Yazo A cikin Ruwaya daga Imam Ja'afar Sadiq (As) yana cewa Babu wata Zuciya face tana da kunnuwa guda biyu Akan dayan kunne akwai Mala'ika Murshid dayan kunnen kuwa akwai Shedan
Shi Mala'ika zai umarceka da aikin Alkhairi shi kuma Shedan zai umarceka da aiki bara kyau
To aha yake acikin mutane akwai Shedanu duk mutumin da zai umarceka da aikin da zai nisantaka da Allah sunansa Shedan.
Sai Annabi Adam yayi kuka sai yace ya Ubangiji kai ka halicceni kuma kai ka halicceni Iblis kuma kasan ya bayyanar da kiyayyarshi gareni sabo da abinda kaimin na Falala kuma gashi ka salladashi a kaina ba zan iya yin fada da Iblis ko nayi nasara akanshiba sai da taimakonka, Sai Allah Yace Ya Adamu bazaka haifi da daya ba face na wakilta masa Mala'iku guda biyu suna kareshi daga munanan abin gwami Sai Annabi Adam yace ya Ubangiji akaramin Sai Allah yace Idan kayi aiki daya kyakkyawa za'a baka lada goma sai Annabi Adam yace ya Ubangiji akaramin Sai Allah yace bazan taba rufe kofar tuba ga daya daga cikin Yayan kaba matukar baizo gargaraba.
Daga Almustapha A Abdullahi Jos