Duk gidan da aka zauna lafiya, to tabbas ma'auratan dake ciki ne suka gyara ma'amalar su da junansu, ku zama daya daga cikin wayannan gidajen mana, tahanyar farantawa junanku, biyawa junanku bukatunsu, hakuri da junanku kulawa da nunawa junanku so da kauna, nasani cikin Kashi dari na ma'auratan da ke akwai, to kaso 90 sunyi aure ne suna so da kaunar junansu, sauran goman sune za'ace anyiwa auren dole ko kuma auren zabi(iyayenka su zaba maka mata kuma ka amince da hakan bawai sunyi maka tilas bane, a'a kaima ka amince da hakan), Amma har mamaki nakeyi yadda akeyin auren cikeda farin ciki da kagara, wai amma bayan yan watannin ko yan shekaru kawai sai kajisu suna kuka da junansu, wance kaza takeyi batada kirki,ko wane kaza yake bayada kirki, idan akayi rashin sa'a shedan ya shigo, saidai kawai wata rana kayi sallama gidansu ka ganta zaune , abin takaicin wai ya saketa ne.
Tambayar da nakeyiwa kaina duk sanda naga irin haka ko kuma naji labarin irin hakan shine, to duk ina so da kaunar da sukewa junansu ta tafi, wani lokaci idan na duba sai naga tabbas ta cancanci saki, saboda ta dauko wasu halayen da bazasu taba sawa a zauna lafiya ba, wani lokaci kuma sai inga tabbas laifin mijin ne, amma saboda shi ikon sakin yake hannunsa kawai sai ya yanke hukunci .
Dagaske ne a cikin 'yan shekarun nan sakin aure yayi yawa, kuma wallahi idan aka duba laifin kowa akwai hannunsa a ciki, tun daga kan iyaye, mijin, har kan matar, kuma wani lokaci son zuciya duk ke haifar da hakan , mun maida aure kamar wasa da anyishi yau wata uku, shekara daya biyu kin dawo gidanku. Ku ko kishi ma bakwaji?......
Ni wallahi ko don kar ya zamana namiji sama da daya yasanni a matsayin mace, wallahi zanyi iya kokarina wurin sama mana da rayuwa mai inganci, amma fa kaima akwai sa hannunka aciki, wurin dorewar hakan,saboda ko kowa baya kishina ni ina kishin kaina.
Akarshe ina ma masu aure, da masu niyyar yi fatan kasancewa cikin inagantacciyar rayuwa, da samar da inagantacciyar al'umma daga garesu, abin alfahari ga duniya baki daya. Ngd sosai da lokacinku da kuka bani. Allah ya bamu ikon gyarawa baki daya
_Zarah A Zamsarf