Zaharaddeen Mziag
Faransa ta tattara malamai musulmai 400, an ɗaure kawunan su da sarqa; A lokacin mamayar ta da Chadi a shekarar 1917 Miladiyya.
Lokacin da Faransa ta shiga garin Ghouta na Aljeriya a cikin 1852, ta shafe kashi biyu bisa uku na yawan jama'argarin, ta banka masu wuta, kuma a cikin dare ɗaya.
Faransa ta gudanar da gwaje-gwajen nukiliya 17 a Algeria tsakanin 1960 da 1966, kuma sun haifar da adadi na wadanda abin ya shafa, tsakanin 27,000 zuwa 100,000..kuma tasirin hakan har yau bai gushe ba.
Lokacin da Faransa ta bar Aljeriya a shekara ta 1962, ta dasa ma'adinai sama da miliyan 11 a bayanta fiye da yawan jama'ar Algeria a lokacin.
Faransa ta mamaye Aljeriya tsawon shekaru 132 .. Faransawan sun halaka Musulmai sama da miliyan ɗaya a cikin shekaru 7 na farkon zuwansu da miliyan ɗaya da rabi a cikin shekaru 7 da suka gabata kafin tashinsu.
Masanin tarihin kasar Faransa Jacques Gorky ya kiyasta cewa jimillar wadanda Faransa ta kashe a Algeria daga zuwanta a 1830 har zuwa tashinta a 1962 Musulmai miliyan 10 ne.
Faransa ta mamaye Tunisia tsawon shekaru 75, Aljeriya tsawon shekaru 132, Morocco tsawon shekaru 44, da Mauritania na shekaru 60.
Lokacin da Faransa ta shiga Masar a shahararren yaƙinta, sojojin Faransa suka shiga masallatan tare da dawakansu, kuma suka yi wa mata Aure da ƴan mata fyaɗe a gaban iyalan su.
Sun kasance suna shan giya a cikin masallatan tare da sauya masallatai da dama zuwa gidan dawakansu .
# A karshe, sun ce Musulunci addinin ta'addanci ne, kuma Annabin mu ta'addanci ya koyar wal'iyazu billahi.😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