@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RASHIN SANIN WANNAN HUKUNCI YASA UMAR ZARTAR DA HUKUNCIN KISA
Kafin bayyanar muslimci ana aikata abubuwa da dama masu kyau da marar sa kyau, sai dai babu wanda ya isa ya bambance su ko kuma ya iya cewa wannan halal ne wannan haram ne. Ba a sami damar yin hakan ba har sai da Allah ya aiko da Annabi Muhammad (S. A. W. W) tare da umarnin hani kan wasu abubuwa da kuma tabbatar da wasu daga cikinsu.
Ko da a wannan zamani matuqar ka aikata mummunan abu a rashin sani Allah ba zai kama ka da hukuncinsa ba. Amma da zarar ka san hukuncin haramcinsa shikenan, duk abinda ka aikata a kansa za a hukuntaka.
Abu Abdallah (A. S) ya bayyanar mana da wannan cikin wani hadisi kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
19- ما، الأمالي للشيخ الطوسي الْحُسَيْنُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ الْقَزْوِينِيُّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ وَهْبَانَ عَنْ عَلِيِّ بْنِ حَبَشِيٍّ عَنِ الْعَبَّاسِ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ الْحُسَيْنِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ صَفْوَانَ بْنِ يَحْيَى عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ أَبِي غُنْدَرٍ[5] عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: الْأَشْيَاءُ مُطْلَقَةٌ مَا لَمْ يَرِدْ عَلَيْكَ أَمْرٌ وَ نَهْيٌ وَ كُلُّ شَيْءٍ يَكُونُ فِيهِ حَلَالٌ وَ حَرَامٌ فَهُوَ لَكَ حَلَالٌ أَبَداً مَا لَمْ تَعْرِفِ الْحَرَامَ مِنْهُ فَتَدَعَهُ.
Ya zo cikin AMALIY na Sheikh 'Dusiy Al-Hussein Bn Ibrahim Al-Quzwineey, daga Muhammad Bn Wahbaan, daga Aliyu Bn Habashiyyu, daga Abbas Bn Muhammad Bn Hussein, daga babansa, daga Safwan Bn Yahya, daga Hussaini Bn Abiy Gundaari, daga babansa, daga Abu Abdullahi (A. S);
" SU ABUBUWA (dukkansu) A SAKE SUKE (basu da iyaka) MATUQAR UMARNI KO HANI BAI ZO MAKA BA. KUMA DUKKAN WANI ABU WANDA HALACCI DA HARAMCI KE KASANCEWA CIKINSA , TO, HAR ABADA HALAL NE GARE KA MATUQAR BAKA SAN HARAMCI DAGA GARE BA BALLANTANA KA BAR SHI ."
A wata riwayar kuma daga Imam Sadiq (A. S) yace,
20- يه، من لا يحضره الفقيه رُوِيَ عَنِ الصَّادِقِ ع أَنَّهُ قَالَ: كُلُّ شَيْءٍ مُطْلَقٌ حَتَّى يَرِدَ فِيهِ نَهْيٌ.
" KOWANNE ABU A SAKE YAKE HAR SAI HANI YA ZO CIKINSA ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج2، ص: 275
Wannan hukunci kuwa ya tabbata daga bakin Imam Ali (A. S) zamani mulkin Ibn Khaddab.
Yadda abin ya faru shine, a zamanin Umar anzo masa da wani mutum ne wanda yasha giya sai Umar yace aje yanke masa hukunci. Sai mutumin yace, " Wallahi ban san cewa haramun bace. "
Umar yace lalle sai an yanke masa hukunci. Sai Imam Ali (A. S) yace aje da shi cikin jama'ar Madinah ayi Shela shin ko akwai wanda ya san shi ? Kuma akwai wanda ya taba gaya masa ko karanta masa cewa Allah ya saukar da ayar hana shan giya ?
Da aka je akayi shela ba a sami wanda ya karanta masa ba, sai Imam Ali (A. S) yace, " SHIKE NAN A SAKE SHI, DOMIN BABU HUKUNCI KAN WANDA HANIN ABU BAI RISKE SHI BA ."
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
9th December, 2020/ 24th Rabi'us-Sani, 1442.