@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BABU WANDA YA CANCANCI WANNAN LAQABI SAI IMAMAI 12
An samu a zamanin baya yadda aka riqa qaqabawa wasu da dama laqabi da Ameerul-Muminina alhali su ba ahlin abin bane. Wannan dalili yasa suka riqa tafka abubuwan da ke nuna cewa lalle wannan suna ba nasu bane, domin ba a kira Imam Ali (A. S) da suna SIDDIQUL-AKBAR ba har sai da ya cancanci hakan, kuma ayyukansa da zantukansa suka tabbatar da haka.
Kamar hakane a wannan zamani za kaji ana kiran mutum cewa malam ko Sheikh, amma da zarar ka kalli ayyukansa da zantukansa sai kaga cin zarafi ne ga haqiqanin masu wannan suna.
Ya zo cikin KANZUL-FAWA'ID na Karajikiyyi cewa, Abu Hassan Muhammad Bn Ahmad Bn Shaazaana, daga Nuhu Bn Ahmad, daga Qais Bn Rabee'i, daga Sulaimanal-A'amashi, daga Ja'afar Bn Muhammad, daga iyayensa da Ameerul-Muminina Imam Ali (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace min;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" YAA ALIYU ! KAINE SHUGABAN MUMINAI KUMA JAGORAN MASU TSORON ALLAH.
YAA ALIYU ! KAINE SHUGABAN WALIYYAI KUMA MAGAJIN ILIMIN ANNABAWA KUMA MAFI ALKHAIRIN SIDDIQAI, KUMA MAFIFICIN WADANDA SUKA GABATA.
YAA ALIYU ! KAINE MIJIN SHUGABAR MATAN TALIKAI KUMA KHALIFAN MAFI ALJHAIRIN MANZANNI.
YAA ALIYU ! KAINE MAJIBINCIN MUMINAI KUMA HUJJA AKAN DUKKAN MUTANE A BAYANA, ALJANNAH TA WAJABA GA WANDA YA JIBINCE KA, KUMA WUTA TA WAJABA GA WANDA YAYI GABA DA KAI.
YAA ALIYU ! NA RANTSE DA WANDA YA AIKO NI DA ANNABCI KUMA YA ZABE NI AKAN DUKKAN MUTANEN KIRKI, DA ACE BAWA ZAI BAUTAWA ALLAH TSAHON SHEKARA DUBU (1000) BA ZA A KARBA MASA BA FACE SAI DA WILAYARKA DA KUMA WILAYAR LIMAMAI DAGA 'YA'YANKA.
KUMA LALLE WILAYARKA BA TA KARBUWA SAI DA YIN BARA'A GA MAQIYANKA DA KUMA MAQIYA LIMAMAI DAGA 'YA'YANKA. DA WANNAN JABRA'ILU (A. S) YA BANI LABARI, WANDA YASO YAYI IMANI, KUMA WANDA YASO YA KAFIRCE ."
22 كَنْزُ الْفَوَائِدِ لِلْكَرَاجُكِيِّ، أَخْبَرَنِي أَبُو الْحَسَنِ مُحَمَّدُ بْنُ أَحْمَدَ بْنِ شَاذَانَ عَنْ نُوحِ بْنِ أَحْمَدَ عَنْ قَيْسِ بْنِ الرَّبِيعِ عَنْ سُلَيْمَانَ الْأَعْمَشِ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ آبَائِهِ عَنْ أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع قَالَ: قَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ ص يَا عَلِيُّ أَنْتَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ وَ إِمَامُ الْمُتَّقِينَ يَا عَلِيُّ أَنْتَ سَيِّدُ الْوَصِيِّينَ وَ وَارِثُ عِلْمِ النَّبِيِّينَ وَ خَيْرُ الصِّدِّيقِينَ وَ أَفْضَلُ السَّابِقِينَ يَا عَلِيُّ أَنْتَ زَوْجُ سَيِّدَةِ نِسَاءِ الْعَالَمِينَ وَ خَلِيفَةُ خَيْرِ الْمُرْسَلِينَ يَا عَلِيُّ أَنْتَ مَوْلَى الْمُؤْمِنِينَ وَ الْحُجَّةُ بَعْدِي عَلَى النَّاسِ أَجْمَعِينَ اسْتَوْجَبَ الْجَنَّةَ مَنْ تَوَلَّاكَ وَ اسْتَوْجَبَ دُخُولَ النَّارِ مَنْ عَادَاكَ يَا عَلِيُّ وَ الَّذِي بَعَثَنِي بِالنُّبُوَّةِ وَ اصْطَفَانِي عَلَى جَمِيعِ الْبَرِيَّةِ لَوْ أَنَّ عَبْداً عَبَدَ اللَّهَ أَلْفَ عَامٍ مَا قُبِلَ ذَلِكَ مِنْهُ إِلَّا بِوَلَايَتِكَ وَ وَلَايَةِ الْأَئِمَّةِ مِنْ وُلْدِكَ وَ إِنَّ وَلَايَتَكَ لَا تُقْبَلُ إِلَّا بِالْبَرَاءَةِ مِنْ أَعْدَائِكَ وَ أَعْدَاءِ الْأَئِمَّةِ مِنْ وُلْدِكَ بِذَلِكَ أَخْبَرَنِي جَبْرَئِيلُ ع فَمَنْ شاءَ فَلْيُؤْمِنْ وَ مَنْ شاءَ فَلْيَكْفُرْ[69]
(2) اعتقادات الصدوق: 111- 114.
(3) كنز الكراجكيّ: 185.
Madallah da wannan labari na Mala'ika Jibrilu (A. S).
Allah ka tabbatar damu kan wilayar Imam Ali data 'ya'yansa 11 (A. S).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
16th December, 2020/ 1st Jimada-Ulah.