@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KO KUN SAN AYAR GANAWA DA ANNABI (S. A. W. W) ?
Imam Ali (A. S) ya kebanta (he is supreme) wajen darajoji daga dukkan sauran 'yan'uwansa Sahabbai, domin duk wata falala tasa da aka kawo za kaga bata shafi cin mutuncin Annabi (S. A. W. W) ba.
Duk wani umarnin da Allah yayi cikin Alqur'ani ya aikata su ba tare da yin shakku ko tsoron aikatawa ba. Akwai wata aya qwaya daya rak wacce ta gagari dukkan wani Sahabi aikatawa, ko da kuwa me ya tara na dukiya.
Wannan aya tazo ne cikin SURATUL-MUJADALAT, kuma Imam Suyudi yayi sharhi a kanta cikin Tafsir nasa mai suna DURRUL-MANSUR.
Ga ayar nan biye Insha Allah.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
﴿ {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِذَا نَاجَيْتُمُ الرَّسُولَ فَقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَةً ذَلِكَ خَيْرٌ لَكُمْ وَأَطْهَرُ فَإِنْ لَمْ تَجِدُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ (12)
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! IDAN ZA KU GANA DA MANZO KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TAKU (don neman tabarruki da girmamawa) . HAKAN SHINE MAFI ALKHAIRI GARE KU DA KUMA TSARKI, IDAN KUWA BA KU SAMI (abin yin sadaqar ba), TO, ALLAH MAI GAFARA NE (kan wannan gazawar taku) KUMA MAI JIN QAI NE ."
أَأَشْفَقْتُمْ أَنْ تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَاتٍ فَإِذْ لَمْ تَفْعَلُوا وَتَابَ اللَّهُ عَلَيْكُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآَتُوا الزَّكَاةَ وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَاللَّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ (13)} ﴾
" KO TSORO KUKE JI DA KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TAKU ? TO, IDAN BA KU AIKATA BA (saboda tsoro) ALLAH YA KARBI TUBANKU (na wannan gazawar). KU TSAIDA SALLAH KUMA KU BAYAR DA ZAKKAH, KUMA KUYI BIYAYYA GA ALLAH DA MANZOSA, ALLAH MAI BADA LABARI NE GAME DA ABINDA KUKE AIKATAWA ."
۞۞۞۞۞۞۞
أخرج ابن المنذر وابن أبي حاتم وابن مردويه عن ابن عباس في قوله: {إذا ناجيتم الرسول} الآية قال: إن المسلمين أكثروا المسائل على رسول الله صلى الله عليه وسلم حتى شقوا عليه، فأراد الله أن يخفف عن نبيه صلى الله عليه وسلم، فلما قال ذلك: امتنع كثير من الناس وكفوا عن المسألة فأنزل الله بعد هذا {أأشفقتم} الآية فوسع الله عليهم ولم يضيق.
Ibn Munziri da Ibn Abiy Haateem da Ibn Mardawihi sun fitar daga Ibn Abbas cikin fadinsa :
" IDAN ZA KU GANA DA MANZO ." Aya, yace,
" Lalle musulmi sun yawaita yin tambaya ga Manzon Allah (S. A. W. W) har hakan yayi qunci a kansa, sai Allah yayi nufin ya sauqaqawa Annabinsa (S. A. W. W). Yayin da ya fadi hakan sai mutane da yawa suka hanu (saboda tsoron bada sadaqa), sai suka kame daga (yawan) yin tambayoyi, sai bayan haka Allah ya saukar da;
" SHIN, TSORO KUKE JI ?"
Sai Allah ya yalwata a kansu basu sami qunci ba.
وأخرج ابن أبي شيبة وعبد بن حميد والترمذي وحسنه وأبو يعلى وابن جرير وابن المنذر وابن مردويه والنحاس عن علي بن أبي طالب قال: «لما نزلت {يا أيها الذين آمنوا إذا ناجيتم الرسول فقدموا بين يدي نجواكم صدقة} الآية قال لي النبي صلى الله عليه وسلم: ما ترى ديناراً قلت: لا يطيقونه، قال: فنصف دينار، قلت: لا يطيقونه، قال: فكم قلت شعيرة؟ قال: إنك لزهيد، قال: فنزلت {أأشفقتم أن تقدموا بين يدي نجواكم صدقات} قال: فبي خفف الله عن هذه الأمة».
Ibn Abiy Shaibata da Abdu Bn Humaid da Tirmidhi sun fitar kuma suka kyautata shi, da Abu Ya'ala da Ibn Jareer da Ibn Munziri da Ibn Mardawihi da Nuhas sun fitar daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib yace, yayin da aka saukar;
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! IDAN ZA KU GANA DA MANZO KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TAKU. "
Sai Annabi (S. A. W. W) yace min,
" ME KAKE GANI GAME DA (yin sadaqa) DINARE ?" Nace, ba za su iya ba. Yace ,
" RABIN (half) DINARE FA ?" Nace, ba za su iya ba . Yace,
" TO, NAWA NE (ya kamata suyi da shi)? Nace, Sha'ir (ya kamata su bayar). Yace,
" LALLE KAI MAI GUDUN DUNIYA NE ." Yace, sai aka saukar;
" SHIN, TSORO KUKE JI DA KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TAKU ?" (Imam Ali) yace,
" TA DALILINA AKA SAUQAQA WANNAN AYA (ga wadanda suka ji tsoro suka gagara). "
وأخرج عبد الرزاق وعبد بن حميد وابن المنذر وابن أبي حاتم وابن مردويه عن علي قال: ما عمل بها أحد غيري حتى نسخت وما كانت إلا ساعة يعني آية النجوى.
