@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN KAJI KANA SON MAQIYAN AHLUL-BAIT (A. S) KAI MA MAQIYINSU SU
Kamar dai yadda hausawa ne ke wata karin magana wai " BA A HADA GUDU DA SUSAN QAFA ". Tabbas wannan karin magana yayi daidai, domin in har kaga mutum na gudu kuma yana sosa qafarsa, to, kawai kace ba abin tsoro ya gani ba !
Ko da a halin yanzu za ka kaji cewa wai wane yana sonka amma kuma amini ne ko masoyin maqiyinka, to, idan ya kasance haka kayi taka-tsan-tsan da shi, domin wataran zai iya ha'intarka ko cutar da kai ba tare da ka sani ba.
Ya zo cikin Tafsirul-Qummy, cikin riwayar Abu Jaruud, daga Abu Ja'afar (A. S) cikin fadinsa (S. W. A);
- فس، تفسير القمي فِي رِوَايَةِ أَبِي الْجَارُودِ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع فِي قَوْلِهِ :
" ALLAH BA YA SANYA ZUCIYA BIYU GA MUTUM CIKIN QIRJINSA ."
" ما جَعَلَ اللَّهُ لِرَجُلٍ مِنْ قَلْبَيْنِ فِي جَوْفِهِ ."
" Ya riqa so da wannan yayi qiyayya da wannan. Amma su masoyanmu (dole) su kebe soyayyarmu kamar yadda suke kebe Zinari daga (shafar) wuta , babu haduwa cikinsa.
Duk wanda yayi nufin sanin (haqiqanin ) soyayyarmu (tare da shi), to, ya jarrabi zuciyarsa, idan har soyayyar maqiyinmu tayi tarayya da son mu (a cikinta), to, ba ya tare damu, muma ba ma tare da shi. Kuma Allah maqiyinsu ne da Jibrilu da Mika'ilu, kuma Allah maqiyi ne ga kafirai ."
فَيُحِبَّ بِهَذَا وَ يُبْغِضَ بِهَذَا فَأَمَّا مَحَبَّتُنَا[1] فَيُخْلِصُ الْحُبَ[2] لَنَا كَمَا يَخْلُصُ الذَّهَبُ بِالنَّارِ لَا كَدَرَ فِيهِ مَنْ[3] أَرَادَ أَنْ يَعْلَمَ حُبَّنَا فَلْيَمْتَحِنْ قَلْبَهُ فَإِنْ شَارَكَهُ[4] فِي حُبِّنَا حُبَّ عَدُوِّنَا فَلَيْسَ مِنَّا وَ لَسْنَا مِنْهُ وَ اللَّهُ عَدُوُّهُمْ وَ جَبْرَئِيلُ وَ مِيكَائِيلُ وَ اللَّهُ عَدُوٌّ لِلْكَافِرِينَ[5].
A wata riwaya makusanciyar ta Ibn Isah daga Bazandiyyu yace, Ridha (A. S) ya rubuto zuwa gare ni yace, Abu Ja'afar (A. S) yace,
" DUK WANDA KE FARIN CIKIN KADA WANI HIJABI YA SHIGA TSAKANINSA DA ALLAH HAR YA KALLI ALLAH (ra'ayul-Ain), SHI MA ALLAH (T) YA KALLE SHI, TO, YA JIBINCI IYALAN MUHAMMAD KUMA YA BARRANTA DAGA MAQIYANSU, KUMA YA CIKA DA LIMAMI DAGA CIKINSU. TO, IDAN SHI YA KASANCE HAKA, ALLAH ZAI YI DUBI ZUWA GARE SHI, KUMA (shi ma) YA KALLI ALLAH ."
2- ب، قرب الإسناد ابْنُ عِيسَى عَنِ الْبَزَنْطِيِّ قَالَ: كَتَبَ إِلَيَّ الرِّضَا ع قَالَ أَبُو جَعْفَرٍ عَلَيْهِ السَّلَامُ مَنْ سَرَّهُ أَنْ لَا يَكُونَ بَيْنَهُ وَ بَيْنَ اللَّهِ حِجَابٌ حَتَّى يَنْظُرَ إِلَى اللَّهِ[6] وَ يَنْظُرَ اللَّهُ إِلَيْهِ فَلْيَتَوَلَّ آلَ مُحَمَّدٍ وَ يَبْرَأْ[7] مِنَ عَدُوِّهِمْ وَ يَأْتَمَّ بِالْإِمَامِ مِنْهُمْ فَإِنَّهُ إِذَا كَانَ كَذَلِكَ
نَظَرَ اللَّهُ إِلَيْهِ وَ نَظَرَ إِلَى اللَّهِ[8]
(5) تفسير القمّيّ: 514.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج27، ص: 52
Amma duk da haka a yanzu za kaji wasu har wa'azi suke yi cikin kafafen sadarwa suna nuna cewa su masoya Manzon Allah (S. A. W. W) ne da Iyalan gidansa (A. S), amma kuma sai kaji suna yabon maqiya kuma makasan Iyalan wannan gida (A. S) . To, suna nufin su zuciyoyi biyu Allah ya sanya musu a qirjinsu wadanda ko wacce da kalar abinda take so ?
Amsa dai kawai ita ce, su maqiyan Iyalan gidan Manzon Allah ne ma su yaqarsu da harsunansu da dukiyoyinsu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08126385470)
16Th December, 2020/ 1st Jimada-Ula, 1442