@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SAQO MAI 'DAUKE DA ILIMI DA HIKIMA
Filinsa ne (A. S) wanda kowa ya san shi wajen hikima da isar da saqo mai kama qwaqwalwa ga dukkan wanda yaji ko ya karanta saqonsa.
Ya aika wannan saqo ne ta hannun Sahabinsa kuma wanda ya miqa wilayarsa gare shi, wato Muhammad Bn Abubakar Bn Abu Quhafata.
11- ما، الأمالي للشيخ الطوسي فِيمَا كَتَبَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع إِلَى أَهْلِ مِصْرَ مَعَ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي بَكْرٍ
Ya zo cikin Amali Lis-Shaikh 'Dusiy cikin abinda amirul-muminina (A. S) ya aika zuwa mutanen Misra tare da Muhammad Bn Abubakar, yana cewa;
عَلَيْكُمْ بِتَقْوَى اللَّهِ فَإِنَّهَا تَجْمَعُ الْخَيْرَ وَ لَا خَيْرَ غَيْرُهَا وَ يُدْرَكُ بِهَا مِنَ الْخَيْرِ مَا لَا يُدْرَكُ بِغَيْرِهَا مِنْ خَيْرِ الدُّنْيَا وَ الْآخِرَةِ قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ :
" Na hore ku da tsoron Allah, domin ita ta tattara (dukkan) alkhairori, babu wata alkhairi koma bayanta (taqawa), ana riska da ita na daga alkhairi wanda waninta ba ya riska daga alkhairorin duniya da lahira. Allah mai girma da daukaka na cewa,
" وَ قِيلَ لِلَّذِينَ اتَّقَوْا ما ذا أَنْزَلَ رَبُّكُمْ قالُوا خَيْراً لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا فِي هذِهِ الدُّنْيا حَسَنَةٌ وَ لَدارُ الْآخِرَةِ خَيْرٌ وَ لَنِعْمَ دارُ الْمُتَّقِينَ[31]
" KUMA AKA CE GA WADANDA SU KAYI TAQAWA, MENENE UBANGIJINKU YA SAUKAR ? SUKA CE, " ALKHAIRI !" TO, GA DUK WANDA YA KYAUTATA CIKIN WANNAN DUNIYA YANA DA KYAKKYAWA, KUMA GIDAN LAHIRA SHINE MAFI ALKHAIRI, KUMA MADALLA DA GIDAN MASU TAQAWA ."
اعْلَمُوا يَا عِبَادَ اللَّهِ أَنَّ الْمُؤْمِنَ مَنْ يَعْمَلُ لِثَلَاثٍ مِنَ الثَّوَابِ إِمَّا لِخَيْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ يُثِيبُهُ بِعَمَلِهِ فِي دُنْيَاهُ قَالَ اللَّهُ سُبْحَانَهُ لِإِبْرَاهِيمَ :
" Ku sani yaa ku bayin Allah ! Lalle mumini shine wanda ke yin aiki don abubuwa uku daga sakamako. Ko dai don alkhairi, to, lalle Allah zai ba shi don aikin nasa a duniya. Allah (S. W. T) ya fada game da Ibrahim (A. S),
" وَ آتَيْناهُ أَجْرَهُ فِي الدُّنْيا وَ إِنَّهُ فِي الْآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ[32] ."
" KUMA MUKA BA SHI LADANSA A CIKIN DUNIYA, KUMA LALLE SHI A LAHIRA YANA DAGA CIKIN SALIHAI (riba biyu kenan) ."
فَمَنْ عَمِلَ لِلَّهِ تَعَالَى أَعْطَاهُ أَجْرَهُ فِي الدُّنْيَا وَ الْآخِرَةِ وَ كَفَاهُ الْمُهِمَّ فِيهِمَا وَ قَدْ قَالَ اللَّهُ تَعَالَى:
(Saboda haka) " Wanda yayi aiki domin Allah (T) , to, zai ba shi ladansa a duniya da lahira, kuma ya isar masa kan muhimman (al'amransa) a cikinsu (duniya da lahira). Haqiqa Allah (T) yace,
" يا عِبادِ الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا رَبَّكُمْ لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا الْحُسْنى وَ زِيادَةٌ ."
