Da kyawawan dabi'u ake yalwatawa mutane !!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MAI KYAWAWAN 'DABI'U YA SAMI WADATA 


Cikin halittun Allah ya halicce su ne bisa yadda yaso, kuma ya rarraba arziqinsa tsakaninsu bisa gwargwado. Anyi wani mabuqaci (talaka) wani kuma aka yi shi mawadaci (mai wadata). 


Kowanne daga cikinsu yana cin albarkacin wani, domin idan babu mabuqata mawadata za su takura wani lokaci, sannan kuma idan babu mawadata mabuqata za su shiga cikin qunci . Saboda haka kowanne sashe na da amfani ga sashe. 


Ba zai taba yiwuwa mutum ya iya gamsar ko wadatar da mutane ta hanyar abinda Allah ya hore masa, sai dai yakan iya sauqaqa musu kan wani abu qanqani ba buqatu na dindindin ba. 


Manzon Allah (S.A.W.W) ya kasance yana cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ 


" إِنَّكُمْ لَنْ تَسَعُوا النَّاسَ بِأَمْوَالِكُمْ فَسَعُوهُمْ بِأَخْلَاقِكُمْ‏ ."


" LALLE KU BA ZA KU (iya) WADATAR DA MUTANE DUKIYOYINKU BA, (saboda haka) KU YALWATA SU DA KYAWAWAN 'DABI'U ."


Idan ka dabi'antu da kyawawan dabi'u za ka iya wadatar da mutane masu yawa cikin qanqanin lokaci, kowa zai iya gamsuwa/wadatuwa da dabi'unka kyawawa fiye da yadda zai wadatu da dukiyarka. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


28th December, 2020/ 14th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post