Maraba da zuwan annabin allah Isah Al-Masihu (As) !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BAWAN DA BA YA KUNYAR KASANCEWARSA BAWA GA MAHALICCINSA 


Babu mai musunn cewa a bada tukwici ga dan saqon da yazowa mutum da wata kyauta ko albishir na wani abin alkhairi da zai same shi, wanda hakan ke nuna godiya ce ga wanda ya aiko wannan dan saqo gare shi, shi yasa ma hausawa ke cewa, " YABA KYAUTA TUKWICI ".


Isah Al-Masihu (A. S) ya zo mana da busharar zuwan Annabin rahma Muhammad (S. A. W. W) wanda ya kasance shine shugaban Annabawa da Manzanni (A. S). Cikin busharar tasa ne Allah ke cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 " وَإِذۡ قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُم مُّصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَمُبَشِّرَۢا بِرَسُولٖ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِي ٱسۡمُهُۥٓ أَحۡمَدُۖ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ ."( ٦)


" A LOKACIN DA ISAH 'DAN MARYAMA YACE, " YAA BANI ISRA'ILA ! NI FA MANZON ALLAH NE GARE KU ( ba Allah), MAI GASKATA ABINDA AZO GABA GARE NI NA DAGA ATTAURA, KUMA MAI YIN BUSHARA DA WANI MANZO WANDA ZAI ZO A BAYANA SUNANSA AHMAD. AMMA YAYIN DA YAZO MUSU DA HUJJOJI BAYYANANU SAI SUKA CE, " AI WANNAN SIHIRI BAYYANANNE. "


            (SAFF:6)


Idan kuwa muna murna da zuwan Manzon Allah (S. A. W. W) da gaske dole mu nuna murna da farin ciki na gani ko zuwan wannan babban jakada mai bushara Isah Al-Masihu (A. S), domin rashin nuna farin cikinmu na haihuwarsa butulci ne. 


Al-Masihu dan Maryama (A. S) bawan Allah wanda ba ya kunyar a kira shi bawan Allah, hakan na nuna mana laifi ne mai girma muce shi Allah ne ko wani bangare na Allah. 


Ya fada mana da bakinsa cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا ٠٣ 


وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا ." ١٣


" YACE, " NI BAWAN ALLAH NE, AN BANI LITTAFI KUMA AKA SANYA NI ANNABI .


KUMA AKA SANYA NI MAI ALBARKA A DUK INDA NAKE, KUMA AKAYI MIN WASIYYAH DA (yin) SALLAH DA (bayar da) ZAKKAH MATUQAR INA RAYE. "


           (MARYAM:30-31)


Kuma Allah ya tabbatar mana da haka a inda yake cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥٓ أَلۡقَىٰهَآ إِلَىٰ مَرۡيَمَ وَرُوحٞ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُواْ ثَلَٰثَةٌۚ ٱنتَهُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓ أَن يَكُونَ لَهُۥ وَلَدٞۘ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا ١٧١ لَّن يَسۡتَنكِفَ ٱلۡمَسِيحُ أَن يَكُونَ عَبۡدٗا لِّلَّهِ وَلَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ ٱلۡمُقَرَّبُونَۚ وَمَن يَسۡتَنكِفۡ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيَسۡتَكۡبِرۡ فَسَيَحۡشُرُهُمۡ إِلَيۡهِ جَمِيعٗا ٢٧١


" YAA KU MUTANEN LITTAFI ! KADA KU ZURFAFA CIKIN ADDININKU, KUMA KADA KU FADA AKAN ALLAH FACE GASKIYA. ABIN SANI KAWAI MASIHU ISAH 'DAN MARYAMA MANZON ALLAH NE KUMA KALMARSA DA YA JEFA TA ZUWA GA MARYAMA, KUMA RUHI NE DAGA GARE SHI, KUYI IMANI DA ALLAH DA KUMA MANZONSA, KADA KUCE UKU, KU HANU (daga wannan mummuniyar magana taku) YA FI MUKU AIKHAIRI. ABIN SANI DAI ALLAH NE ABIN BAUTA 'DAYA (ba uku ba), TSARKI YA TABBATA GARE SHI DA YA KASANCE YANA DA 'DA (son), (domin) ABINDA KE CIKIN SAMMAI DA QASSAI NASA NE, KUMA YA ISA GA ALLAH YA ZAMA WAKILI (kan irin wannan mummuniyar magana taku) .


(Shi fa) MASIHU BA YA (jin) KUNYA YA KASANCE BAWAN ALLAH (domin ya san shi bawa ne), HAKA MA MALA'IKU MAKUSANTA (ba sa jin kunya ace su bayin Allah ne), DUK WANDA KE JIN KUNYA DAGA BAUTA MASA KUMA YAYI GIRMAN KAI, TO, DA SANNU (Allah) ZAI TARA SU GABA 'DAYA !"


            (NISA'I:171-172)


Yaa Allah muna murna da zuwa Isah Al-Masihu (A. S), kuma ba za mu fadi abinda ka hane mu na cewa shi daya daga cikin uku ne, tsarki ya tabbata a gare ka da ya kasance gare ka. 


      HAPPY XMAS JESUS 


                     ☝🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


25th December, 2020/ 11th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post