@Shna Islam ✍️.
Ina farawa da sunan Allah Uban gidan Halittu Mai ikon yin komai, Ya Allah kabani iko ince Dan wani Abu akan Zabbanben bawan ka ISHAQ MUH'D SULEMAN, Tabbas Allah Kai ne kayi kowa'ne bawa Kuma Kai'ne keda ikon Azurta kowa kabar wani cikin bukata Kuma badan baka son shi ba, sai dan hakan ne yafi dacewa da shi.
A'farko ina rokon'ka ya Babban Adilin Sarki Allah ka tsare mani Alkalamin rubutu na harna Gama banyi kalaman kwababa, Dan Darajjar Jinanin Shahedan'mu a ciki harda na Dan uwan mu abokin aiki Masoyin Sauran Abokan aiki wato ISHAQ MUH'D SULEMAN.
Shaheed ISHAQ MUH'D SULEMAN ya Cancanci dukkan yabo a bakina saboda wasu dalilan da bazan iya kirgawa ba Wajibi ne a gareni nayiwa Shahahed Sheda duk da nasan Uban gijinsa nayi masa sheda.
zanyi masa Sheda ne saboda yanada hakki a kaina Allah sarki Shahedi Ina haduwa da mutane da yawa a rayuwa ta a wajeje daban daban Amma a gaskiya bansan a kwai wani lokaci Dana hadu da irin kaba, sai Ranar da Allah ya hadani dakai Na fara sanin ISHAQ ne ta haiyar Soshiyal Midiya, mun dauki tsawon lokaci muna bibiyar Rubutun juna a Soshiyal Midiya ba Tare da kowa nayiwa kowa magana ba, Amma duk lokacin da yayi Post zan duba Kuma zanyi masa abunda ya dace Haka Shima.
Allah da ikon sa sai ya kaddara zamusan juna sosai Kuma mun fara Mu'amila da juna ne ta sanadin Shafin Ma'asumah Negeria News Update sai yazama cewa Yana wakiltar Shafin Nima Ina wakilta, tare da Sanadin Auwal m Tukur Dan koda na san ISHAQ MUH'D SULEMAN tare nasan su da Auwal m Tukur Kuma abokan Auwal m Tukur sun kasance kamar duk abokaina ne saboda taren mu da shi Banda abokin da ya Kai shi a duniya.
Hakan ya Kara karfafa muna Zumuncin mu har yayi karfi sosai wadda a lokacin idan zakaga yadda muke zakace Daman munyi zama waje daya da shi, saboda mutum ne mai son mutane mai fara'ah da Nishadi akan duk wadda zamantakewa ta hada shi da shi bawan Allah mutumin kirki.
Mun fara haduwa da Shaheed ISHAQ MUH'D SULEMAN ne a wani taro da akayi na Shafin Ma'asumah a Birnin Kano nan ne na fara ganin shi da yake mun Riga shi Isa wajen program din muna zaune kawai sai naga isowar shi shigowar shi keda wuya naga "Yan uwa kowa ya fara tsokanar shi ana ba'ah, sai dare dare da fara'ah waje ya dauki Nishadi sosai wadda tunda nazo Banga hakan ba sai da ya iso Ina ganin hakan yasa nace lallai wannan bawan Allah Mumini ne Kuma Masoyin Allah ne, saboda Allah na farin ciki da mutumin da ya farantawa Mumini rai.
Haka akaci gaba da Program cikin Farin ciki da wasa da dariya Kashh laifin Dadi karewa ana cikin hakan sai Ranar kammala taron tazo aiko Ranar da safe naga fuskokin kowa tattare suke da damuwa saboda za a rabu da juna bayan an shaku, hakan yasa wasu Sisters masu Imani kuka Haka dai aka jure aka dauki Hotonan ban kwana akayi sallamah da kowa kowa ya Kama haiya.
Allah sarki Ishaq Ashe ganin farko ne Kuma ganin Karshe namai bayan kowa ya Kama haiyar gida shine mutum na farko daya fara Kiran Auwal m Tukur sukayi magana har muka gaisa da yake lokacin muna tare da Auwal din can bayan mun dauki lokaci da Gama waya sai Auwal ya Kira shi yace muna Yana Gusau.
Bayan ya Isa gida ya Kira ne muna waya cikin Farin ciki har Yana tsokana ta sai naji kamar karmu daina waya hakan yasa aduk lokacin Dana Kira shi muna fara waya zaice bari in Kira ka Haka kuwa ake sai ya kira ni muta waya kai kace ba kati yasa ba Munyi Zumunci Mai Dadi har lokacin Shahadar shi.
Muna cikin Hakan kwatsam a 27 ga watan Disamba sai Sanarwa tazo mun a Facebook ta haiyar bude Data na hau Facebook kawai naga cewa yau jami'an tsao sun budewa "Yan uwa almajiran Malam Zakzaky masu Muzaharar Free Zakzaky Wuta har sun halbi Dan Media sun ciremai yatsa daya, ina duba Hoton sai naga Ashe Ishaq ne nayi Innalillahi sai na daga waya na kira shi yake mun Karin bayani nayimai sannu..
Anyi masa aiki har sauki ya fara samuwa Dan ya kirani a wata Rana na manta Ranar mukayi magana nace ya jikin yace ai jiki da sauki sosai a lokacin har munata ba'ah da shi a she ta bankwana ce, muna Nan sai naga Ance ai an'kuma da Ishaq asibity jikin ya matsamai sai nayi Yunkurin Kiran shi dan naji Amma a lokacin bai daga wayar ba wadda yake har zuwa wannan lokacin baidaga wayar ba Innalillahi wa inna alaihin raji un,.
Na shiga Facebook kenan sai naga Post cewa Innalillahi wa inna alaihin raji un Dan uwa ISHAQ MUH'D SULEMAN ya yi Shahada sakamakon Halbin da jami'an tsaron Yan Sanda suka Mai a wajen wata Muzaharar Free Zakzaky da akayi a Sokoto Innalillahi wa inna alaihin raji un 😭, Gwamnatin Nigeria ta kashe muna jajirtancen wakili Mai kokari mai fafutikar ganin Jagora Sayyid Zakzkay (H) ya samu "yanci Wanda yake sake samun irin sa ba waje kusa ba😭 Buhari Allah ya Isa bazamu taba manta jinin ISHAQ MUH'D SULEMAN ba Kuma bazamu yafe ba wallahi sai mun rama.
Amincin Allah ya tabbata ga SHAHED ISHAQ MUH'D SULEMAN Tun Ranar da aka haifika har Ranar da kayi Shahada da Ranar da za'a tashe ka kana Mazlumi na Sadaukantar da Ladan wannan rubutun zuwa ga ruhin Shahedan Muaulunci tunda ga kan Annabi Adam har zuwa Zamanin Allamah Sayyid Zakzkay (H) Allah ya gaggauta kwato muna jagoran mu da matar sa daga hannun Azzalumman Kasar Nan ilahee.
Ma'asumah Ng news Update
@Shana Islam.