Bazamu manta da Shaheed Ishaq Muhammad Sulaiman ba !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


GWARZO CIKIN WAKILAN SHAFIN MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS 


Ka zama abin alfahari gare mu yaa shaheed Ishaq Muhammad Sulaiman, domin har zuwa yau Allah bai azurta wani wakili cikin wakilan shafin Ma'asumah da yin shahadah ba koma bayanka. 


Shaheed Ishaq Muhammad Sulaiman jarumi ne kuma gwarzo mai qwazo cikin wakilan shafin Ma'asumah wanda ya bada lokacinsa da dukiyarsa wajen tallafawa harkar muslimci a Nigeria wacce Sayyid Zakzaky (H) ke jagoranta. 


Abinda yafi komai muhimmanci cikin rayuwarsa shine, ya bada ransa wajen fafutukar sai Gwamnatin zalunci wacce Buhari ke jagoranta ta saki Sayyid Zakzaky (H) wanda take riqe dashi bisa zalunci na tsahon shekaru biyar har da watanni biyu da rabi a qidayar muslimci. 


Ya samu shahada ne a irin wannan rana 27-12-2019 wanda yanzu haka yana da shekara guda kenan da yin shahadah. 


Yaa Allah ka karbi shahadarsa kasa ya zama mai ceton zuriyarsa, ka kuma bamu makoma irin tasa. 


BA ZA MU TABA MANTAWA DA KAI BA YAA SHAHEED ISHAQ MUHAMMAD SULAIMAN !


😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


Wannan kuka ne na baqin cikin rabuwa da kai don irin gudumawar da kake bayarwa ba wai baqin cikin takaicin rashinka muke yi ba .


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


        (08126385470)


27th December, 2020/ 13th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post