Samun Yaqini Na Sama Da Taqawa A Daraja !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BISA YAQINI NAKE YIN KOYI DA GIDAN IYALAN ANNABI (S. A. W. W) 


Muslimci shine addini kammalalle wanda Allah ya yarjewa bayinsa, kuma duk wani addini da ka riqa koma bayan muslimci ba zai kaika ga samun tsira ranar alqiyama ba. 


Muslimci shine matakin farko wanda ya kamata a taka a matsayin tsani (ladder) na zuwa ga Allah, sai dai imani da taqawa da yaqini sun fi shi matsayi da daraja wajen Allah (T). 


Zama mutum musulmi ba komai bane idan babu imani, hakama imani in babu taqawa, samun taqawa ba yaqini kuwa akwai naqasu cikinsa . Saboda haka duk wani abinda za ka yi shi matuqar babu yaqini cikinsa ya zama aiki naqasasshe. 


An sami mutane da yawa da suka rayu tare da manzon Allah (S. A. W. W) cikin muslimci, amma muslimci nasu bai zame musu katanga daga shiga wuta ba. 



2- كا، الكافي عَنِ الْعِدَّةِ عَنْ سَهْلٍ وَ الْحُسَيْنِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنِ الْمُعَلَّى جَمِيعاً عَنِ الْوَشَّاءِ عَنْ أَبِي الْحَسَنِ ع قَالَ سَمِعْتُهُ يَقُولُ‏:


Yazo cikin Kafiy daga Iddati daga Sahal da Hussaini Bn Muhammad , daga Mu'allah gaba daya daga Wassha'i daga baban Hassan (A. S) yace, na ji shi yana cewa, 


 الْإِيمَانُ فَوْقَ الْإِسْلَامِ بِدَرَجَةٍ وَ التَّقْوَى فَوْقَ الْإِيمَانِ بِدَرَجَةٍ وَ الْيَقِينُ فَوْقَ التَّقْوَى بِدَرَجَةٍ وَ مَا قُسِمَ فِي النَّاسِ شَيْ‏ءٌ أَقَلُّ مِنَ الْيَقِينِ‏[36].



" SHI IMANI YANA SAMA DA MUSLIMCI A DARAJA, KUMA TAQAWA NA SAMA DA IMANI A DARAJA , SANNAN YAQINI NA SAMA DA TAQAWA A DARAJA . BABU WANI ABU MAFI QARANCI DA AKA RABA SHI TSAKANIN MUTANE KAMAR YAQINI ."



      (1) الكافي ج 2 ص 51.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏67، ص: 137


Wannan hadisi na karantar damu ne cewa, za a iya samun musulmi da masu imani da taqawa masu yawa cikin mutane, amma kuma sai masu yaqini su qaranta. 


Yanzu mutum zai iya muslimta kuma yayi imani cewa Allah ne ya halicce shi kuma ya aiko da Muhammad (S. A. W. W) a matsayin dan saqo, amma kuma sai ya kasance ba shi da yaqini kan abinda Allah ke fada na sakamakon masu yi masa biyayya da kuma azabarsa ga dukkan wanda yayi zalunci ya qarya dokarsa (S. W. A). 


Idan muka koma cikin Qur'ani kuwa don gamsar daku wannan magana za muga ayoyi kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" وَجَعَلۡنَا مِنۡهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا لَمَّا صَبَرُواْۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يُوقِنُونَ ٤٢"


Dangane da Annabi Musa (A. S) bayan littafin da aka ba shi shine Allah ke fadawa Annabi Muhammad (S. A. W. W) labari da cewa, 


" KUMA MUN SANYA SHUGABANNI DAGA CIKINSU, SUNA SHIRYARWA DA UMARNINMU YAYIN DA SUKA YI HAQURI, KUMA SUN KASANCE SUNA YIN YAQINI DA AYOYINMU ."


            (SAJDAH :24)


Wannan na nuna mana ne cewa ba a samun yaqini sai an taka matakai kafin aje gare shi, wato muslimci da imani da taqawa . Samun yaqini shine qololuwa a daraja. 



Dangane da Annabi Ibrahim (A. S) kuwa Allah (T) na cewa, 



" وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ أَرِنِي كَيۡفَ تُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ قَالَ أَوَلَمۡ تُؤۡمِنۖ قَالَ بَلَىٰ وَلَٰكِن لِّيَطۡمَئِنَّ قَلۡبِيۖ قَالَ فَخُذۡ أَرۡبَعَةٗ مِّنَ ٱلطَّيۡرِ فَصُرۡهُنَّ إِلَيۡكَ ثُمَّ ٱجۡعَلۡ عَلَىٰ كُلِّ جَبَلٖ مِّنۡهُنَّ جُزۡءٗا ثُمَّ ٱدۡعُهُنَّ يَأۡتِينَكَ سَعۡيٗاۚ وَٱعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ ٠٦٢"


" (Ka tuna) A LOKACIN DA IBRAHIM YACE, " YAA UBANGIJI KA NUNA MIN YADDA KAKE RAYAR DA MATATTU ." YACE : " SHIN, (har yanzu) BA KAYI IMANI BANE (da abinda nake fada) ?" YACE : " NA'AM (nayi imani 100%) ! SAI DAI KAWAI DON ZUCIYATA TA NUTSU (yaqini). " YACE : " TO, KA RIQI HUDU DAGA CIKIN TSUNTSAYE (mabambanta), KA KARKATAR DASU ZUWA GARE KA, KA YANKA SU (ka daka su), SA'AN NAN KUMA KA SANYA KOWANNE YANKI DAGA CIKINSU AKAN DUTSE (guda hudu), SA'AN NAN KA KIRAYE SU (da sunayensu) ZA SU ZO MAKA SUNA TAFIYA. KUMA KA SANI LALLE ALLAH MABUWAYI NE MASANI ."


             (BAQARA :260)


Kunga anan babu mai musu cewa Annabi Ibrahim (A. S) musulmi ne kuma mumini, amma bai kai matakin samun yaqini ba har saida yaga ayoyin Allah a bayyane. 


Saboda haka ban kai ga matakin amsa kiran Sayyid Zakzaky (H) wanda ke kira qarqashin Wasiccin Manzon Allah (S. A. W. W) ba har sai da na sami yaqini. 


Yanzu hana ina yin aqidata ta Shi'ah ce bisa yaqini. Fatanmu shine Allah ya tabbatar damu kan wannan tafarki tare da bawa jagoranmu kariya daga makircin makirai. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08126385470)


16th November, 2020/ 29th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post