Kasar da akewa mahaifiya fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta, kasar da ake kashe mahaifi a gaban matarsa da 'ya'yansa, kasar da ake kashe 'ya'ya a gaban iyayensu, kasar da ake kashe yaya gaban kannensa, ake kashe kanne agaban yayansu, kasar da ake wulakanta dukiyar al'umma a gabansu!!!, ake kone muhallansu gabansu, kasar da mutane ke barin muhallansu da kansu saboda tashin hankali, kasar da mahaifiya take barin danta tana kallonsa yana kallonta saboda ceton rai, kasar da miji yake barin matansa saboda ceton ransa, kasar da 'ya'ya ke barin raunanan iyayensu saboda ceton ransu.
Natsuwa ta kaura, kwanciyar hankali ta gushe, aminci ya kau, farin ciki ya zama labari, walwala ta Kare, alokaci daya Kuma, tashin hankali ya yawaita, zaman lafiya ya zama tarihi.
A kasata ne kawai ake iske mutum har dakinsa akasheshi a kona gawarsa, agaban iyalansa wasuma a kona su da ransu har suzam toka agaban idanun al'umma. WANNAN ITACE KASA TA NIGERIA!!!!!!
Kuma wannan duk yana faruwa ne da sanin gwamnati, Allah wadaran naka ya lalace, duk da haka wasu na son cigaban wannan gwamnatin suna saran wani abu na alkhairi daga gareta.
Hmmm!!
Tabbas a Nigeria kadaine ake kashe mutum kuma dan uwansa mutum yace Allah ya kara ai laifinsa ne, tabbas a Nigeria kadaine ake wulakanta dukiyar al'umma wasu al'ummar suce gara da akai, tabbas a Nigeria kadaine ake maida garuruwa gulbin jini kuma makwaftan garin suce laifinsu ne, tabbas a kasata Nigeria ne kawai ake hakan, duk sauran kasashe suna nuna rashin jin dadinsu da kuma damuwar su akan duk abinda ya samu wani dan kasarsu, amma kaico banda kasata, kasata kasar zalunci, kasar azabtarwa, kasar muzgunawa, kasar cin haram, kasar marasa tausayi da jin Kai, kasar da bata dauki ran dan Adam bakin komi ba, kasar da batada guri sai taga ta cutar da mutanenta.
Ya Allah kafimu sanin kasarmu Allah ka kawo mana dauki, ka'yantar da bayinka daga hannun azzulam mahukunta, ya Allah ka tausayawa bayinka.
Mu bama zama muna saka sharri da sharri, muna fatan alkhaeri ne da kowa, Allah ya yafe mana baki daya
✍🏽zarah A Zamsarf