Daga Nasir Isa Ali
--
--Manjo Janar Yaakov Amidror (murabus)
--
Tsohon babban Hafsan sojan HK.Israila Mr.Yaakov Amidror tsohon sojan IDF ne (yan mamaya) ya rike mukaman da dama a lokacin da yake aikin soja ciki har da sashin leken asiri da kuma nazarin dubarun yaki,musamman da kungiyoyin GWAGWARMAR. Bayan yayi murabus ya koma yana koyar da dubarun yaki a makarantun sojan Israiala har ya kai ga rike mukamin babban mashawarci na kasa ga Firaministan Israiala,tare da bada shawara kan dubarun yaki.
-
Ya bayyana cewar,bayan yake yake na zahiri wanda muka yi a baya da kungiyar HAMAS,HIZBULLAH,JIHADUL ISLAMY da sauransu,sai muka lura da cewar ashe banda karfin wadannan kungiyoyin na zahiri, to akwai abinda ke tunzurasu tare da kara musu komaji a boye.
Wannan ne yasa muka sake zama domin mu yi nazari mai fadin gaske a kan wadannan kumgiyoyin.
Mr.Yaakov Amidror
Ya bayyana cewar,sun yi nazari mai zurfi sannan sosai sai suka gano cewar Kungiyar HAMAS,Hizbullah,jihadul Islamy ba wai kawai kungiyoyi bane kamar kowacce kungiya a'a,mun gano cewar Janar Qassem Sulaimani na Iran ya iya canza musu tunani inda ya mayar dasu suka zama wasu aqidu masu zaman kansu maimakon kallonsu a matsayin kungiyoyi a zahirinsu. Wannan ne yasa muma sai muka canza salon yakar wadannan kungiyoyi din. A baya yaki daya muke yi dasu wato yakin zahiri (na makamai) kuma cushen da muke yi a cikinsu shine don mu samu bayanar yadda zamu yakesu, amma daga baya sai muka gano cewar,yakin ya koma ya zama fuska uku:
-
1-Yakarsu da karfin makamai a zahiri.
2-Yakar aqidarsu (wanda wannan shine yafi wahala kuma yafi kawo nasara,domin muna yakarsu ne a cikin gida wajen hada su fada,yada wasu aqidun na daban,raba kawukasu da haifar da sabanin fahimta da sauransu.
3- sai na uku shine yakar inda ake murda kambun nasu wato Iran da Syria,dole ne mu yunkura domin dakile duk wata hanyar da suke samun tallafin makamai,horo da kuma na tunani.
-
Wannan ne yasa kuke ganin cewar ana daukar lokaci mai tsawo kafin a fito fili a gwabza din,idan har muna samun nasara a bangarorin yakin ruwan sanyi (yakin kwakwalwa) to bamu da bukatar sai mun saka karfi. Idan har kuka ga mun sa karfi,to lallai wani abin muke son raunatawa a zahirance, sai kuma mu koma yakin ruwan sanyi din.
Muna yin amfani da hanyoyi mabambanta masu kuma hatsari,amma duk da hatsarin nasu a hakan muke bi domin cimma nasara. Ba zan iya fadar hanyoyin namu ba,haka ba zan fadi dubarun namu ba.saboda wasu dalilai na kariya.
Muna gwara kansu a cikin gida,muna hada su fada da wasu kungiyoyin na daban,muna yin amfani da farfaganda wajen yada tsegunguma,muna hadasu da gwamnatocin yankin nasu fada.
-
Wadannan hanyoyin sun fi komai samar mana da nasara tare da jefa wa wadannan kungiyoyin shagala da kuma baiwa shugabanninsu ayyukan yi a cikin gida. Saboda sukan dauki lokaci basu gano bakin zaren ba,kuma shugabanninsu sukan shagala wajen neman warware matsalolin da muka cinna musu. Kafin nan kuma mun sake kirkirar wata dubarar ta daban.
Inji Mr.Yaakov Amidror.
------
NIA