@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
LITTAFIN ALLAH NE BABBAN MADOGARA
Saboda tausayi irin na Allah (T) ga bayinsa yasa bai bar komai ba saida yayi bayaninsa cikin Alqur'ani mai tsarki don kada al'ummar Annabinsa (S. A. W. W) ta fada cikin rudani.
Muhammad (S.A.W.W) ya kasance jagora abin koyi wanda ke fassara komai na daga cikin abinda Allah ya aiko shi da shi (Qur'ani) zuwa ga bayinsa. Cikin fassarar da yake yiwa ayoyin littafin Allah za muga babu cin karo a tsakaninsu, duk wata magana da aka ce daga gare shi ne ko daga waninsa matuqar ta ci karo da littafin Allah a kanyi watsi da ita na a riqi abinda yazo cikin littafin Allah.
Sanya baqaqen kaya ga 'yan Shi'ah ya zama abin aibantawa wajen wasu jama'a na musulmi, domin sukan dauke shi tamkar wani babban aikin kafirci ne wanda ke bayyanar da 'yan Shi'ah .
Samun amsar wannan tambaya ba zai yiwu ba har sai mun koma ga Qur'ani don ya zama alqali mai zartar da hukunci.
Allah (S. W. A) na fada cikin Alqur'ani cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
۞يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ خُذُواْ زِينَتَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ وَلَا تُسۡ
" YAA KU 'YA'YAN ADAMU ! KU RIQA ADONKU ZUWA GA KOWANNE MASALLACI, KUMA KUCI KU SHA KUMA KADA KUYI BARNA, DOMIN SHI (Allah) BA YA SON MASU BARNA ."
Malamai sunyi bayani cewa wannan ayar ta sauka ne sakamakon Kafiran Larabawa suna yin dawafi tsirara, shine Allah ya saukar da wannan aya don su kasance suna sanya tufafi kafin suyi dawafi. Sannan kuma suka qara da cewa ayar tana umarni ne da cewa a riqa sanya kayan ado na daga tufafi.
Da aka sami wasu masu qoqarin haramta wani kalan kaya bisa son ransu sai Allah ya qara da cewa,
قُلۡ مَنۡ حَرَّمَ زِينَةَ ٱللَّهِ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَ لِعِبَادِهِۦ وَٱلطَّيِّبَٰتِ مِنَ ٱلرِّزۡقِۚ قُلۡ هِيَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا خَالِصَةٗ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ ٢٣
(FADA MUSU (Yaa Muhammad) ! WANENE YA HARAMTA (kayan) ADON ALLAH WANDA YA FITAR DASHI (musamman) DOMIN (amfanin) BAYINSA DA KUMA TSARKAKA NA DAGA ARZIQI ? KACE, AI SHI ( wannan kayan adon anyi shi ne) DOMIN WADANDA SU KAYI IMANI CIKIN RAYUWAR DUNIYA, KUMA KEBE (gare su) RANAR ALQIYAMA. KAMAR HAKANE MUKE RARRABE AYOYI (daki-daki) GA MUTANE MASU SANI ."
قُلۡ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَ وَٱلۡإِثۡمَ وَٱلۡبَغۡيَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَأَن تُشۡرِكُواْ بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ سُلۡطَٰنٗا وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ ٣٣
(Kuma) " KACE ABIN SANIN KAWAI UBANGIJINA YA HARAMTA (aikata) ALFASHA WADANDA SUKA BAYYANA (qarara) DAGA GARE TA DAMA WADANDA KE BOYE (da ba a bayyanar dasu ba), DA KUMA ZUNUBI DA ZALUNCI BA BISA HAQQI BA. DA KUMA YIN SHIRKA GA ALLAH WANDA BA A SAUKAR DA WATA DAMA (kan yin hakan ba), DA KUMA FADIN ABINDA BAKU SANI BA GA ALLAH ."
(NURR: 31-33)
Nuna godiya ce ma ga Allah ka duba kalan kayan da kake sha'awa ka dinka, domin yana so ya ganka cikin ado wanda zai faranta ma rai da kuma dukkan mai sha'awar irin wannan kalar.
Manzon Allah (S. A. W. W) na,
.
وأخرج الترمذي وحسنه عن عمرو بن شعيب عن أبيه عن جده قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إن الله يحب أن يرى نعمته على عبده».
Tirmidhi ya fitar kuma ya kyautata shi zuwa ga Amruu Bn Shu'aib daga babansa , daga kakansa yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" LALLE ALLAH NA SO YAGA NI'IMARSA AKAN BAYINSA ."
Saboda haka babu wata hujja da mutum zai kawo na cewa sanya baqaqen kaya haramun ne, sai dai in ya samo hujjar daga Shaidan ne.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08126385470)
14th Nov, 2020/