An ƙara yiwa yan uwa na garin Jos babban rashi: Allah ya yiwa Mardiyya diyar wakilin yan uwa Malam Shehu Laranto rasuwa, bayan tayi jinya na yan kwanaki !!!


 

A yau Alhamis wanda yayi daidai da 10\12\2020 Allah yayi wa Mardiya Shehu Rasuwa wanda ta fara jinya kwanaki tara da suka gabata. 


Mardiya ta kasance diyace ta 7 ga Wakilin Unguwan Laranto wato Malam Shehu, 

Shekararun ta 11 tayi a duniya. 


Malam Sulaiman Aliyu shine ya jagoranci Jana'izar Margariya kuma an binneta a Makabartar Narkuta. 


Muna fatan Allah ya karbi uzurin ta ya yafe mata kurakuranta mukuma in tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani. 


Allah ya gaggauta fito mana da Jagoranmu Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) daga hanun Azzalumai. 


Daga Almustapha A Abdullahi Jos

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post