Taqiyya A Aqidar Ahlus-Sunnah: Bambancinmu Da Su Kawai, Su Ba Su Raɗa Mata Suna Bane !!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Abu na farko da ya kamata mu fara bayyanawa anan shine ma'anar Taqiyyah don wadanda basu taba jin sunanta ba su san inda muka dosa. 

               TAQIYYA 

             -----------------

Taqiyyah ita ce boye gaskiyar abinda ke cikin zuciya a bayyanar da sabaninta. Idan kaso za ka iya fassarata da kishiyar manufunci. 

Bambancin su shine, ita taqiyyah mai yinta ne ke cutuwa domin ba ta barinsa ya bayyanar da haqiqanin aqidarsa ko abinda ke zuciyarsa. Munafurcin kuwa mai yinta ne ke amfanuwa yayin da yake cutar da al'umma. 

Yin taqiyyah kan zama haramun a wani lokaci, kamar a gurinda in an yi ta zai iya cutar da muslimci ko kuma taimakon zalunci ko lullube gaskiya d.s . A wani guri kuma takan zama halas, yayin da yinta zai iya zama wata maslaha ta zamantakewar al'umma. 

Shi'ah da Sunnah duk sunyi tarayya cikin wasu ayoyi dake nuni da yin taqiyya, domin dasu suke kafa hujja. Abinda ya bambanta su shine, su Shi'ah sun rada mata suna har suka fitar da ita cikin aqidunsu kuma suke karantar da mabiyansu muhimmancita da matsayinta cikin aqidunsu. Su kuma Sunnah sun kasa rada mata suna, amma kuma suna amfani da ita cikin ayyukansu na ibada/addini ba tare da sun san me suke yi ba. 

Sai dai saboda gurbacewar karatunsu da rashin fahintarsu yasa suke sukar 'yan Shi'ah da cewa wai suna da wata aqidar munafurci wacce suke kira Taqiyyah .

Yanzu zamu kawo riwayoyin sunnah ne mu kafa hujja da yin taqiyyah a muslimci, wataqila su fahinci ashe Taqiyya tushe ne cikin addinin muslimci ba munafurci bane. Idan kuwa munafurcin ne ya zama kowa na munafuncin kenan Shi'ah da Sunnah. 

DAGA CIKIN SAHIHUL BUKHARI 

قول الله تعالى: "إلا من أكره وقلبه مطمئن بالإيمان ولكن من شرح بالكفر صدراً فعليهم غضب من الله ولهم عذاب عظيم" النحل: 106 

"........ SAI DAI WANDA AKA TILASTAWA ALHALI ZUCIYARSA NA CIKE DA IMANI . SAIDAI WANDA YAYI FARIN CIKI DA KAFIRCI, TO, AKWAI FUSHI A KANSA DAGA ALLAH, KUMA GARE SU AKWAI AZABA MAI GIRMA ."

                (NAHL:106)

وقال: "إلا أن تتقوا منهم تقاة" آل عمران: 28 

" FACE KAWAI KU RIQI (wannan abu) DON TSORO DAGA GARE SU A MATSAYIN KARIYA ."

        (AL-IMRAAN:28)

: وهي تقيَّة 

" ITA CE TAQIYYAH (in ji Bukhari). "

وقال: "إن الذين توفاهم الملائكة ظالمي أنفسهم قالوا فيم كنتم قالوا كنا مستضعفين في الأرض - إلى قوله - عفوًّا غفوراً" النساء: 97 - 99 

" LALLE WADANDA MALA'IKU KE 'DAUKAR RAYUKANSU (alhali) SUNA MASU ZALUNTAR KANSU, (sai Mala'ikun) SUCE (musu) : " A CIKIN WANNE HALI KUKA KASANCE ? " Sai wadanda suka zalunci kansu ) SUKA CE : " MUN KASANCE WADANDA AKA RAUNATA A CIKIN QASA ." .............Har zuwa " MAI YAFIYA NE MAI GAFARA ."

