@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Ba ayi ba kuma ba za a taba yin wani mummunan aiki wanda muninsa ya girgiza Al-Arshi kamar abinda akayi ranar 12-12-2015 a garin Zarian Nigeria na kisan gilla kan rayukan raunana sama da 1000 ba.
Shekaru 200 da wani abu da suka wuce anzo yin makamancin wannan wanda aka karkashe almajiran Sheikh Usman Bn Fodiyo don rusa daular muslimci da ya kafa/shimfida bisa qoqarin maye shi da tsarin turawan Ingila.
Kamanceceniyar wadannan ta'addanci guda biyu shine, 'yan ta'addan da suka yi wadannan ta'addancin masu riya cewa su musulmi ne, kuma dukkansu sunyi aiki ne wanda iyayensu Yahudu suka sa su bayan tarbiyyantarwar da tayi musu.
Idan muka lura da kyau za muga cewa sarakunan wancan zamani musulmai ne, sai sun cakuda muslimcin nasu ne da bori da tsafi. Su ma shugannin wannan zamani musulmai ne, sai dai Mushirikai ne masu hada tsarin Allah dana waninsa, ko kuma wadanda suka canza tsarin Allah suka maye shi dana kafirci.
Bambancin da ke tsakaninsu kuma shine, duk irin ta'addancin dana zamanin Sheikh Usman Bn Fodiyo suka yi basu qona Gawa da ranta ko bayan ranta ba, sannan basu binne gawa ba tare da anyi mata sallah ba, wannan aikin nasu yayi daidai da ayyukan jahiliyya kafin zuwan muslimci, domin sun bisne mutane da rayukansu .
Gwamnatin Buhari (L. A) ce ta aiwatar da wannan ta'addanci wanda Yahudawa suka ba shi aiki ta hannun Yariman Saudiyyah kamar yadda ya ambata da bakinsa mai wari ! Sun fake da qaryar wai an tarewa shugaban Sojijin Nigeria hanya ne wanda hakan ya basu damar aiwatar da abinda suka aikata, alhali aikin da suka yi ya saba dokar qasar da suka yi imani da ita.
Abinda kuma suka kasa sani da farko shine, duk abinda za suyi ba za su iya kawar da gwagwarmayar muslimci wacce Sayyid Zakzaky (H) ke jagoranta ba, amma a yanzu sun san haka tunda sun gani da idonsu.
Sannan kuma wannan ta'addanci nasu ya munana qasar a idon duniya da kuma sanya ta cikin baqin kundin tarihi, domin sun aikata wannan mummunan aiki ne a daidai lokacin da ake da hukuma mai kula da kare haqqin Bil-Adama wanda a idonta akayi domin tayi bincike kuma ta tabbatar da cewa an keta alfarma dan Adam.
Malamai da sarakuna sun gani da idonsu, amma maimakon su qyamaci wannan mummunan aiki sai ya kasance sunyi farin ciki da ganin daidai din abinda aka aikata ga 'yan Shi'ah, suna masu cewa su suka jawowa kansu.
Sun qirqiri qarya wai cewa 'yan Shi'ah suna bautar Gunki ne kuma suna zagin Sahabbai da matan Annabi (S. A. W. W).
Da shike ba tunani ne dasu ba, sannan son duniya a abin cikinta ya rufe musu ido sun kasa gane cewa ita wannan kafirar Gwamnatin Nigeria tace ba ruwanta da addini, domin kowa zai iya bautawa abinda yaga dama ba tare da an tsangwamesu ba.
Wannan goyon baya nasu ga zalunci ne ya sanya wannan qasa cikin qunci, firgici, da matsanancin rayuwa wanda babu lokacin fita daga cikinsa matuqar ana tsare da wannan bawan Allah Sayyid Zakzaky (H).
Yau shekaru biyar (5) kenan cif da kwana 57 a lissafi qamariyya ana tsare da Sayyid (H) alhali koto ta bada umarnin a sake shi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08137925034)
12th December, 2020/ 27th Rabi'us-Sani, 1442.
FREE SAYYID ZAKZAKY
(H) !!!