@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
WASIYYAR ANNABI (S. A. W. W) GA IMAM ALI (A. S) KAN ABINDA ZAI FARU A BAYANSA
Jahilci ba ya taba zama hujja ga mutum kuma bai kamata ya zama jagora gare shi ba cikin komai nasa na rayuwa ko addini.
Har hujja za kaji suna kafawa wai in har da gaske ne Imamanci haqqin Aliyu ne a bayan Annabi (S. A. W. W) me yasa bai yaqe su ya qwace haqqinsa ba alhali kowa ya san cewa shi jarumi ne ?
To, mu za mu baku hujja ne da abinda ya fito daga bakin Manzon Allah (S. A. W. W). Ku biyo mu cikin nutsuwa da karatu na fahinta don samun gamsuwa.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
SULAIMUN YA BADA LABARI
Yace,
" Ina cewa, na samu cikin asalin KITABIL -HILALIY misalinsa zuwa fadinsa,
" GARE KA AKWAI ABIN KOYI MAI KYAU DAGA HARUNA YAYIN DA YA CEWA 'DAN'UWANSA MUSA, " LALLE FA MUTANE SUN RAUNATANI KUMA HAR MA SUNYI KUSA SU KASHE NI ."
Sulaiman yace, Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S) ya bani labari cewa yace,
" NA KASANCE INA TAFIYA TARE DA MANZON ALLAH (S. A. W. W) CIKIN WASU HANYOYIN MADINAH SAI MUKA JE KAN WANI LAMBU, SAI NACE YAA MA'AIKIN ALLAH ! MENENE YAFI KYAU DAGA LAMBUN NAN ? YACE (S. A. W. W),
" ABINDA YAFI KYAU, AI KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU A ALJANNAH ."
SA'AN NAN MUKA JE GA WANI LAMBUN NA DABAM, SAI NACE, YAA MA'AIKIN ALLAH ! MENENE YAFI KYAU DAGA LAMBUN NAN ? YACE,
" ABINDA YAFI KYAU CIKINTA KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU A ALJANNAH ."
HAR SAI DA MUKA JE KAN LAMBU NA BAKWAI INA CEWA MENENE YAFI KYAU A CIKINSU YANA CEWA, " ABINDA YAFI KYAU CIKINSA KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU A ALJANNAH ."
TO, A YAYIN DA MUKA KAUCE DAGA KAN HANYA SAI YA RUNGUME NI SA'AN NAN YA FASHE DA KUKA. SAI NACE, YAA MA'AIKIN ALLAH ! MENENE YA SA KA KUKA ? YACE,
" QIYAYYAR DAKE CIKIN ZUKATAN MUTANE, AMMA BA ZA SU BAYYANAR DA ITA GARE KA BA HAR SAI DAI A BAYANA , QIYAYYAR BADR DANA UHUD ."
NACE, INCE DAI AKWAI AMINCI CIKIN ADDININA ? YACE,
" AKWAI AMINCI CIKIN ADDININKA. KUMA KAYI BUSHARA YAA ALIYU, LALLE RAYUWARKA DA MUTUWARKA TARE DANI, KUMA KAINE 'DAN'UWANA, KUMA KAINE WASIYYINA, KUMA KAINE ZABABBENA KUMA WAZIRINA KUMA MAI GADONA KUMA MAI TSAYAWA A MADADINA, KUMA KAINE ZA KA BIYA MIN BASHINA, MAI BINNE GAWATA, KUMA KAINE MAI KUBUTAR DA ZURIYATA, KUMA MAI BAYAR DA AMANATA, KUMA MAI YIN YAQI AKAN SUNNATA GA MASU WARWARE ALQAWARI DAGA AL'UMMATA DA AZZALUMAI DA KUMA 'YAN TAWAYE .