           (NISA'I :97-99)

وقال: "والمستضعفين من الرجال والنساء والولدان الذين يقولون ربنا أخرجنا من هذه القرية الظالم أهلها واجعل لنا من لدنك ولياً واجعل لنا من لدنك نصيراً" النساء: 75 

(Yace), " DA WADANDA AKA RAUNANA DAGA MAZA DA MATA DA YARA, SUNA CEWA; " YAA UBANGIJINMU ! KA FITAR DAMU DAGA WANNAN ALQARIYA WACCE MUTANENTA SUKE DA ZALUNCI, KUMA KA SANYA MANA MAJIBINCI DAGA GARE KA, KUMA KA SANYA MANA MATAIMAKI DAGA GUNKA ."

          (NISA'I : 75)

فعذر الله المستضعفين الذين لا يمتنعون من ترك ما أمر الله به، والمكره لا يكون إلا مستضعفاً، غير ممتنع من فعل ما أمر به 

وقال الحسن: التقيَّة إلى يوم القيامة 

Allah yayi uzuri ga raunanan nan da basu hanu daga barin abinda Allah ya hane su da shi ba, da wadanda aka tilastawa, ba ya kasancewa sai ga raunana, ba wadanda suka hanu daga aikata abinda aka yi umarni da shi ba. 

Hassan yace: " Taqiyyah ce har ranar tashin alqiyama ! "

و قال ابن عمر وابن الزبير والشعبي والحسن 

وقال النبي صلى الله عليه وسلم: (الأعمال بالنيَّة) [ر:1] 

Kamar haka Ibn Umar da Ibn Zubair da Sha'abiy da Hassan suka fada . 

Annabi (S. A. W. W) yace, " SHI AIKI NA TARE DA NIYYA CE. "

( Wato, da niyyar mutum ake hukunta shi ba abinda ya bayyana, domin mutum ya kanyi wani aikin ba don Allah ba, saboda haka ba zai sami ladan wannan aiki ba. Kuma zai iya aikata mummuna ba tare da niyya ba, saboda haka sai Allah yayi masa uzuri). 

6541 - حدثنا يحيى بن بكير: حدثنا الليث، عن خالد بن يزيد، عن سعيد بن أبي هلال، عن هلال بن أسامة: أن أبا سلمة بن عبد الرحمن أخبره، عن أبي هريرة: 

أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يدعو في الصلاة: (اللهم أنج عيَّاش ابن أبي ربيعة، وسلمة بن هشام، والوليد بن الوليد، اللهم أنج المستضعفين من المؤمنين، اللهم اشدد وطأتك على مضر، وابعث عليهم سنين كسني يوسف) [ر:961]

Yahya Bn Bukhairi ya bamu labari, Laitheey ya bamu labari daga Khaalid Bn Yazeed ,daga Sa'id Bn Abiy Hilaal, daga Hilaal Bn Usamata : Cewa, Baban Salamata Bn Abdurrahman ya ba shi labari, daga Abu Hurairata cewa: 

Annabi (S. A. W. W) ya kasance yana addu'ah cikin sallah :

" YAA ALLAH ! KA TSERATAR DA IYAASHIN IBN ABIY RABI'ATA, DA SALAMATA BN HISHAAM, DA WALEED BN WALEED. YAA ALLAH ! KA TSERATAR DA RAUNANA DAGA MUMINAI !

YAA ALLAH ! KA TSANANTA KAMUNKA /DAMQAR KA AKAN MASU CUTARWA, KUMA KA AIKO DA SHEKARU A KANSU KAMAR SHEKARUN YUSUFA !"

Wannan shine abinda yazo cikin Sahihul-Bukhari. 

To, bisa tunani da fahinta irin tawa banga wani dalilin da za a dogora da shi ana zagin 'yan Shi'ah cewa suna da aqidar munafurci ba (TAQIYYAH), domin cikin sunnah ma suna da wannan a rubuce. 

Idan kuwa yin taqiyyah munafurci ne, to, babu wanda ba munafuki ba kenan cikin mabiyan Shi'ah da Sunnah, domin kowa na da wannan aqida rubuce cikin littafansu wadanda suka yarda da abinda ke cikinsu. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 

(08126385470-08137925034)

20th November, 2020/ 5th Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post