INNALIL-LAHI WA INNAH ILAIHIR-RAAJI'UUN: Kakar Malam Adamu Muhammad Ningi ta koma ga Allah mahalicci !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

A wannan rana ce juma'a 11-12-2020/ 26-4-1442 Allah ya karbi ran kakar su malam Adamu Muhammad Ningi. 


Ta rasu ta bar 'ya mace daya (1) mabiyar Sayyid Zakzaky (H) da jikoki 9 wadanda 7 daga cikinsu duk masu wilaya ga Ahlul-Bait (A. S) ne, tare da 'ya'yan jikoki 23. Kai, bayan nata da tsaho domin har da jikokin jikoki 5 ta bari. 


Daga cikin jikokin nata akwai dan'uwa malam Adamu Muhammad Ningi .


Muna barar sallar Wahsha ga wannan baiwar Allah wacce ta qinqishen masoya gidan Manzon Allah (S. A. W. W). 


Sunanta shine Asma'u Abdullahi. 


Allah haskaka qabarinta ya kuma riskar da ita zuwa ga ceton Manzon Allah (S. A. W. W) da iyalan gidansa (A. S).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post