Sirruka Biyar (5) Game Da Samun Mijin Aure Ga Diya Mace !!!


 

Daga Taskar Sirruka: Na Sayyid Abdullahi Ashura:


Akwai fa'idodi masu tasiri da qarfin gaske dangane da matsalar rashin Auruwa ga ‘ya mace, wanda an jarraba su kuma an ga biyan buqata. Ga kadan daga ciki


KHATAMAR SAYYIDA ZAINAB (S):

Ana yin wannan ‘Khatam’ na Sayyida Zainab (SA) don samun mijin Aure ga mace cikin gaggawa. Sati hudu ake yin aikin amma ba kullum ba, wato duk ranar Talata ake yi, macen da ke son yin auren za ta yi Alwala ta zauna ta fuskanci Alqibla, ta yi wannan wuridi;-


1. Allahummah Swalli Ala Muhammadin Wa’aali Muhammad. (Sau 100).

2. Ya Hayyu Ya Qayyum. (Sau 100).

3. Allahummah Shaafiy Kulla Mareedh. (Sau 100).

4. Assalamu Alaiki Yaa Zainab Binti Amirul Muminin. (Sau 100).


In kin kammala sai ki yi Tawassuli da Sayyida Zainab jikar Manzon Allah (S) ‘yar Sayyida Fatimah Azzahra (SA), ki roqi Allah don alfarmarta da isarta da tsarkinta, ya cika miki burinki na yin aure da samun miji nagari, za ki yi hakan ne cikin halin marairaicewa da qanqantar da kai, in zai yiwu ma ki yi kuka, ki nemi Allah ya kawo miki mijin aure nagari. Haka za a yi duk ranar Talata har Talata hudu a jere, kuma ana so ya zamo a lokaci iri daya ake yin aikin. Zai yi kyau in za a riqa yin sadaka da abin da ya sauwaqa a duk ranar da aka yi aikin.


TAMBIHI:

Ba dole ne sai mace ta yi aikin da kanta ba, wani zai iya yi mata in har ba za ta iya ba, amma shi ma zai aikata duk abubuwan can da aka fada a baya. Sannan idan mace ta fara yi, to ko halin rashin tsarki ya bijiro mata (Haila) za ta iya ci gaba da yi har ta karasa. Sannan idan mace ta yi sau daya ta ga jinkiri, tana iya maimaitawa har sau uku, tabbas za ta samu mijin aure da izinin Allah!


SIRRIN SAMUN MIJIN AURE A RUBUTUN SURATU MARYAM:


Wata fa'ida da aka sha jarrabawa wajan samun mijin aure ga mace ita ce rubuta Suratul Maryam. Wato duk ranar Alhamis a yi Alwala a rubuta Suratu Maryam a wanke, sai mai matsalar ta sha ruwan rubutun, amma za ta rage kadan ta shafe kai da jikinta da shi, idan ta shafe ba za ta goge ba, wato za ta bar ruwan rubutun ya bushe a jikinta da kansa, haka za ta yi tsawon Alhamis uku a jere, Allah zai kawo mata mijin aure ba tare da dogon jinkiri ba.


SIRRIN SAMUN MIJIN AURE TA HANYAR SADAKA DA DABINO:


An ruwaito a Madrasa ta Ahlul-Bait (AS) cewa;- Idan budurwa ta kai munzalin aure, kuma ba ta samu miji ba, to a samu Dabino mai kyau mai tsafta, sai a lissafa shekarunta na haihuwa, sai a warewa kowace shekara Dabino kwaya 12, misali; in shekarunta 20 ne, to kenan za a samu kwayar Dabino 240.


Sai a hada dabinon waje daya, a yi Alwala a zauna a wuri mai tsafta inda ba hayaniya, a sa dabinon a gaba a karanta Suratul Fathi, wato ‘Innaa Fatahna Laka Fathan Mubeena”, da kuma Suratu Yaseen, da “Izajaa’a Nasrullahi”, sai a daga hannu a roqi Allah ya kawo mijin aure nagari da gaggawa, a tofa a dabinon, sai a rabar da shi ga mabuqata.


(In da hali ya zama ranar Alhamis ne za a yi wannan aikin), to washe gari Juma’a sai a yi Alwala (ba tare da Dabino ba), a samu wuri mai natsuwa a zauna a karanta Suratu ‘Daha qafa 3, kullum a yi haka har tsawon kwana 7 a jere, wato zuwa ranar Alhamis kenan. To bi’izinillahi yarinyar za ta samu mijin aure da gaggawa.


A lura, a ranar farko ne kawai za a yi amfani da Dabino, sauran ranakun karatun suratu ‘Daha kawai za a karanta, sannan cikin kwanakin addu’ar ana so a rinka sadaka da abin da ya sauwaqa. Wannan fa’ida an sha jarraba ta ana samun biyan bukata.