Abdurrazaq da Abdu Bn Humaid da Ibn Munziri da Ibn Abiy Haateem da Ibn Mardawihi sun fitar daga Aliyu yace,
" BABU WANI DA YAYI AIKI DA ITA (ayar) KOMA BAYANA HAR AKA SOKETA , KUMA BATA KASANCE BA FACE NA LOKACI ." Yana nufin ayar ganawa.
وأخرج سعيد بن منصور وابن راهويه وابن أبي شيبة وعبد بن حميد وابن المنذر وابن أبي حاتم وابن مردويه والحاكم وصححه عن عليّ قال: إن في كتاب الله لآية ما عمل بها أحد قبلي، ولا يعمل بها أحد بعدي آية النجوى {يا أيها الذين آمنوا إذا ناجيتم الرسول فقدموا بين يدي نجواكم صدقة} كان عندي دينار فبعته بعشرة دراهم، فكنت كلما ناجيت النبي صلى الله عليه وسلم قدمت بين يدي درهماً، ثم نسخت فلم يعمل بها أحد فنزلت {أأشفقتم أن تقدموا بين يدي نجواكم صدقات} الآية.
Sa'eed Bn Mansur da Ibn Rawaihi da Ibn Abiy Shaibata Abdu Bn Humaid da Ibn Munziri da Ibn Abiy Haateem da Ibn Mardawihi da da Haakeem sun fitar kuma sun inganta shi daga Aliyu yace,
" LALLE CIKIN LITTAFIN ALLAH AKWAI WATA AYA, BA A SAMI WANI DA YAYI AIKI DA ITA GABANINA BA, KUMA BABU WANDA ZAI YI AIKI DA ITA A BAYANA . AYAR GANAWA. "
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! IDAN ZA KU GANA DA MANZO KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TAKU ."
" Ya kasance a wajena akwai Dinare, sai na canza shi zuwa Dirhami goma, na kasance idan zan gana da Manzo sai na gabatar da dirhami gabaninsa, sannan aka soketa. Babu wani da ya aikata ta, sai aka saukar,
" SHIN, TSORO KUKE JI DA KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TAKU ?"
وأخرج عبد بن حميد وابن المنذر وابن أبي حاتم عن مجاهد قال: نهوا عن مناجاة النبي صلى الله عليه وسلم حتى يقدموا صدقة فلم يناجه إلا عليّ بن أبي طالب، فإنه قد قدم ديناراً فتصدق به، ثم ناجى النبي صلى الله عليه وسلم فسأله عن عشر خصال، ثم نزلت الرخصة.
Abdu Bn Humaid da Ibn Munziri da Ibn Abiy Haateem sun fitar daga Mujaheed yace,
" An hane mu ganawa da Annabi (S. A. W. W) har sai mun gabatar da sadaqa, babu wanda ya (iya) ganawa dashi sai Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S), domin shi ya gabatar da Dinare yayi sadaqa da shi, sannan ya gana da Annabi (S. A. W. W) ya tambaye shi abubuwa goma (lokaci daban-dabam). Daga nan aka saukar da rangwame. "
وأخرج سعيد بن منصور عن مجاهد قال: كان من ناجى النبي صلى الله عليه وسلم تصدق بدينار، وكان أول من صنع ذلك علي بن أبي طالب، ثم نزلت الرخصة {فإذ لم تفعلوا وتاب الله عليكم}.
Sa'eed Bn Mansur ya fitar daga Mujaheed yace,
" Ya kasance wanda ya gana da Annabi (S. A. W. W) yayi sadaqa da Dinare, ya kasance farkon wanda ya aikata (hakan) shine Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S). Sa'an nan aka saukar da.rangwame .
" IDAN BA KU AIKATA BA ALLAH YA KARBI TUBANKU.... "
وأخرج ابن أبي حاتم عن مقاتل قال: إن الأغنياء كانوا يأتون النبي صلى الله عليه وسلم فيكثرون مناجاته، ويغلبون الفقراء على المجالس، حتى كره النبي صلى الله عليه وسلم طول جلوسهم ومناجاتهم، فأمر الله بالصدقة عند المناجاة، فأما أهل العسرة فلم يجدوا شيئاً، وكان ذلك عشر ليال، وأما أهل الميسرة فمنع بعضهم ماله وحبس نفسه إلا طوائف منهم جعلوا يقدمون الصدقة بين يدي النجوى، ويزعمون أنه لم يفعل ذلك غير رجل من المهاجرين من أهل بدر فأنزل الله: {أأشفقتم} الآية.
Ibn Abiy Haateem ya fitar daga Maqqatil yace, lalle mawadata sun kasance suna jewa Annabi (S. A. W. W) su yawaita ganawa da shi, suyi rinjaye kan faqirai akan zama da shi, har Annabi (S. A. W. W) ya qyamaci tsohon zaman nasu (da suke yi) da kuma ganawarsu, sai Allah yayi umarni da yin sadaqa yayin ganawar. Su kuwa ma'abota qunci basu sami komai ba, hakan kuwa ya kasance ne na tsohon kwana goma. Amma su kuwa masu yalwa sai sashensu suka riqa hana sashe dukiyarsa, suka tsare kawukansu sai wani daga cikinsu yake gabatar da sadaqa gabanin ganawar. Su kuma suna riyawa cewa shi babu wanda ya aikata haka koma bayan wani daga cikin Muhajiruun daga wadanda suka halarci (yaqin) Badr. Sai Allah ya saukar da,
" SHIN, TSORO KUKE JI.... "
Mun taqaita riwayoyin anan haka don sauqaqawa masu qoqarin bibiyarmu cikin shauqi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
10th November, 2020/ 24th Rabi'ul-Awwal, 1442.