@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MU KYAUTAYA 'DABI'UMMU MU SAMAR DA ZAMAN LAFIYA
Bin son zuciya da nuna isa ya halakar da Shaidan (Iblis) ba wai rashin ilimi ko jahilci bane . A matsayinka na bawa (slave) dole ya kasance ka cire bin son zuciyarka, kayi koyi tare da biyayya ga wanda yazo maka da shiriya cikin ayyukanka da zantukanka.
Kyawawan dabi'u sune kayan adon mumini kuma abinda ke nuna cewa yana koyi da Manzon Allah (S. A. W. W) . Duk wanda ya rasa kyawawan dabi'u ya zama abin zargi wajen Allah dama wajen mutane, sannan ya muzantan kansa da kansa.
Kyawawan dabi'u ba abu ne wanda za a qayyade maka su ba domin suna da yawa, sai dai a ambata maka wasu, wasu kuma za ka iya ji ko gani daga wasu.
Za muyi amfani da wannan riwaya wacce aka samo ta daga Imam Ja'afarus-Saadiq (A. S) a matsayin nusarwa. Ga ta kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
مع، معاني الأخبار لي، الأمالي للصدوق أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ عِيسَى عَنْ أَبِيهِ عَنِ ابْنِ أَبِي عُمَيْرٍ عَنْ حَمَّادِ بْنِ عُثْمَانَ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى الصَّادِقِ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ ع فَقَالَ لَهُ يَا ابْنَ رَسُولِ اللَّهِ أَخْبِرْنِي بِمَكَارِمِ الْأَخْلَاقِ فَقَالَ الْعَفْوُ عَمَّنْ ظَلَمَكَ وَ صِلَةُ مَنْ قَطَعَكَ وَ إِعْطَاءُ مَنْ حَرَمَكَ وَ قَوْلُ الْحَقِّ وَ لَوْ عَلَى نَفْسِكَ[144].
Ya zo cikin Amali Lis-Sudduq, daga Sa'ad daga Ibn Isah daga babansa, daga dan baban Umair , daga Hammad Bn Usman yace, wani mutum ya zo wajen Sadiq Ja'afar Bn Muhammad (A. S) yace masa,
" Yaa dan Ma'aikin Allah ! Ka bani labari game da kyawawan dabi'u. " Sai yace,
" YIN YAFIYA GA WANDA YA ZALUNCE KA,
DA SADAR (da zumuncin) WANDA YA YANKE KA,
DA BAYARWA WANDA YA HANA KA,
DA FADAR GASKIYA KO DA KUWA AKAN KANKA NE ."
(5) معاني الأخبار ص 191، أمالي الصدوق: ص 165.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج66، ص: 369
Wadannan abubuwa su suka fi qarancin samu cikin al'umma a wannan zamani, da ace ana aikata su haqiqa da za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali, domin dukkansu dabi'un Manzon Allah (S. A. W. W) wanda yayi amfani dasu wajen cin nasara cikin da'awarsa.
Yanzu dan'uwanka ne zai yi maka laifi ko kuskure sai kace ba za ka yafe masa ba, alhali kaima kana so in kayi a yafe maka. Sannan kuma sai kace tunda wane ya yanke daga gare ka ba ya zuwa gurinka kamar yadda aka sani ada cikin 'yan'uwa (brothers) wajen zumunci, yanzu abin yayi qaranci.
Kuma yanzu ya zama wanda ya baka ne kawai za ka bawa, kai ba za ka bawa wanda ya hanaka ba, alhali ba shin shi zai koyar dashi dabi'un Manzon Allah (S. A. W. W). Sannan kuma rashin tsoron Allah yayi yawa cikin zukata yadda ba a iya fitowa a fadi gaskiya.
ALLAH YA 'DORA MU KAN AIKATA KYAWAWAN 'DABI'U ABABAN KOYI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
3rd December, 2020/ 18th Rabi'us-Sani, 1442.