TAMBIHI:

Budurwa da Bazawara duk za su iya aiki da wannan laqani, sannan mace za ta iya yi wa kanta wannan addu’a ba sai lallai iyaye sun yi mata ba, kuma ana iya hadawa duka biyun, wato iyaye su yi, kuma ita ma ta yi, sannan idan an fara da tsarki, to ko daga baya halin rashin tsarki ya bijiro (Haila) bai bata aikin ba, za a ci gaba har a karasa. In wani dalili ya sa an ga jinkirin biyan bukata, to ana iya maimaitawa har sau 3.


SIRRIN TSAYAR DA MANEMI GA MACE:


Malam a taimaka mun wani abu na damu na. Na jima da kaiwa shekarun aure, amma duk saurayin da ya zo nema na, sai magana ta yi nisa sai ya gudu, kullum maganar aurena sai tabarbarewa take yi. Malam ina so ne a ba ni addu'ar tsayar da mai nema na, wato addu'ar da za ta sa duk wanda ya zo wajena ya tsaya mu yi aure da shi, ba daga baya ya tsere ba. Ina fata za a share mun hawaye!! Zainab


AMSA: Shaikh Abu Aliy Sina'a yana cewa; Idan mace ta rasa tsayayyen mijin Aure, to a rubuta mata Suratur Rahman, sai a Rubuta sunanta a qarshen rubutun, sannan sai a Rubuta wannan Addu'ar, shi ma sai a rubuta sunanta a wurare biyun da ke cikin baka, ga shi kamar haka;-


Yaa Jama’atar Rijaal, Salabtu Uqulakum (Sunanta) Kasalabatut Tamrati Min Shajaratiha, Walhabbati Min Akmamiha, Wa’alqaitu Alaikum Mahabbatan Minniy, Wa Addfan, Wahananan, Wa’ishqan, Watahyijan Laa ‘Daaqata Lakum Bil-Julusi Walaa Bil-Qu’udi Hatta Yatazawwajaha Ahadun Minkum, Wa’abdalat Ta’adiylaha, Wabaana Tazwiyjaha. Yaa Hala’an Laafiyhi Kawahul Azwaajur Rauhaniyya Assakinatu fiy Qulubil Ajnabiyeena Fayanzuru Ila (Sunanta).


يا جماعة الرجال سلبت عقولكم(sunanta)كسلبت التمرة من شجرتها والحبة من اكمامها وألقيت عليكم محبة مني وعطفا وحنانا وعشقا و تهييجا لا طاقة لكم با الجلوس ولا بالقعود حتى يتزوجها أحد منكم وأبطلت تعطيلها وبان تزويجها يا هلعا لا فية حوكوا الأزواج الروحانية الساكنة فى قلوب الأجنبين فينظروا إلى(sunanta )


Za a yi wannan rubutun ne ranar Juma’a, sai a wanke rubutun a ajiye, sai ranar Lahadi sai ta yi wanka da shi a inda ruwan ba zai gangara ya hadu da najasa ba, kuma bayan kammala wankan ba za a goge jiki da tawul ba. Bayan ta yi wankan, sai ta karanta (ko a karanta mata) wadannan ayoyi biyu na suratu YUNUS (aya ta 81 da 82) qafa bakwai;-


“Qala Musa Maaji’itum Bihis Sihru, Innallaha Sayubdiluh, Innallaha Laayuslihu Amalal Mufsideen. Wayuhiqqullahul Haqqa Bikalimatihi, Walau Karihal Mujrimoun”.


قال موسى ما جئتم به السحر إن الله سيبطله إن الله لا يصلح عمل المفسدين، ويحق الله الحق بكلماته ولو كره المجرمون،


Shi kenan, Insha Allah mai aurenta zai zo da gaggawa kuma za a yi auren da izinin Allah. In bisa wani dalili an ga jinkiri, to ana iya maimaitawa har sau uku. Wannan addu’a an sha jarraba ta ana ganin biyan bukata da gaggawa!


ADDU’AR SAMUN MIJI GA BUDURWA:

Ya zo a ruwayoyi cewa; Idan budurwa ta isa aure amma ba ta samu miji ba, to a riqa yi mata (kuma ita ma ta riqa yin) wuridin wannan ayar ta Suratul … aya ta 134, akalla qafa 70 ko 100 a kowace rana, ga ayar;-

“Innallazhiyna Yatluna Kitaballahi, Wa’aqamus-Salata, Wa’anfaqu Mimma Razaqnahum Sirran Wa’alaniyatan, Yarjuna Tijaratan Lan Tabour!”.

Haka nan, duk macen da take karantawa ko ake karanta mata ‘Suratut-Talaaq’ qafa 21 kullum, da nufin Allah ya kawo mata masoyi wanda zai aureta, to za ta samu mijin aure ba da dadewa ba Insha Allah! Wannan sirrin ma an sha jarraba shi ana dacewa.


Rairayowa da Fassarawa:

Adamun Adamawa

080-3258-5734.

6 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Muna gdy Allah Kara basira

    ReplyDelete
  2. Mun gode Allah ya saka

    ReplyDelete
  3. Masha Allah.
    Allah Ubangiji y saka d mafificiyar gd a Aljannah

    ReplyDelete
Previous Post Next Post