@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
YAU MAGANA KAWAI ZAN YI BA TARE DA NASSI BA
Abinda basu gane ba har yanzu shine, yin magana ta gaskiya wacce za ayi ta ba tare da kawo nassi ba ya fi tarin maganganun da za a kawo su cikin nassi wadanda aka gina su da qarya.
Ilimi ya tabbatar da cewa an qirqiro riwayoyi masu yawa na qarya don nemawa wani daraja/falala yayin da aka qirqiro wasu don danne matsayi da darajar wasu. Wannan dalili yasa Annabi (S. A. W. W) ya tsinewa masu qirqirar qarya su dangatata da shi don cimma wata manufa tasu.
Abinda nake son kawowa anan shine, cikin rubuce-rubucen magabata wanda na yanzu suka doru a kansu suna yadawa shine wai muslimci ya sami cigaba ne a daidai lokacin da Umar Ibn Khaddab ya muslimta saboda jaruntakarsa da kuma dukiyarsa.
Shekaranjiya nake jin wani malami yana jawabi a wajen taron Maulidi wai babu jarumi kamar Umar cikin Sahabbai wanda muslimci ya sami daukaka ta hanyar muslimtarsa. Shine wanda ya jagoranci muzahara a Makkah don bayyanar da muslimci a sarari.
Har ma wasu suka qara cikin rubuce-rubucensu cewa Shaidan na tsoronsa ta yadda ba ya yarda su hada hanya dashi, kuma duk inda yake ba a samun Shaidan a gurin, amma kuma Annabi (S. A. W. W) wanda suka ce an tsaga qirjinsa an cire rabon Shaidan yana da Shaidaninsa wanda yake qoqarin kautar dashi, sai dai kawai yafi qarfinsa ne.
Da ace wannan magana haka take ta tabbata da ba zan ce komai ba, domin jayayya ko kuma qoqashin lullube wata daraja ko falala ta wani hassada ce, sai dai shakkun da nake yi cikin wannan magana yasa na bude baki tare dora alqalami don cewa wani abu kan wannan al'amari.
TAMBAYA
Dole na bijiro da wasu tambayoyi don neman amsa daga masana. Ga tambayoyin nan kamar haka :-
(1)- Duk da wannan jaruntaka tasa me yasa ya riqa gudu a filayen yaqi aqalla guda uku (3) yayin da wasu suka dake ?
(2)- Me yasa ba a taba kawo sunan wani jarumi daga kafirai wanda aka ce shi ya kashe shi ba ?
(3)- Shin menene yake sa mutane juyawa a filin yaqi abar Annabi (S. A. W. W) in ba Shaidan ba ? Ko bai sami wannan jaruntakar tasa bace sai bayan wadannan yaqoqi ?
(4)- Tunda jarumi ne me yasa bai taba fitowa cikin mutane uku dake fara gwabzawa (physical combat) da kafirai kamar yadda take a al'adar larabawa wajen yaqi ba ?
(5)- Me ya hana shi fitowa ya tunkari Amru Bn Abdul-Wud yayin da ya fito yana iqirari a yaqin Khandaq ba?
(6)- Yanzu wanda tarihin jaruntarsa ta bayyana qarara cikin rubuce-rubucen magabata bai fi cancanta a ambace shi a matsayin jarumin jarumai ba ?
Zan taqaita tambayoyin nawa anan don kada yawan amsoshinsu su gagare ni karantawa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
19th November, 2020/ 4th Rabi'us-Sani, 1442.