Tambaya Da Amsa: Tambaya A Kan Miyar Kifin Da Ya Haramta A Ci !!



Daga Zaurenmu na Amon na ɗaya. 


Na'am, Sayyid abubuwan da ba'a ci a jikin dabba yayin da aka dafa abinci dashi ko miya shima za'a tsame daga ciki ko kuwa bai halasta a ci abincin ba?

 Da kuma bayanin da kuka kawo dangane da tarwada a miya na cewa za'a cireshi daga miyar ne se a ci. Shine mukeson Sayyid ya haskaka Mana haka a bisa fatawar Sayyid Ka'id dukansu guda biyun.

Nagode


Dukkanin Kifin da ya haramta a ci shine wanda bashi da ɓawon jiki (Scales). Ga maganganun Malamai akan Romon sa ko Miyarsa:


Cin Tarwaɗa da dukkanin kifin da ba shi da sikel - scale - wannan ɓawon jikin - Haramun ne cinsu a Shi'a bisa Ijma'in Malamanmu.


Sai dai kuma yayin da aka yi Miya ko dafa Abinci da Kifin da ya haramta a ci ya halasta a ci ko a sha miyar ko romon kawai babu matsala.


Wallaahul-aalim.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post