" YAA KU BAYI WADANDA SU KAYI IMANI ! KUJI TSORON UBANGIJINKU, GA WANDA YA KYAUTATA (ayyukansa ) YANA DA KYAKKYAWAN (lada a lahira ) DA KUMA QARI (tun daga nan duniya)."
وَ الْحُسْنَى هِيَ الْجَنَّةُ وَ الزِّيَادَةُ هِيَ الدُّنْيَا وَ إِنَّ اللَّهَ تَعَالَى يُكَفِّرُ بِكُلِّ حَسَنَةٍ سَيِّئَةً قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ:
" Shi kyakkyawan ita ce Aljannah , kuma qarin ita ce duniya . Kuma lalle Allah (T) yana kankare kowanne mummunan (aiki) da kyakkyawan (da ka aikata). Allah mai girma da daukaka yace,
" إِنَّ الْحَسَناتِ يُذْهِبْنَ السَّيِّئاتِ ذلِكَ ذِكْرى لِلذَّاكِرِينَ ."[33]
" LALLE KYAWAWAN (ayyuka) NA TAFIYAR DA MUNANAN (ayyukan da kuke aikatawa), LALLE WANNAN WA'AZI NE GA GA MASU WA'AZANTUWA ."
حَتَّى إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ حُسِبَتْ لَهُمْ حَسَنَاتُهُمْ ثُمَّ أَعْطَاهُمْ بِكُلِّ وَاحِدَةٍ عَشْرَ أَمْثَالِهَا إِلَى سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ:
" To, wannan har zuwa lahira za a saka musu da kyawawan ayyukansu, sa'an nan a ba su daga kowanne daya (daga kyawawan ayyukansu) misalinsa goma zuwa ninki dari bakwai . Allah mai girma da daukaka na cewa,
" جَزاءً مِنْ رَبِّكَ عَطاءًحِساباً ."[34]
" SAKAMAKO NE DAGA UBANGIJINKA, KUMA KYAUTA MAI YAWA (a matsayin hisabin aikin ku) ."
وَ قَالَ
" Kuma yace, "
" فَأُولئِكَ لَهُمْ جَزاءُ الضِّعْفِ بِما عَمِلُوا وَ هُمْ فِي الْغُرُفاتِ آمِنُونَ ."[35]
" TO, WADANNAN GARE SU AKWAI SAKAMAKO NINKI SABODA ABINDA SUKA AIKATA (na kirki), KUMA SU SUNA AMINTATTU CIKIN BENAYE. "
__________________________
(1) يونس: 26.
(2) تفسير القمّيّ 287.
(3) النحل: 30.
(4) العنكبوت: 27.
(5) هود: 114.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج67، ص: 67
فَارْغَبُوا فِي هَذَا رَحِمَكُمُ اللَّهُ وَ اعْمَلُوا لَهُ وَ تَحَاضُّوا عَلَيْهِ وَ اعْلَمُوا يَا عِبَادَ اللَّهِ أَنَّ الْمُتَّقِينَ حَازُوا عَاجِلَ الْخَيْرِ وَ آجِلَهُ شَارَكُوا أَهْلَ الدُّنْيَا فِي دُنْيَاهُمْ وَ لَمْ يُشَارِكْهُمْ أَهْلُ الدُّنْيَا فِي آخِرَتِهِمْ أَبَاحَهُمُ اللَّهُ فِي الدُّنْيَا مَا كَفَاهُمْ بِهِ وَ قَالَ عَزَّ اسْمُهُ :
" Saboda haka ku kwaidaitu cikin wannan sai Allah yayi muku rahma, kuma kuyi aiki (mai kyau) domin Sa, kuma ku dore a kansa. Sannan ku sani yaa ku bayin Allah ! Lalle masu taqawa suna da wani rabon alkhairi wanda ake gaggauta shi gare su, kuma mutanen duniya suyi tarayya dasu (wajen jin dadinsa) cikin duniyarsu , amma mutanen duniya ba za suyi tarayya dasu (cikin wannan alkhairi) a lahira ba, Allah ya halasta musu shi ne (kawai) a duniya gwargwadon abinda zai ishe su dashi. Kuma wanda sunanSa ya daukaka (Allah) yace,
" قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللَّهِ الَّتِي أَخْرَجَ لِعِبادِهِ وَ الطَّيِّباتِ مِنَ الرِّزْقِ قُلْ هِيَ لِلَّذِينَ آمَنُوا فِي الْحَياةِ الدُّنْيا خالِصَةً يَوْمَ الْقِيامَةِ كَذلِكَ نُفَصِّلُ الْآياتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ ."[ 36]
" KACE, " WAYE YA HARAMTA ADON ALLAH WANDA AKA FITAR DA SHI DOMIN BAYINSA, DA KUMA TSARKAKA NA DAGA ABINCI ? KACE, " SHI NA WADANDA SU KAYI IMANI NE CIKIN RAYUWAR DUNIYA, KUMA KEBABBE (gare su masu kyautatawan) A LAHIRA. KAMAR HAKA MUKE RARRABE AYOYI GA MUTANE MASU SANI ."