KUMA KAI A WAJENA KAMAR MISALIN HARUNA NE A WAJEN MUSA, KUMA GARE KA AKWAI ABIN KOYI MAI KYAU DAGA HARUNA YAYIN DA MUTANENSA SUKA RAUNATA SHI HAR MA SUKA YI KUSAN KASHE SHI. KAYI HAQURIN ZALUNCIN QURAISHAWA GARE KA DA KUMA 'DORUWARSU A KANKA, DOMIN KAI MATSAYIN KAMAR MATSAYIN HARUNA NE WAJEN MUSA DA WADANDA SUKA BI SHI. SU KUMA KAMAR MISALIN 'DAN MARAQI NE DA WADANDA SUKA BI SHI.
DOMIN MUSA YA UMARCI HARUNA YAYIN DA YA KHALIFANTAR DASHI A KANSU, IDAN SUKA BACE KUMA YA SAMI MATAIMAKA YA YAQE SU DASU, IDAN KUMA BAI SAMI MATAIMAKA BA TO, YA KAME HANNUNSA KUMA YA TSARE JININSA KADA YA RABA TSAKANINSU.
YAA ALIYU ! BABU WANI ANNABI DA AKA AIKO SHI FACE WASU SUN SALLAMA MASA DA DADIN RAI, WASU MUTANE NE KUMA BISA DOLE (suka bi shi), SAI KUMA ALLAH YA 'DORA WADANDA SUKA SALLAMA BISA DOLE AKAN WADANDA SUKA SALLAMA BISA SON RANSU, SUKA KASHE SU DON LADANSU YA GIRMAMA.
YAA ALIYU ! LALLE SHI BABU WATA AL'UMMAR DATA SABA A BAYAN ANNABINTA FACE WADANDA KE KAN BATANTA SUN 'DORU AKAN MA'ABOTA GASKIYA. KUMA LALLE ALLAH YA HUKUNTA RARRABUWA DA SASSABAWA CIKIN WANNAN AL'UMMA SANNAN LABARI YA QULLU CIKIN MAGANARSA (S. W. A). HAQURI ZA KAYI AKAN BALA'INSA DA SALLAMAWA DA YARDA DA HUKUNCINSA ."
22- أَقُولُ وَجَدْتُ فِي أَصْلِ كِتَابِ الْهِلَالِيِّ، مِثْلَهُ إِلَى قَوْلِهِ وَ لَكَ بِهَارُونَ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ إِذْ قَالَ لِأَخِيهِ مُوسَى إِنَّ الْقَوْمَ اسْتَضْعَفُونِي وَ كادُوا يَقْتُلُونَنِي[38] قَالَ سُلَيْمٌ وَ حَدَّثَنِي عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ ع أَنَّهُ قَالَ: كُنْتُ أَمْشِي مَعَ رَسُولِ اللَّهِ ص فِي بَعْضِ طُرُقِ الْمَدِينَةِ فَأَتَيْنَا عَلَى حَدِيقَةٍ فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ مَا أَحْسَنَهَا مِنْ حَدِيقَةٍ قَالَ ص مَا أَحْسَنَهَا وَ لَكَ فِي الْجَنَّةِ أَحْسَنُ مِنْهَا ثُمَّ أَتَيْنَا عَلَى حَدِيقَةٍ أُخْرَى فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ مَا أَحْسَنَهَا مِنْ حَدِيقَةٍ قَالَ مَا أَحْسَنَهَا وَ لَكَ فِي الْجَنَّةِ أَحْسَنُ مِنْهَا حَتَّى أَتَيْنَا عَلَى سَبْعِ حَدَائِقَ أَقُولُ يَا رَسُولَ اللَّهِ ص مَا أَحْسَنَهَا وَ يَقُولُ لَكَ فِي