Rbtwa: J. I. R
Zainab dai bayan gama wayar su da Ahmad, ta shiga tunani. Zuciyarta na raba mata abun biyu. Ta rike amanar Ahmad. Gefe guda yana saka mata ta amsa Alhaji Hudu. Haka dai ta jima tana wannan sake-saken.
Asma'u ta matsa sosai. Tana ta zuga Zainab, shi ko Alhaji Hudu ya matsa da sakin kudin nan. Haka dai abun ya yi ta tafiya. Har a zo a rinjaye Zainab. Ta dauki shawaran Asma'u. Kudin Alhaji Hudu ya tafi da ita.
Alhaji Hudu wata rana ya zo. Sai ya aika kan Zainab ta fito. Sai kawai dan aiko ya fito, "Wai an ce ka shiga ba matsala". Nan Alhaji Hudu ransa yayi fari, "Yau ni ne Zainab take cewa na shigo? Kai lallai da alamu tsuguno ya karema mai bara". Haka nan Alhaji Hudu ya shiga gidan nan. Daga shigowarsa Zainab ta yi wuf cikin murmushi irin na nuna so da yarda. Ta nuna masa wani daki, kan ya shiga nan ne masaukinsa.
Bayan da Alhaji Hudu ya shiga. Zainab ta kawo masa ruwan randa mai sanyi, su zauna. Su yi ta hira, Zainab ta bayyana manufarta. "Alhaji ka yi hakuri, kasan komai yana da bukatar shawara, kuma shawara yana da bukatar lokaci, shiyasa ban yi gaggawan sanar dakai zuxiyata ta yi na'am dakai ba. Tun farko ka kwanta min, kawai yanayi ne namu na mata. Na aminta da soyayyarka". Ahamd "Lallai kam, na ji dadi da jin wanan sako mafi haske a gareni, karki damu ai dama an ce, hakuri karshinki nasara. Ba gashi kin mallakamin zuciyarkiba, alhamdulillah!".
Su yi hiransu a matsayin masoya. Karshe Alhaji Hudu ya zo zai tafi, ya ciro kudi ya baiwa Zainab. Sannan ya je ya karisa ya gaida kakan Zainab. Itama ya aje mata kudi. Su Asma'u duk su samu na su. Ya yi sallama ya koma cikin murna da farin-ciki.
Soyayya ta kullu a tsakanin Zainab da Alhaji Hudu. Suna soyayyarsu sosai. Har Zainab ta sake ma Alhaji Hudu. Haka dai su ta soyayyarsu. Alhaji Hudu yana nuna mata gata. Na daga duk abun da take da bukata.
Wata rana, Ahmad ya kira Zainab. Ta shiga ba a dagaba. Wa she gari ya dada ba a daga. Ahmad ya shiga tunani "Anya Zainab ba ta kasa ni a kasuwa ba ne? A ce bata neman ba, na nemeta ta shiga a qi dauka. Ni na fara karaya gaskiya". Haka dai Ahmad yayi ta fama da tunani. Domin abun ya zama bako a garesa.
Haka nan dai ya kan Kira number Zainab amma bata dagawa. Karshema block nasa ta yi. Ko ya kira ba ta tafiya. Ahmad ya shiga halin, Allah gani gareka. Duk ya shiga damuwa. Ya na ta tunanin shikenan Zainab ta gama da shi.
Mu hadu a kashi na gaba, don jin Wana mataki zai dauka. Don yakar wanan babban jarabawa da ta fuskantu rayuwarsa.