@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KARANTA MUSU WANNAN LABARI KO ZA SUYI TUNANI
Daga cikin jerin wadanda idan suka lalace qasa ta lalace akwai maluma wadanda Allah ya basu amfanar al'umma su fada musu gaskiya don su bi Allah da taqawa su sami yardarsa gobe qiyama.
Sai dai kuma daga cikinsu akwai wadanda suka zabi duniyarsu kan lahira, masu biye son zuciyarsu, masu shiga cikin sarakuna da shugabanni don neman yardarsu maimakon neman yardar Allah. To, idan aka sami yawan irin wadannan malamai cikin al'umma sai komai ya lalace al'amra su jagwalgwale.
A zamanin Annabi Musa (A. S) anyi wani malami cikin manyan malaman Banu Isra'ila mai suna BIL'AMU 'DAN BA'URA , ko da shike wasu sunce SAIFIY BN RAAHIB ne, wasu kuma suka ce UMAYYATATU BN ABIY SALT ne, sai dai magana mafi rinjaye ita ce BIL'AMU 'DAN BA'URA.
To, shi wannan malami Allah ya ba shi ilimi ta kai yadda yana cikin wadanda Allah ke saurin karbar addu'arsu, kuma mutanen garin na alfahari da shi.
Wata rana sai Annabi Musa (A. S) ya aika shi zuwa wajen Sarkin Madyana don ya kiraye shi zuwa ga Allah. Da ya isa zuwa ga wannan Sarki maimakon yayi aikin da aka tura shi kansa, sai Sarkin ya yanka masa qasa mai yawa ya mallakar masa ita.
Ganin wannan tagomashi daga Sarki sai malamin yabi addinin Sarkin yabar na Musa (A. S). Sai kuma ya cigaba da taimakonsa wajen yaqar Annabi Musa (A. S).
Domin ya zama darasi ga miyagun malaman wannan zamani masu shiga cikin sarakuna da shugabanni suna yaqar bayin Allah, sai Allah ya umarci Manzonsa (S. A. W. W. W) da cewa ya bamu wannan labari don zama izna gare mu.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱلَّذِيٓ ءَاتَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا فَٱنسَلَخَ مِنۡهَا فَأَتۡبَعَهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَكَانَ مِنَ ٱلۡغَاوِينَ ٥٧١
" KUMA KA KARANTA A KANSU LABARIN WANDA MUKA KAWO MASA AYOYINMU, SAI YA KAUCE DAGA GARE SU, SAI SHAIDAN YA BI SHI (cikin ayyukansa ), SAI YA KASANCE CIKIN HALAKAKKU. "
وَلَوۡ شِئۡنَا لَرَفَعۡنَٰهُ بِهَا وَلَٰكِنَّهُۥٓ أَخۡلَدَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُۚ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ ٱلۡكَلۡبِ إِن تَحۡمِلۡ عَلَيۡهِ يَلۡهَثۡ أَوۡ تَتۡرُكۡهُ يَلۡهَثۚ ذَّٰلِكَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۚ فَٱقۡصُصِ ٱلۡقَصَصَ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ ٦٧١
" DA MUN SO DA MUN 'DAUKAKA SHI DA ITA (ilimi da shiriya), KUMA AMMA SHI YA NEMI DAWWAMA NE A CIKIN QASA (alhali ba a dawwama cikinta), KUMA YA BI SON ZUCYARSA (ta hanyar sabawa Allah da yin biyyayya ga shugannin zalunci da kafirci). TO, MISALINSA KAMAR MISALIN KARE NE, IDAN KA KORE SHI YAYI TA LALLAGE (da harshensa), IDAN MA KA BAR SHI (a kwance yana hutawa) YAYI TA LALLAGE (babu bambanci tsakanin aikinsa da hutunsa). WANNAN SHINE MISALIN MUTANE WADANDA SUKA QARYATA GAME DA AYOYINMU. KA KARANTA IRIN WADANNAN LABARU (a kansu) KO ZA SUYI TUNANI ."
سَآءَ مَثَلًا ٱلۡقَوۡمُ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَأَنفُسَهُمۡ كَانُواْ يَظۡلِمُونَ ٧٧١
" YA MUNANA IRIN WANNAN MISALI NA WADANDA SUKA QARYATA GAME DA AYOYINMU, KUMA KANSU SUKA KASANCE SUNA ZAKUNTA (ba wani ba) ."
(A'ARAF :175-177)
Yanzu shi wannan malami ya sami magada masu yawa cikin wannan zamani/al'umma yadda suke bin addinin shugabanni masu aiki da tsarin kafirci, kuma suna taimaka musu wajen yaqi da malamai magada Annabawa (A. S).
Irin wadannan malamai sune za ka ji su cikin kafafen yada labarai suna yiwa azzalumai kamfen (campaign) da suna yada addinin muslimci.
YAA ALLAH KA GANAR DA WADANNAN MIYAGUN MALUMA !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
8th December, 2020/ 23rd Rabi'us-Sani, 1442.