@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KACE BAN SANI BA KAWAI SHI YAFI ALKHAIRI GARE KA
Na dade ina jin shakku ko kokwanto cikin mafi yawan fadawar da malaman bangaren sunnah ke bayarwa yayin da akayi musu tambayoyi.
Dalilin wannan shakku ko kokwanton da nake yi shine, sau da yawa in anyi musu tambaya kan wata mas'ala har suka bada amsa, a qarshe sai suce Allah ne masani (ALLAHU A'ALAMU ) (wanda hakan ke nuna suna shakku) . To, idan naji irin wannan amsa sai na soma shakku kan abinda suka fada, domin a fahintata su ma kansu basu da yaqini kan amsar da suka bayar.
Ban ce basa yi ba, amma dai ni ban taba jin Sayyid (T) ya bada amsa kan tambayar da akayi masa sannan a qarshe yace, "ALLAHU A'ALAMU " ba. Hakama ban taba ji daga bakin wasu malamai na wannan harka ba.
Ku yimin afwa, ba cewa nayi basa fada ba, cewa nayi ban taba ji ba !
Ban san wannan sirri ko hikima ba har sai da naci karo da wadannan riwayoyi kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
26- سن، المحاسن أَبِي عَنْ حَمَّادِ بْنِ عِيسَى عَنْ حَرِيزٍ عَنِ الْهَيْثَمِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مُسْلِمٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِذَا سُئِلَ الرَّجُلُ مِنْكُمْ عَمَّا لَا يَعْلَمُ فَلْيَقُلْ لَا أَدْرِي وَ لَا يَقُلِ اللَّهُ أَعْلَمُ فَيُوقِعَ فِي قَلْبِ صَاحِبِهِ شَكّاً وَ إِذَا قَالَ الْمَسْئُولُ لَا أَدْرِي فَلَا يَتَّهِمْهُ السَّائِلُ.
Daga Hammad Bn Isa ,daga Hareez, daga Haitham , daga Muhammad Bn Muslim, daga Abu Abdullahi (A. S) yace,
" IDAN AKA TAMBAYI WANI DAGA CIKIN KU ABINDA BAI SANI BA, TO, YACE BAN SANI BA, KADA YACE ALLAH NE MASANI (ALLAHU A'ALAMU), DOMIN HAKAN ZAI SA KOKWANTO CIKIN ZUCIYAR MAI TAMBAYAR . IDAN WANDA AKA YIWA TAMBAYA YACE, " BAN SANI BA " , TO, MAI TAMBAYAR BA ZAI TUHUME SHI (cikin zuciyarsa) BA. "
A wata riwaya kuma,
28- سن، المحاسن أَبِي عَنِ ابْنِ الْمُغِيرَةِ عَنْ فُضَيْلِ بْنِ عُثْمَانَ عَنْ رَجُلٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِذَا سُئِلْتَ عَمَّا لَا تَعْلَمُ فَقُلْ لَا أَدْرِي فَإِنَّ لَا أَدْرِي خَيْرٌ مِنَ الْفُتْيَا.
Daga Ibn Mugeerata, daga Fudhail Bn Usman, daga wani mutum, daga Abu Abdullahi (A. S) yace,
" IDAN AKA TAMBAYE KA ABINDA BAKA SANI BA, TO, KACE BAN SANI BA, DOMIN CEWA BAN SANI BA TAFI ALKHAIRI DAGA BADA FATAWA (cikin Jahilci) ."
A wata riwayar kawai
29- سن، المحاسن جَعْفَرُ بْنُ مُحَمَّدٍ عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ الْأَشْعَرِيِّ عَنِ ابْنِ الْقَدَّاحِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ قَالَ عَلِيٌّ ع فِي كَلَامٍ لَهُ لَا يَسْتَحْيِي الْعَالِمُ إِذَا سُئِلَ عَمَّا لَا يَعْلَمُ أَنْ يَقُولَ لَا عِلْمَ لِي بِهِ.
Daga Ubaidullahi Al-As'ariy, daga Ibn Qaddahi, daga Abu Abdullahi (A. S), daga babansa (A. S) yace,
" ALI (A. S) YA FADA CIKIN KALAMANSA, " KADA MALAMI YAJI KUNYA IN AN TAMBAYE SHI ABINDA BAI SANI BA YACE BAN SAN SHI BA ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج2، ص: 120
Za kuga hakan idan kuka bibiyi tarihi cikin irin tambayoyin da aka riqa yiwa Manzon (S. A. W. W) ko Imam Ali (A. S) , babu wanda ke bada amsa daga cikinsu sannan a qarshe yace ALLAHU A'ALAMU. Duk amsar da suka bayar suna da ilimi da yaqini ne kanta, shi yasa ba sa shakku, kuma masu yi musu tambayar ma ba sa yin shakku ko za a sami Bambancin amsa.
Allah ya sa mu dace.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
31st November, 2020/ 16th Rabi'us-Sani, 1442.