@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Manzon Allah (S. A. W. W) ya bayyana mana wasu dabi'u kyawawa wadanda dukkansu ababen godewa ga mumini idan ya same su.
Ga su kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص الْعِلْمُ خَلِيلُ الْمُؤْمِنِ وَ الْحِلْمُ وَزِيرُهُ وَ الْعَقْلُ دَلِيلُهُ وَ الْعَمَلُ قَائِدُهُ وَ الرِّفْقُ وَالِدُهُ وَ الْبِرُّ أَخُوهُ وَ الصَّبْرُ أَمِيرُ جُنُودِهِ[140].
(1) مجمع البيان ج 4 ص 323.
(2) الكافي ج 2 ص 240.
Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" SHI ILIMI ABOKI NE GA MUMINI, HAQURI KUMA MATAIMAKINSA, HANKALI KUMA DALILINSA, AIKI KUWA JAGORANSA, TAUSAYI KUMA MAHAIFANSA, KYAWAWAN AYYUKA KUMA 'DAN'UWANSA , HAQURI KUMA SHUGABAN RUNDUNARSA ."
NB:-
- Duk wanda ya sami Ilimi ya sami abokin tafiya wanda zai riqa nuna masa gaskiya da qarya.
- Shi kuwa haquri mataimakinsa ne, domin shi zai ba shi dama wajen aikata aikhairi ko da ga mai cutar da shi ne.
- Hankali kuwa shine wanda zai tantance masa qarya da gaskiya. Duk lokacin da aka nemi jefa shi cikin rudani hankalinsa ne zai tantance masa. Shi yasa Allah ke ce mana don menene ba za muyi tadabburin Qur'ani ba ?
- Aiki kuwa shine jagora, domin ta hanyarsa ne ake zuwa ga rahmar Allah. Duk wanda bai yi aiki da iliminsa ba, to, ba zai amfana ta dalilinsa ba.
- Tausayi shine mahaifan mumini, domin idan yana tausayi zai sami masu tausaya masa kamar yadda mahaifa ke tausayin 'ya'yansu.
- Idan mutum na aikata kyawawan ayyuka ya sami 'yan'uwa masu raka shi har cikin qabarinsa.
- Haquri kuwa (Sabri) shine shugaban dukkan rundunarsa, duk wani motsi na mutum in babu haquri ba zai yi nasara.
Tambayi 'yan kasuwa ko 'yan gwagwarmaya ko masu karatu ko sana'a kaji fa'idar haquri.
ABIN LURA
HILMU da SABRI duk suna nufin haquri ne, sai dai matakai ne wanda wani ya fi wani, kamar dai ace maka MU'UMINUN ne da TAQIYYUN.
Allah yasa mu dace.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08126385470)
29th December, 2020/ 15th Jimada-Ulah, 1442.