الْجَنَّةِ أَحْسَنُ مِنْهَا فَلَمَّا خَلَا لَهُ الطَّرِيقُ اعْتَنَقَنِي ثُمَّ أَجْهَشَ بَاكِياً وَ قَالَ بِأَبِي الْوَحِيدُ الشَّهِيدُ فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ مَا يُبْكِيكَ فَقَالَ ضَغَائِنُ فِي صُدُورِ أَقْوَامٍ لَا يُبْدُونَهَا لَكَ إِلَّا مِنْ بَعْدِي أَحْقَادُ بَدْرٍ وَ تِرَاتُ أُحُدٍ قُلْتُ فِي سَلَامَةٍ مِنْ دَيْنِي قَالَ فِي سَلَامَةٍ مِنْ دِينِكَ فَأَبْشِرْ يَا عَلِيُّ فَإِنَّ حَيَاتَكَ وَ مَوْتَكَ مَعِي وَ أَنْتَ أَخِي وَ أَنْتَ وَصِيِّي وَ أَنْتَ صَفِيِّي وَ وَزِيرِي وَ وَارِثِي وَ الْمُؤَدِّي عَنِّي وَ أَنْتَ تَقْضِي دَيْنِي وَ تُنْجِزُ عِدَاتِي عَنِّي وَ أَنْتَ تُبْرِئُ ذِمَّتِي وَ تُؤَدِّي أَمَانَتِي وَ تُقَاتِلُ عَلَى سُنَّتِي النَّاكِثِينَ مِنْ أُمَّتِي وَ الْقَاسِطِينَ وَ الْمَارِقِينَ وَ أَنْتَ مِنِّي بِمَنْزِلَةِ هَارُونَ مِنْ مُوسَى وَ لَكَ بِهَارُونَ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ إِذِ اسْتَضْعَفَهُ قَوْمُهُ وَ كَادُوا يَقْتُلُونَهُ فَاصْبِرْ لِظُلْمِ قُرَيْشٍ إِيَّاكَ وَ تَظَاهُرِهِمْ عَلَيْكَ فَإِنَّكَ بِمَنْزِلَةِ هَارُونَ مِنْ مُوسَى وَ مَنْ تَبِعَهُ وَ هُمْ بِمَنْزِلَةِ الْعِجْلِ وَ مَنْ تَبِعَهُ وَ إِنَّ مُوسَى أَمَرَ هَارُونَ حِينَ اسْتَخْلَفَهُ عَلَيْهِمْ إِنْ ضَلُّوا فَوَجَدَ أَعْوَاناً أَنْ يُجَاهِدَهُمْ بِهِمْ وَ إِنْ لَمْ يَجِدْ أَعْوَاناً أَنْ يَكُفَّ يَدَهُ وَ يَحْقُنَ دَمَهُ وَ لَا يُفَرِّقَ بَيْنَهُمْ يَا عَلِيُّ مَا بَعَثَ اللَّهُ رَسُولًا إِلَّا وَ أَسْلَمَ مَعَهُ قَوْمُهُ طَوْعاً وَ قَوْمٌ آخَرُونَ كَرْهاً فَسَلَّطَ اللَّهُ الَّذِينَ أَسْلَمُوا كَرْهاً عَلَى الَّذِينَ أَسْلَمُوا طَوْعاً فَقَتَلُوهُمْ لِيَكُونَ أَعْظَمَ لِأُجُورِهِمْ يَا عَلِيُّ إِنَّهُ مَا اخْتَلَفَتْ أُمَّةٌ بَعْدَ نَبِيِّهَا إِلَّا ظَهْرَ أَهْلُ بَاطِلِهَا عَلَى أَهْلِ حَقِّهَا وَ إِنَّ اللَّهَ قَضَى الْفُرْقَةَ وَ الِاخْتِلَافَ عَلَى هَذِهِ الْأُمَّةِ وَ سَاقَ الْخَبَرَ إِلَى قَوْلِهِ وَ صَبْراً عَلَى بَلَائِهِ وَ تَسْلِيماً وَ رِضًا بِقَضَائِهِ[39
(1) كمال الدين ص 262- 264.
(2) كتاب سليم 69- 70. مع أدنى تفاوت.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج28، ص: 55
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
29th December, 2020/ 15th Jimada-Ulah, 1442.
Tags:
Tunatarwa