Yadda Auwal K/Mashi Ya Lashe Gasar Mawaka Ta Farko A Africa Daga Nigeria!!

Yadda Auwal K/Mashi Ya Lashe Gasar Mawaka Ta Farko A Africa Daga Nigeria!!

Masu Karatu Yau 6-Nov-2020 Muna Tafe Muku da Hirar Da Wakilinmu yayi Da Shararren Mawakin Ashurar Nan Wanda Ya Kware a Fannin Wakokin Juyayi Wato Auwal K/Mashi, Inda Firar Aciki tabo Ratuwarsa A Gidan Yari da Kuma Yadda ya Bayyana Nasarar da yasamu tacin Wannan Gasar da Sauran Muhimman Abubuwan Dazu ku Gani...

Ma'asumah Nigeria News Update

MA'ASUMAH:- "Masu Karatun mu Zasu Ka Bayyana musu Kadan Daga Cikin Tarihin ka ???

K/MASHI:- "Sunana Muhammad Auwal Alhassan k/mashi an haifeni a k/mashi 1980, nayi karatun primary a army children school sai Sheikh abubakar gumi college (kulliya) Sai seminar A Takaice kenan

MA'ASUMAH:- "Miyabaka Shawa kazama Mawaki Kuma waya Koyar Dakai Waka???

K/MASHI:- "(Dariya) babu wanda ya koyamin WaKa ,
kuma wakena ta samo Asaline daga take (slogans) na muzahara inayiwa harisawa daman ni Haris ne dan hakane nasoma Waken chaza mazaje, daga nan sai kuma nasoma Waken Ashura Kuma nafijin dadin waken Ashura fiye da kowane daman idan inayi ji nake tana fitowa daga Ruhina

MA'ASUMAH:- "Munsamu Labarin Ka Zamo na Biyu a  Gasar Mawakan Ashura A Karo na Farko a Africa Ko Zaka Bayyana Masu Karatu Yadda Gasar Take Kuma Suwa Suka Assasata??

K/MASHI:- "Wata cibiyace ta Abbasiyyah dake Kasar Iraqi.
Anyi gasar ne akan waki'ar karbalah, an yarda mutum yayi da daya daga harsunan afurka amma ayi tarjamar Wakar  da harshen Larabci, to amma ni da hausa nayi kuma Saboda kurewar lokaci banyi tarjamar ba.Akwai wasu ka'idojin na daban kamar mintina da kuma shekarun Mai shiga Gasar.

MA'ASUMAH:-"A Nan Nigeria Kai kadai Kashi ga Gasar Ko Kuma Akwai Mawaka da Yawa Aciki, Wane Farin Ciki kaji Lokacin Da Kasamu Sakon Ka Zamo na Biyu a Gasar??

K/MASHI:-" Gaskiya ban iya sani ba tunda online ne Ta (email) ake Tura Komai,  Amma naga wasu mata biyu daga Nigeria 1st and 3rd bangaren mata ne wata Hamida da hakima.


MA'ASUMAH:-" Dawace Waka Kaci Wannan Gasar ??

K/MASHI:-"Sunan Wakar (Husainaaaa) a gidan Yari na rubuta Wakar..

Ku Sauke Wakar Gatanan a Kasa Dannan Photon Nan Mai ja Domin Download dinta

MA'ASUMAH:-"Ya zuwa yanzu Kasamu Yin Waka nawa A Harkar nan Sannan Acikin su Wacece Makandamiyar ka??

K/MASHI:-" gaskiya ban iya kididdigesuba I zuwa yanzu,  Kuma nafi Son su dikka (Dariya)


MA'ASUMAH:-'Ok Sannan ko Zaka Iya Banbanta Mana Cigaban Da Aka Samu a Harkar Waka Da Da Kuma Yanzu da Kuma ci Bayan Da Kasamu???


K/MASHI:-"lallai dai akwai Cigaba a Harkar Waka  Sosai 
ni banga ci baya ba, domin Acan Da a  Harka islama munada karancin Mawakan Ashura amma yanzu akwai su Burjik Masha Allah, Kaga Alhamd Ansamu Cigaba ko A Tanan....
.
.
Ku Gafarce mu Anan Sai Nan Da kwana Biyu Zamu Kawo Muku Cigaban Firar mu Da Auwal K/Mashi Gwarzon Da Yazamo Na Biyu A Gasar Mawakan Ashura Anan Afurka


Ga Kadan Daga Cikin Tambayoyin dazai Amsa Mana Anan Gaba, sai ku biyomu don Jin Tsarabar Gidan Tari da Yadda aka kamasu Har wasu Ababe da Bakuta6a Jiba
________________________
👇👇👇👇
MA'ASUMAH:-"A Cikin Wata Waka Dakayi Mai Suna (Sahiba) Wadda Idan Mai Sauraro yaji zai Fahimci Kayiwa Uwar Gida (Sister) ita ne Wanda Hakan Kamar ya Zamo Karo na Farko, Ko Zaka iya Bayyana kadan Daga Cikin Dalilan Yin Wakar ???


MA'ASUMAH:-"A yadda Duniya ta Sani Kana Dai Daga Cikin Almajiran Sheirk Ibraheem Zakzaky (h) Wadanda Aka Kama a Waki'ar zariya Kuma Har Sukayi Zaman Gidan Yari, Shin Ko Zaka Bamu labarin Yadda aka Kamaku da Rayuwar ku a Gidan Yari ??

Wadannan  Amsoshin Tambayoyin da Sauran Wasu Masu Zuwa Zasu Zo Maku Anan da Kwana Uku Cikin Iyawar Allah (T) a Wannan Shafin na Ma'asumah Nigeria News Update.

Gamai Bukatar Ya Taya Mlm  Auwal K/Mashi Murna Yakira Wannan Number +234 806 318 2784

Muna Godiya muhadu a Cikin Cigaban Hirar 

Daga Wakilinmu Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post