sukan Fara tare ababen hawa da masu tafiya a kafa. Su Kai su police station na garin a kulle su day safe suyi belin kansu a kan kudi 2000, 3000,4000, ko 5000, 20000, 30000 Kai har dubu 40000 sun karba. Tare da yiwa mutun dukan tsiya kafin su Kai shi police station. Idan kuma mutun ta gudu sukan bishi a guje har cikin gidan mutane. Idan Basu samu nasarar kamashi ba, sukan kama Mai gidan ne su tafi da shi, ba tare da yin la'akari da kowaye ba.
To sai wakilin Yan uwan Malam Muhammad Tukur yaja hankalin su kan cewa hakan bai daceba. Domin suna hadawa da zalinci a cikin al'amarin su. Ya cigaba da cewa "ba yadda za'a azzalumi yace zai yaki zalinci domin kuwa shima zalincin zai yi" Jin Wannan nasihar da suka ji Malamin yayi shine yasa suka ce suka samu Dagacin suka shirya Masa karairayi daban daban domin ganin an hana cigaba da gabatar da Free-Huduba a garin. Wanda tin bayan waki'ar Zariya sunyi kokarin ganin hana cigaban Tunatarwar da ake duk sati a garin.
Wannan shine halinda ake ciki a halin yanzu a garin.