سَكَنُوا الدُّنْيَا بِأَفْضَلِ مَا سُكِنَتْ وَ أَكَلُوهَا بِأَفْضَلِ مَا أُكِلَتُ شَارَكُوا أَهْلَ الدُّنْيَا فِي دُنْيَاهُمْ فَأَكَلُوا مَعَهُمْ مِنْ طَيِّبَاتِ مَا يَأْكُلُونَ وَ شَرِبُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا يَشْرَبُونَ وَ لَبِسُوا مِنْ أَفْضَلِ مَا يَلْبَسُونَ وَ سَكَنُوا مِنْ أَفْضَلِ مَا يَسْكُنُونَ وَ تَزَوَّجُوا مِنْ أَفْضَلِ مَا يَتَزَوَّجُونَ وَ رَكِبُوا مِنْ أَفْضَلِ مَا يَرْكَبُونَ أَصَابُوا لَذَّةَ الدُّنْيَا مَعَ أَهْلِ الدُّنْيَا وَ هُمْ غَداً جِيرَانُ اللَّهِ يَتَمَنَّوْنَ عَلَيْهِ فَيُعْطِيهِمْ مَا يَتَمَنَّوْنَ لَا يُرَدُّ لَهُمْ دَعْوَةٌ وَ لَا يُنْقَصُ لَهُمْ نَصِيبٌ مِنَ اللَّذَّةِ فَإِلَى هَذَا يَا عِبَادَ اللَّهِ يَشْتَاقُ إِلَيْهِ مَنْ كَانَ لَهُ عَقْلٌ وَ يَعْمَلُ لَهُ تَقْوَى اللَّهِ وَ لَا حَوْلَ وَ لَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ[37].
" Sun zauna a duniya da mafificin abinda za su zauna (a cikinsa daga gidaje), kuma suka ci cikinta da mafificin abinda za su ci, mutanen duniya sunyi tarayya dasu cikin duniyar tasu, suka ci tare da su daga dadadan (abinci) da suke ci, kuma suka sha daga tsarkakan abinda suke sha, kuma suka sanya (tufafi) daga mafificin abinda suke sanyawa, kuma suka zauna daga mafificin abinda za su zauna, kuma su ka aura daga mafificin abinda za su aura, kuma suka hau daga mafificin abinda za su hau. Sun dandana dadin duniya tare da mutanen duniya, su kuwa gobe (qiyama) masu maqwabtaka ne da Allah, za su riqa buri daga gare shi, kuma zai basu abinda suke burinsa, ba zai taba mayar musu abinda suka roqe ba (sai ya ba su shi), sannan ba zai tauye musu wani abu daga wannan dadi ba. To, zuwa ga wannan yaa ku bayin Allah sai ku qosa (urge) zuwa gare shi ga wanda ya kasance yana da hankali (daga cikinku), kuma yayi aikin gare shi don tsoron Allah, babu wata dabara ko wani qarfi sai ga Allah ."
__________________________
(1) النبأ: 36.
(2) سبأ: 37.
(3) الأعراف: 31.
(4) أمالي الطوسيّ ج 2 ص 25.
(5) أمالي الطوسيّ ج 2 ص 124.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج67، ص: 68
Wannan shine saqon da Imam Ali (A. S) ya aika Muhammad Bn Abubakar da shi zuwa mutanen Misra. Allah yasa mu amfana daga wannan saqo.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
3rd December, 2020/ 18th Rabi'us-Sani, 1442.