@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DAGA ABU JA'AFAR (A. S)
Ita nadama (regret) kan auku ne ta bangare biyu, walau mutum yayi ta kan wani aikin alkhairi ko kuma sharri.
Kowanne daga cikinsu abu ne mai kyau, sai dai daya daga cikinsu ya fi daya.
Yazo cikin Kafiy, daga Muhammad Bn Yahya, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Isah , daga Muhammad Bn Sinaan, daga baban Khaleed Al-Qammadi, daga Humrana, daga baban Ja'afar (A. S) yace,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" YIN NADAMA AKAN YAFIYA (afwa) YA FI FALALA DA KUMA YALWA DAGA YIN NADAMA AKAN UQUBA ."
الكافي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عِيسَى عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ عَنْ أَبِي خَالِدٍ الْقَمَّاطِ عَنْ حُمْرَانَ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: النَّدَامَةُ عَلَى الْعَفْوِ أَفْضَلُ وَ أَيْسَرُ مِنَ النَّدَامَةِ عَلَى الْعُقُوبَةِ[27].
Sau da yawa wasu kan yi nadama kan wani abu da suka yi na yafiya ga wani wanda ya saba musu ko ya zalunci, har yake ai da ya sani da bai yi wannan yafiya ba, a biya kawai ko kuma a daukar masa fansa shi yafi.
To, duk wanda ya yafewa dan'uwansa wani laifin da yayi masa wannan wani dalili daga baya ya sanya shi yin nadama kan wannan yafiya, to, wannan aiki nasa na yafiyar bai baci ba.
Wani kuma kanyi nadama ce kan wani zaluncin da ya aikata, wanda hakan na daga cikin sharadin tuba kuma abinda Allah ke so. Saboda haka zai sami lada kan wannan aiki nasa na nadamar da yayi.
Sai dai kuma yin nadamar kan yafiyar da yayi shine mafi alkhairi fiye da wanda yayi shi kan zalunci, domin abinda ya aikata da farkon aikin alkhairi ne, shi kuma wannan aikin sharri ne.
" KUYI YAFIYA SAI KU SO JUNA ." (In ji Manzon Allah S. A. W. W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
31st December, 2020/ 17th Jimada-Ulah, 1442.