@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN GASKIYA TAZO KAWAI KARBARTA AKE YI
Allah (T) ya halicci zuciya kuma ya sanya so da qiyayya a cikinta, takan so abu mai kyau da mummuna, sannan kuma takan qi abu mai kyau da mummuna . Hakan kuwa na faruwa sakamakon yanayin yadda abin yazo mata.
Wani lokaci abu mai kyau kan zo mata, amma sai ta qi shi saboda bai zo mata yadda take so ba , wani lokaci kuma mummuna ne zai zo mata, amma sai ta so shi saboda yazo daidai da abinda take so.
Kafin zuwan muslimci al'umma ta yi dumu-dumu ne cikin bautar Gumaka, bautar da mata tare da kashe su, danne haqqin raunana da qarawa masu mulki qarfi. A daidai wannan lokaci aka haifi fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W) kuma ya taso cikin kyawawan dabi'u har ta kai yadda kowa ke yi masa shaida kan haka . Ya kasance mai gaskiya da riqon amana da ganin girma na gaba da shi tare da tausayawa na qasa da shi.
Duk da wannan kyawawan dabi'u da yake da su (S. A. W. W) wanda aka yi masa shaida kan haka, a daidai lokacin da aka aiko shi a matsayi Manzo da kuma saqon muslimci da kadaita Allah (T) wajen bauta sai aka qaryata shi. Wannan abinda yazo da shi mai kyau ne, amma da shike sigar da yazo musu yana nuna cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah ne, hakan yasa suka qi karbar masa, kuma su kayi gaba mai tsanani da shi.
Duk da irin wannan gaba tasu matsananciya gare shi (S. A. W. W), hakan bai hana daga baya wasu sun dawo sun amsa masa kiran nasa ba, kuma suka taimake shi wajen isar da saqonsa.
Saboda haka har zuwa wannan zamani da muke ciki ana samun mutane da dama daga cikin musulmai na adawa da mai kira zuwa ga sahihiyar hanya , ko kuma su riqa adawa da wani abu na gaskiya saboda rashin fahintarsa ko kuma saboda ginuwa kan wata aqida wacce ba koyarwar muslimci take bi ba.
Babban abin misali anan shine, kana samu a baya wasu na adawa da da'awar Sayyid Zakzaky (H) har ma da daukar matakin daqile ta, amma daga baya sai ka gansu sun fada tsulundum cikin mabiyansa (H).
Wasu kuma za kaga suna qiyayya ne da al'amarin yin Maulidin fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A.W.W), amma kuma sai a wayi gari kaga dasu ake damawa cikinsa .
MUSLIMCI BA SHINE HANYA MADAIDAICIYA BA
Babu wani abin daurewar kai idan aka ambaci muslimci da cewa ba shine hanya madaidaiciya, domin shi ya kasance addini ne wanda ke rarrabe tsakanin kafirai da musulmai. Duk wanda ya amsa sunan muslimci ya sami wata kariya wacce za a cire shi daga cikin kafirai, sannan irin hukuncin da ya hau kan kafirai bai hau kansa ba.
Babbar hujjata ta wannan magana ita ce, babu mai musanta cewa musulmi ne kadai ke karanta Alqur'ani kuma ya karanta cikin sallarsa cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ " (٦)
" KA SHIRYAR DAMU TAFARKI MADAIDAICI ."
(SURATUL-FATIHATI:6)
Da ace muslimci shine tafarki madaidaici, to, da duk wanda ya muslimta ya shiryu kan hanya madaidaiciya, kuma da duk wanda ya mutu zai shiga Aljannah. Amma wani abin mamaki shine, idan ka kasa musulmi kashi 100, to, ba lalle kashi 50 su tafi aljannah ba. Menene dalili ? Ya kamata kowa ya yiwa kansa wannan tambaya.
HANYA MADAIDAICIYA
Hanya madaidaiciya ita ce karbar gaskiya ko daga ina ta fito, kuma ko daga bakin wanene, sannan kuma ayi aiki da ita kamar yadda Allah (T) yayi umarni . Wannan abin ne kuma akayi qarancinsa har zuwa yanzu.
Saboda haka duk wanda ya muslimta kuma ya karbi gaskiya yayi aiki da ita ko da ta saba da son ransa, to, wannan shine ke kan hanya madaidaiciya kuma shine zai shiga Aljannah da iznin Allah.
Kenan don a baya an sami wadanda ke gaba da sahihiyar da'awa sai kuma daga baya ya fahinci gaskiya ya karbe ta yake aiki da ita, to, bai zama abin mamaki ba kuma bai zama abinda za a zauna ana hirarsa ba, sai dai in za a kawo a babin misali.
Sai dai kuma karbar gaskiya da yin aiki da ita ba zai hana a kullum mutum ya riqa addu'ah da cewa,
" KA SHIRYAR DAMU KAN TAFARKI MADAIDAICI ." ba, domin yin hakan neman tabbatuwa ne kan haka.
Kada ka manta, mutum zai iya muslimta amma ya shiga wuta mafi tsanani kamar yadda na ambata a baya, amma duk wanda ya shiryu kan tafarki madaidaici ba zai shiga wuta.
YAA ALLAH KA SHIRYAR DAMU KAN TAFARKI MADAIDAICIYA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
5th December, 2020/ 20th Rabi'us-Sani, 1442.