Annabi Isah Al-Masihu (As) bai ce shi Allah bane, Saboda tausayinsa ga al'umma, yana neman Allah ya gafarta musu !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Haihuwar Al-Masihu Isah dan Maryama (A. S) ta kasance abin al'ajabi wacce ta sha bamban da haihuwar duk 'ya'yan Adamu (A. S), domin misalinsa tamkar misalin Annabi Adam (A. S) ne a halitta kamar yadda Allah (T) ya bamu labari, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" إِنَّ مَثَلَ عِيسَىٰ عِندَ ٱللَّهِ كَمَثَلِ ءَادَمَۖ خَلَقَهُۥ مِن تُرَابٖ ثُمَّ قَالَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ ." ٩٥


" LALLE MISALIN ISAH A WAJEN ALLAH KAMAR MISALIN ADAMU NE, (Allah) YA HALICCE SHI DAGA LAKA, SA'AN NAN YACE, " KASANCE " SAI YA KASANCE ."


      (AL-IMRAAN :59)


Annabi Adam (A. S) an halicce shi da laka ba Uwa ba Uba, haka ma Annabi Isah (A. S) an halicce shi ta hanyar Uwa ba Uba wanda hakan bata taba kasancewa ga wani daga cikin 'ya'yan Adamu (A. S). 


Wannan dalili yasa Nasara ke cewa wai shi Allah ne alhali ba shi ya fada musu haka ba. Sun riqe shi abin bauta alhali shi ma kansa bautar Allah yake. Shi kuwa wanda ya kasance yana bautawa wani bai cancanci a bauta masa ba. 


TUHUMAR ALLAH GA ANNABI ISAH AL-MASIHU (A. S) 


Allah (T) na cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" وَإِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ءَأَنتَ قُلۡتَ لِلنَّاسِ ٱتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيۡنِ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ مَا يَكُونُ لِيٓ أَنۡ أَقُولَ مَا لَيۡسَ لِي بِحَقٍّۚ إِن كُنتُ قُلۡتُهُۥ فَقَدۡ عَلِمۡتَهُۥۚ تَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِي وَلَآ أَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِكَۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ ٦١١ 


" KUMA A LOKACIN DA ALLAH YACE, " YAA ISAH 'DAN MARYAMA, SHIN, KAI NE KA CEWA MUTANE " KU RIQE NI NI DA MAHAIFIYATA A MATSAYIN ABIN BAUTA GUDA BIYU KOMA BAYAN ALLAH ? " YACE, " TSARKI YA TABBATA A GARE KA , BA YA (taba) KASANCEWA GARE NI NA FADI ABINDA BA NI DA HAQQI A KANSA, IN NA KASANCE NA FADE SHI HAQIQA (Allah) KA SAN SHI. KAINE KASAN ABINDA KE CIKIN ZUCIYATA, NI BAN SAN ABINDA KE CIKIN ZUCIYARKA BA, LALLE JAQIQA KAI KAINE MAFI SANIN ABINDA KE BOYE ."


مَا قُلۡتُ لَهُمۡ إِلَّا مَآ أَمَرۡتَنِي بِهِۦٓ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۚ وَكُنتُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا مَّا دُمۡتُ فِيهِمۡۖ فَلَمَّا تَوَفَّيۡتَنِي كُنتَ أَنتَ ٱلرَّقِيبَ عَلَيۡهِمۡۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ ٧١١ 



" NI DAI BAN FADA MUSU (komai ba) FACE ABINDA KA UMARCENI (a kansa) CEWA, " KU BAUTAWA ALLAH UBANGIJINA KUMA UBANGIJINKU . NI DAI NA KASANCE MAI SHADA NE A KANSU YAYIN DA NAKE CIKINSU (ban san sun riqeni ni da mahaifiyata abin bautawa ba), AMMA YAYIN DA KA KARBI RAINA KAINE KA KASANCE MAI TSARO A KANSU (ka san abinda suka yi a bayana), KUMA KAI MAI (bayar da) SHAIDA NE AKAN KOMAI ."


Saboda tausayinsa da kuma qaunarsu da samun rahma yasa yake cewa Ubangiji, 


 "إِن تُعَذِّبۡهُمۡ فَإِنَّهُمۡ عِبَادُكَۖ وَإِن تَغۡفِرۡ لَهُمۡ فَإِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ ٨١١


" IDAN KAYI MUSU AZABA (ai) BAYINKA NE, IDAN KUWA GA GAFARTA MUSU (kan abinda suka yi ai dama) KAI KAINE MABUWAYI MAI HIKIMA (cikin dukkan hukuncinKa) ."


     (MA'IDAH :116-118


MADALLAH DA ZUWAN MAI TAUSAYIN AL'UMMAR DA AKA AIKO SHI GARE SU. 


                    ☝🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


26th December, 2020/ 12th Jimada-Ulah, 1442.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post