@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ZA A JARRABCI JINSI MUTANE BIYAR A LAHIRA KAFIN YI MUSU HISABI
Allah (T) ya halicci bayinsa ne kawai domin su bauta masa , sai dai kuma cikin wadannan bayi nasa akwai wadanda za ayi musu uzuri ko kuma jarraba su ranar alqiyama kafin yi musu hisabi.
Wasu sun rayu zamanin fatara, wasu kurame/bebaye, yayin da wasu suke marar sa hankali, wasu kuma sukan koma ga Ubangijinsu ne tun suna 'yan jarirai. To, su jinsin wadannan bayi ana yi musu jarrabawa ne ranar alqiyama kafin ayi musu hisabi, a wata riwayar kuma aka ce Allah kadai yasan yadda zai yi dasu.
Yazo cikin Tafsirul-Qummy cikin fadin Allah (T);
تفسير القمي قَوْلُهُ
" وَ الَّذِينَ آمَنُوا وَ اتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُمْ بِإِيمانٍ أَلْحَقْنا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ ."
" KUMA WADANDA SU KAYI IMANI KUMA ZURIYARSU TA BI SU DA IMANI, TO, ZA MU RISKAR DA ZURIYARSU GARE SU... "
yace,
فَإِنَّهُ حَدَّثَنِي أَبِي عَنْ سُلَيْمَانَ الدَّيْلَمِيِّ عَنْ أَبِي بَصِيرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ أَطْفَالَ شِيعَتِنَا مِنَ الْمُؤْمِنِينَ تُرَبِّيهِمْ فَاطِمَةُ ع قَوْلُهُ أَلْحَقْنا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ قَالَ يُهْدَوْنَ إِلَى آبَائِهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَ قَالَ عَلِيُّ بْنُ إِبْرَاهِيمَ فِي قَوْلِهِ وَ ما أَلَتْناهُمْ مِنْ عَمَلِهِمْ مِنْ شَيْءٍ أَيْ مَا نَقَصْنَاهُمْ.
Yace shi babana ya bani labari daga Sulaiman Al-Dailamiy, daga baban Basir, daga Abu Abdullahi (A. S) yace,
" LALLE JARIRAN 'YAN SHI'AR MU (mabiyan mu) DAGA MUMINAI FADIMATU (S. A) CE ZA TA RENE SU. "
Fadinsa (T) cewa, " ZA MU RISKAR DA ZURIYARSU GARE SU ." Yace,
" ZA A SHIRYAR DASU NE ZUWA UBANNINSU RANAR ALQIYAMA. "
Aliyu Bn Ibrahim (Al-Qummiy) ya fada cikin Fadinsa, " BA ZA MU TOZARTAR DA WANI ABU DAGA AYYUKANSU BA ." Abin nufi shine, ba za mu tauye musu ba.
(Wannan na qara tabbatar mana adalcin Allah ne, komai qanqantar abinda mutum ya aikata na alkhairi zai ga sakamakonsa).
RIWAYA TA BIYU
2- الخصال أَبِي عَنْ مُحَمَّدٍ الْعَطَّارِ عَنِ الْأَشْعَرِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ إِسْمَاعِيلَ عَنْ حَمَّادٍ عَنْ حَرِيزٍ عَنْ زُرَارَةَ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ:
Daga Muhammad Addariy, daga Ash'ariyyu, daga Aliyu Bn Isma'il, daga Hammad, daga Hariz, daga Zurarata, daga Abu Ja'afar (A. S) yace,
إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ احْتَجَّ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ عَلَى خَمْسَةٍ عَلَى الطِّفْلِ وَ الَّذِي مَاتَ بَيْنَ النَّبِيِّينَ وَ الَّذِي أَدْرَكَ النَّبِيَّ وَ هُوَ لَا يَعْقِلُ وَ الْأَبْلَهِ[2] وَ الْمَجْنُونِ الَّذِي لَا يَعْقِلُ وَ الْأَصَمِّ وَ الْأَبْكَمِ فَكُلُّ وَاحِدٍ مِنْهُمْ يَحْتَجُّ عَلَى اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ قَالَ فَيَبْعَثُ اللَّهُ إِلَيْهِمْ رَسُولًا فَيُؤَجِّجُ لَهُمْ نَاراً فَيَقُولُ لَهُمْ رَبُّكُمْ يَأْمُرُكُمْ أَنْ تَثِبُوا فِيهَا فَمَنْ وَثَبَ فِيهَا كَانَتْ عَلَيْهِ بَرْداً وَ سَلَاماً وَ مَنْ عَصَى سِيقَ إِلَى النَّارِ.
" IDAN RANAR ALQIYAMA TAZO ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA ZAI YI JARRABAWA AKAN (jinsin mutane) BIYAR. Akan :
- JARIRAI, da
- WANDA YA MUTU A TSAKANIN ANNABAWA BIYU, (Annabin farko ya rasu kuma ba a aiko na biyu ba),
- WANDA YA RISKI ANNABI AMMA BA YA FAHINTAR KOMAI (saboda yarinta),
- BUGUN ALJANI WANDA BA YA DA HANKALI ,
- KURMA/BEBE.
KOWANNE 'DAYA DAGA CIKIN SU ZA SU BUQATU ZUWA GA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA ."
Yace,
" SAI ALLAH YA AIKO DA MANZO ZUWA GARE SU YA BIJIRO MUSU DA WUTA, SAI YACE MUSU, UBANGIJIN KU NA UMARTAR KU DA CEWA KU FADA CIKIN TA. WANDA YA FADA CIKINTA SAI SANYI DA AMINCI YA KASANCE A KANSA (memakon zafin wutar), WANDA KUMA YA SABA SAI A KORA SHI CIKINTA (ya nuna cewa shi dan tawaye ne ga Manzo) ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج5، ص: 290
Wadannan riwayoyi na gaskata fadin Allah (T) inda yake cewa,
" BA MU KASANCE MUNA YIN AZABA (ga wani ba) HAR SAI MUN AIKO DA MANZO (ya qaryata shi) ."
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
30th November, 2020/ 15th Rabi'us-Sani, 1442.