@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MADALLAH DA WADANNAN UBANNI NAGARI
Allah shi ke zaben wasu daga cikin bayinsa ya fifita su kan wasu bisa iko da ganin damarsa, kuma dole mutum ya sallama musu in shi mumini ne. Sannan kuma ba haqqi ne a kansa ya tambayi dalilin hakan ba.
۞تِلۡكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۘ مِّنۡهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُۖ وَرَفَعَ بَعۡضَهُمۡ دَرَجَٰتٖۚ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ..................
" WADANCAN MANZANNI NE, MUN FIFITA SASHENSU AKAN SASHE, DAGA CIKINSU AKWAI WANDA ALLAH YAYI MASA MAGANA, KUMA YA 'DAUKAKA SASHENSU DA DARAJOJI. KUMA MUKA BAIWA ISA 'DAN MARYAMA HUJJOJI BAYYANANNU, KUMA MUKA QARFAFA SHI DA RUHI MAI TSARKI.....
(BAQARA:253)
Irin wannan fifikon ne Allah ya fifita Manzon Allah (S. A. W. W) da Imam Ali (A. S) suka zama mafiya matsayi, daraja da fifiko akan iyayen kowa daga cikin wannan al'umma.
Haqqinsu shine mafi girman haqqi akan wannan al'umma fiye da haqqin mahaifansu dake kansu ba tare da an tauye nasu haqqin ba.
In ba wani gilli ne cikin zukatan mutane ba babu wanda zai ji qeqayin wannan magana cikin zuciyarsa, domin yakan ce malaminsa ya fi mahaifansa, to, ina kuma ga Manzon Allah (S. A. W. W) da kuma Imam Ali (A. S) ?
Ya zo cikin riwaya kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
. وَ قَالَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ ع سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ ص يَقُولُ أَنَا وَ عَلِيٌّ أَبَوَا هَذِهِ الْأُمَّةِ وَ لَحَقُّنَا عَلَيْهِمْ أَعْظَمُ مِنْ حَقِّ أَبَوَيْ وِلَادَتِهِمْ فَإِنَّا نُنْقِذُهُمْ إِنْ أَطَاعُونَا مِنَ النَّارِ إِلَى دَارِ الْقَرَارِ وَ نُلْحِقُهُمْ مِنَ الْعُبُودِيَّةِ بِخِيَارِ الْأَحْرَارِ.
Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S) yace, " Na ji Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa,
" NI DA ALIYU UBANNIN WANNAN AL'UMMA CE, KUMA HAQQINMU A KANSU SHINE MAFI GIRMA FIYE DA HAQQIN UBANNIN DA SUKA HAIFE SU. DOMIN MUNE ZA MU TSERATAR DA SU DAGA WUTA ZUWA GIDAN TABBATA MATUQAR SUNYI MANA BIYAYYA. SANNAN KUMA MU RISKAR DASU (da Aljannah) DAGA GIDAN BAUTA (duniya) DA KUMA ZABABBUN 'YANTATTU ."
(1) الاحتجاج: ص 128
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج66، ص: 344
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08137925034)
3rd December, 2020/ 18th Rabi'us-Sani, 1442.