Ana sanar da dukkanin Al'ummar Musulumi Ranar Lahadi 13\12\2020 da Misalin Karfe 7:00ns za a gabatar da Addu'a na cika Shekara daya da Rasuwar Marigariya Malama Lubabatu Ladan a kofar Gidan Alhaji Ahmad dake filin sukuwa a nan cikin garin Jos.
Hujjatul Islam Sheikh Adamu Tsoho Ahmad ne ya jagoranci Jana'izar Marigariyar wanda ta sami Sheda daga bakinsa mai Albarka Inda yake cewa Malam Luba ta kasance tanawa Addini hidima ne tun daga Kuruciyarta har zuwa Lokacin da tayi Aure Bamu Santa da wani abu wanda ba Alkhairi ko hidimawa Addiniba.
Rashin Hajiya Luba a garin Jos mun shiga cikin jimami da dimuwa,
An binneta a Makabartar Narkuta kusa da Muslimah Diyar Sheikh Adamu Tsoho Ahmad.
Daga karshe muna mata fatan Allah ya yafe mata ya sanyata daga cikin bayinsa Salihai.
Allah ya gaggauta fito mana da Malana Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) daga hanun Azzalumai
Daga Almustapha A Abdullahi Jos