Zaman aure wani abune wanda bakowa ke gane hakikanin sa ba, sai wanda ya shiga cikinsa, amma wani lokaci akawai matsalolin da wanda ke cikin baya kula dasu, wanda ke waje yafi fahimtar hakan. kamar laifi ne, ba kasafai kake gane rashin dacewar abu ba idan kana ciki, amma da zarar ka fita to zaka iya gane komeye rashin dai_dai din, abin lura garemu mata da maza!!
Gare ku yan uwa mata, ina shawartarmu da mu kula kuma mu lura da wannan, duk da ba duka aka taru aka zama daya ba, yana da kyau idan kin fahimci abinda mijinki yafi so a tare dake, to kiyi iya kokarinki karki bari wannan abun ya rabu dake, afuwan ina magana ne akan personal abubuwa, banda so wanda Allah ya bama kowane namiji akan mace, to kuma Allah ya banbanta kowane namiji akwai abinda yafi so ko kuma yafi birgeshi ajikin mace, idan har kin fahimci ko meye yafi so atare dake, to karki bari wannan abun ya rabu dake. Idan kuma bakidashi kiyi kokari ki sameshi.
Tabbas indai ana kwana ana tashi to tsufa zakiyi wata Rana, sannan banda wannan akwai haihuwa, afuwan ni bana saka haihuwa cikin abinda ke sawa mace ta zama koma baya a wurin mijinta, saboda kafin da kuma bayan haihuwa duk indai har kinsan wacece ke to zaki gyara kafin haihuwar da kuma bayanta, saboda ga abubuwan gyaran jiki nan a ko'ina idan kinada bukata, matsalolin da mata ke fuskanta agidajen aurensu, wannan na daya daga cikin matsalar, sai muce wai da mun haihu shikenan mun tsufa, ba sai mun rika gyarawa ba. Wai mun barwa 'ya'yanmu, To bari na tuna maki idan kin manta, idan mijinki surar jikinki tafi birgeshi dake ( shape)to da kin bari kin lalace wallahi duk yanda yake sonki wallahi saiya rage, kuma ahankali zaya cigaba da ragewa ne.
Akwai abubuwan da su dama suna zaman wajibine a wurin duk macen data san ko wacece ita, kamar tsafta,iya girki, sanin yadda zaki zauna da mijin,ladabi, biyayya dadai sauran su da dama, amma banda su kina bukatar sanin waye mijinki ?,meyafi so?, Wane lokaci yafiso idan kinyi masa laifi ki bashi hakuri? Wane kalan kaya ko abinci yafi so? Wane kalma yafi jin dadi idan kin fada masa kuma wane ne baya so?dama wasu abubuwa da daman gaske.
Kar kice wai ai tunda dai yanzu munyi aure basai na rika yin wasu abubuwan ba, kamar misali : kwalliya, karkice ai tunda nayi aure basai nayi ba aidai yasan inayi, to idan kwalliyan nan yafi birgeshi dake fa? kuma shi duk sanda zaya zo fira wurinki tsaf yake iskeki, wato saboda a lokacin kinaso ya kara sonki ne ko?, amma da anyi auren saiki daina, ina yayi magana kice ai aikine yayi maki yawa ko wani abu da yayi kamada haka, sorry kuma mazan da naku laifin insha Allah zan danyi magana akai.
Nidai nasani mace gaba dayanta anyita ne saboda namiji, kuma duk kyawun fuska ko jikin da Allah ya baki to wallahi saboda mijinki ya baki, wannan dan rubutun bazaya iya fadar komai ba wallahi, amma ina rokonki da don girman Allah kisan wacece ke a wurin mijinki, duk fa yanda mijikin yazama to wallahi ko kinso ko kin ki akwai sa hannunki, domin ance namiji ba'a taba gama rainonsa, mahaeifiya na gamawa ne ta mikawa mata, to idan bakisan ciwon kanki ba taya zaki san ciwon mijinki har ki gyara shi.
Insha Allah zan dan kara cewa wani abu acikin rubutuna na gaba.
_Zarah A. Zamsarf