A jiya juma'a, 20/11/2020 hukumar gudanarwar babban Asibitin Jihar Kano, Murtala Muhammed Specialist Hospital ta jihar Kano ta bada takardar Shedar gamsuwa da jinjina ga Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Da'irar Kano.
An bada shedar ne sakamakon gudunmawar jinin da Almajiran Shaikh Zakzaky suka saba bayarwa lokaci bayan lokaci, Kuma kamar yadda a yau ma Almajiran Shaikh Zakzaky sun bada jini kyauta ga Asibitin, don ceton rayukan mabukata jini.
A karshen takardar, Hukumar Asibitin ta yi fatan Almajiran Shaikh Zakzaky su karbi wannan yabawan da aka yi masu da hanu biyu.
Irin wannan yabon daman ya saba zuwa daga bangarori daban daban na Al'ummah, albarkacin tarbiyar Shaikh Zakzaky ga Almajiransa na ceton rayukan jama'a.
Wanda a yanzu kuma Buhari na tsare da shi, Shaikh Zakzaky da Iyalinsa, Malama Zeenah a Kurkuku, tun bayan kisan kiyashin Zaria, inda aka kashe Yayansa da kuma Almajiransa sama da dubu.
A halin yanzu ,tattare da harsasai a jikinsu, kuma babu kulawar kwararrun likitoci, sama da shekaru 5 suna tsare a Kurkuku, bayan babbar Kotu a Abuja ta bada umarnin a sake su, tare da biyansa diya