Burinsu a ko yaushe shine; nuna gazawar 'yan uwa !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MUMININ QWARAI SHINE WANDA YA SHAGALTU DA GAZAWAR KANSA 


Addinin muslimci addini ne na gaskiya wanda Manzon Allah (S. A. W. W) ya koyar damu yadda ake yinsa kuma ya nuna mana abubuwan da za su bata shi. Cikin abubuwan da ya koyar damu (S. A. W. W) shine duk wani aiki da za ayi cikin muslimci ba a samun ladarsa har sai an tsarkake niyya tare da yinsa bisa ikhlasi. 


Da yawa mutum kan bata ayyukansa tun daga niyya, duk wanda zai yi aiki da nufin wani ya gani ko ya yabe shi ko kuma ya ji a jikinsa ai babu wani kamarsa, to, aikinsa ya baci. 


Babu laifi idan kaga wani na gazawa ta wani janibi ka nusar da shi ko kayi masa nasiha, yin hakan zai sa ka sami lada ko da ace mutum bai yi aiki da abinda ka fada masa ba. 


Sai dai kuma akwai wasu mutane masu tafiya cikin kura-kurai amma ba sa yin la'akari da kansu, a kullum burinsu shine su hangi laifi ko gazawar wani dan'uwansu maimakon shagaltuwa da nasu laifuffukan. 


Abinda yafi muni ma shine, a ko da yaushe burinsu shine su gamsar da wani ko su cusa masa ganin gazawar wani a idanuwansu ta yadda zai zama shine abin tattaunawarsu cikin majalisa. 


Kuma da za ka auna ayyukansu dana wanda suke zagi ko ganin gazawarsa da sai ka tarar ayyukansa yafi nasu alkhairi sau dubu (1000), domin ya kanyi komai nasa da ikhlasi ne . Su wadannan munafukai ne cikin kowacce irin tafiya, kuma Allah na sanin dukkan manufofinsu na boye dana bayyane. 


Allah ya zargi irin wannan aiki nasu inda yake cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ ٨٧ 


ٱلَّذِينَ يَلۡمِزُونَ ٱلۡمُطَّوِّعِينَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ فِي ٱلصَّدَقَٰتِ وَٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهۡدَهُمۡ فَيَسۡخَرُونَ مِنۡهُمۡ سَخِرَ ٱللَّهُ مِنۡهُمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ ٩٧


" SHIN, ASHE BASU SAN ALLAH NA SANIN SIRRINSU DA GANAWARSU (a boye bane), KUMA LALLE ALLAH SHINE MASANIN (abubuwan) FAKE BANE ?


SUNE MASU AIBANTA MASU YIN ALHERI DAGA MUMINAI CIKIN DUKIYOYIN SADAQA, DA WADANDA BASU SAMU (abin bayarwa ba) FACE IYAWARSU, SAI SUNA YI MUSU IZGILI. ALLAH NA YIN IZGILI GARE SU. KUMA SUNA DA AZABA MAI RADADI !"


     (TAUBA:78-79)


Ni dai banga ribar da mutum zai samu ba don ya gamsar da wani gazawar dan'uwansa, sai dai in yana yi don raba kan al'umma ce da kuma yiwa Yahuduwa aiki, to, anan sai nace lalle yana cin ribar duniya in har yana samun wani abu daga gare su. 


Abinda ya hau kansu kawai shine kowa yayi ta kansa kamar yadda Allah (T) ke fada, 


" KUYI TA KANKU ! WANDA YA BATA BA ZAI CUTAR DAKU BA MATUQAR KUN SHIRYU !"


The only question here is that, are you rightly guided ?


Wannan tambaya ce wacce ba ku isa amsa ta ba, saboda haka sai mu dawo kan gundarin ayar muyi aiki da ita, wato kowa yayi ta kansa !


WANNAN TUNATARWA CE. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


       (08137925034)


1st December, 2020/ 16th Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post