Shi lokaci kamar faduwar rana ne, idan ta fadi ba wanda ya isa ya dawo da ita baya, saidai a jira ta gobe Kuma, idan ka bari lokacinka ya wuce baka moresa ba, baka anfanesa da abubuwan da zasu taimakeka duniya da lahira ba, to idan ya tafi bafa ranar da zaya sake dawowa gareka, lokaci yana wucewa ne kamar budewar littafi, duk page din daka wuce tofa tabbas ka wucesa, saidai ana samun banbanci, wasu sukan buda nasu littafin ne su rika kallo kallo kawai aciki, ba tare da sun karanta abinda page din ya kunsa ba, wasu kuma suna bin page din rayuwarsu ne a natse a tsanake, suga abinda yakeda bukatar gyara da kuma ayyukan dake bukatar a cigaba da yinsu, hakan yake saka kake ganin masu karanta Page din rayuwarsu bawai suna kallo kallo ba kawai, suke samun sauyi a kowane lokaci a kuma cikin komai.
Hausawa na cewa wai ANA BIKIN DUNIYA AKE NA KIYAMA tabbas hakane, domin don anyi rasuwa anguwa a misali, hakan baya hana kaga an haihu ko ana biki a cikin anguwar, kuma dole masu wannan hidimar suyi farin ciki, wa'yanda akayiwa rasuwa kuma suyi kuka, ita rayuwa abin dubawa ne a kowane lokaci, sai ana sara ana duban bakin gatari, idan baka anfani rayuwarka ba, to fa yadda kowa yake rasuwa kaima rasuwa zakayi, don baka anfani lokacinka ba hakan baisa mutuwa tace to bari saika anfanesa sannan na daukeka, a'a kamayi anfani da lokacin wurin neman lahira da duniyar duka wane aka cika, bare kuma ka rungume hannu bakayi ba.
Lokacin mu yana da matukar muhimmanci garemu dama sauran al'umma, domin idan cikin lokacinmu mukayi abinda ya kamata to zamu zama abin koyi ne ga sauran al'umma, kenan idan mun yi aikin da bai dace ba zamu jawa kanmu ne da al'ummar mu, domin idan muka samar da mai kyau kwara daya, to muna saran ta dalilinsa mu samu masu kyau da yawa, to kaga kenan idan mun samar da akasin hakan muna nufin samar da marasa kyaune da yawa acikin al'ummar mu.
Yanada kyau mu rika tuna cewa itafa rayuwar duka an bamu aro ne, kuma shi kayan aro a kowane lokaci maishi zaya iya ansar abinsa, ka shirya baka shirya ba, idan ya tashi ansa kawae xaya ansa ne sauran ya rage gare ka, kayi abinda ya kamata ko A'a, shi ba ruwansa da hakan kaine ya aramawa ya kuma baka dama don ka gina goben ka da lahirarka.
Zan cigaba insha Allah
✍️ Zarah A Zamsarf