Shekaru 64 Da Fara Yin Maulidi A Garin Guda, Ningi !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SHEIKH ABUBAKAR YUNUSA NINGI YA KAFA TAHIRI MAI KYAU 


Harkar Maulidin Manzon Allah (S. A. W. W) ya zama abu mafi girma wajen yaduwa/cigaba (improvement) a wannan nahiya tamu. Shine wanda a kowacce shekara ake samun qaruwar jama'ah masu goya masa baya tare da qoqarin dabbaqa shi a gidajensu ko fitowa suyi tarayya da masu aiwatarwa. 


Duk da sukar da yake samu daga bakunan maqiyan Manzon Allah (S. A. W. W) amma hakan bai hana shi cigaba cikin kowacce shekara ba, kuma bai hana masu sukar su fito suna kallon masu zagayen murnar samuwar fiyayyen halittar ba.


Sheikh Abubakar Yunusa Ningi da ke jihar Bauchi fitaccen malamin Qadiriyya ne wanda ya fara raya al'amarin Maulidin Manzon Allah (S. A. W. W) shekaru 64 da suka gabata a qasar Ningi, kuma a cikin garin Guda 4km daga cikin garin Ningi .


Shehin malamin ya fara raya maulidin ne yayin da yake koyarwa a primary school ta garin Guda, ta hanyar tattara daliban ya jagorance su a qafa (Tattaki) zuwa cikin garin Ningi. Tun suna yi basu wuce mutane 25 ba, yanzu Allah ya fadada harkar ta yadda dubban al'umma ce ke fitowa ranar 12 da 19 ga watan Rabi'ul-Awwal suna zagaya gari. Sannan kuma tun daga ranar 12 ga watan har watanni biyu da ke biyo shi su qare ba a samun ranar da za ta wuce ba tare da anyi taron Maulidi a wata makarantar islamiyyah ko gidajen mutane a daidaiku ba. 


Shehin malamin na daga cikin malaman da aka taba gayyata don gabatar da lecture a makon hadin kai da ake yi a Zaria kuma ya amsa gayyatar, sai dai Allah bai bashi ikon halarta ba sakamakon waqi'ar data auku a garin Zaria 2015 wacce tayi sanadin hana yin wannan taro. 


A halin yanzu dai Shehin malamin yana fama da rashin lafiya, kuma yana buqatar addu'ah daga bakunan masoya Manzon Allah (S. A. W. W) don fatan samun sauqi ya cigaba da wannan aiki nasa wanda ladarsa ba za ta yanke ba ko da bayan rayuwarsa ce, domin ya dasa wannan soyayya ta Ma'aiki cikin zukatan mutane, kuma suna raya ta a aikace. 


Wannan hoto da kuke gani na chairman din mawaqa (Sha'irai) ne na qasar Ningi ke gabatar da waqen yabon Manzon Allah (S. A. W. W) a wajen taron Maulidin da aka gabatar jiya 17-11-2020 a islamiyyar Saqafatul-Islam dake garin Guda. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


18th November, 2020/ 3rd Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post