Sahihan Ahlus-Sunnah Cike Suke Da Cin Zarafin Annabi (S.A.W.W) !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KO KADAN BASU SAN DARAJAR ANNABI (S. A. W. W) BA 


Yakan iya zama abin mamaki wani lokaci, amma in ka nazarce su sai kaga komai ma za su iya fada a kansa don basu san wanene Shi (S. A. W. W) ba, ballantana sanin matsayinsa ko haqqinsa a kansu. 


Ka san sai mutum yayi magana kake iya fahintar haqiqanin shi wanene, amma ba don haka ba za ka iya fassara shi ne gwargwadon fahintar da kayi masa. To, su Ahlus-Sunnah sun bude bakunansu sun furta magana, saboda haka kai tsaye mun san su suwanene. 


Don taqaitawa zan kawo abinda nake son isar dashi kai tsaye daga cikin abinda Muslim ke kawowa cikin Sahihinsa. 


Ya kawo shi ne cikin KITABUN-NIKAH, qarqashin Babin da ke cewa, 


ندب من رأى امرأة فوقعت في نفسه إلى أن يأتي امرأته أو جاريته فيواقعها


(LADABIN WANDA YAGA MACE SAI (sha'awa) TA FADO MASA CIKIN RANSA, YA TAFI ZUWA GA MATARSA KUYANGARSA YA AFKA MATA) 


حدثنا عمرو بن علي حدثنا عبد الأعلى حدثنا هشام بن أبي عبد الله عن أبي الزبير عن جابر أن رسول الله صلى الله عليه وسلم رأى امرأة فأتى امرأته زينب وهي تمعس منيئة لها فقضى حاجته ثم خرج إلى أصحابه فقال


Muslim na cewa, Amruu Bn Aliyu ya bamu labari, 

Abdul-A'alah ya bamu labari, Hishaam Bn Abiy Abdullahi ya bamu labari daga baban Zubair daga Jabir cewa, lalle Manzo Allah (S. A. W. W) yaga wata mata (wacce ta bashi sha'awa), sai ya jewa matarsa Zainaba ya biya buqatarsa (na sha'awar data kama shi) , sa'annan ya fita (daga gare ta) zuwa ga Sahabbansa yace, 


" ان المرأة تقبل في صورة شيطان وتدبر في صورة شيطان فإذا أبصر أحدكم امرأة فليأت أهله فإن ذلك يرد ما في نفسه ."


" LALLE ITA MACE TAKAN FUSKANTO (mutane ne) CIKIN SURAR SHAIDAN (Iblis), KUMA TA JUYA (baya) CIKIN SURAR SHAIDAN. (Saboda haka) IDAN 'DAYANKU YAGA MACE (har sha'awarta ta kama shi), TO, YA JEWA IYALINSA, DOMIN HAKAN ZAI KAWAR DA ABINDA YAKE ZUCIYARSA (na sha'awa) ."


Ni wallahi har ma na rasa abinda wannan hadisi ke katantarwa, saboda haka ya zama wajibi nayi tambaya don neman sani. 


               TAMBAYA 

              ___________


(1)- Shin, dama Annabi (S. A. W. W) na kallon mata ne irin kallon da zai bashi sha'awa alhali ya hane mu game da yin haka ?


(2)- Shin, ya akayi aka san cewa Annabi (S. A. W. W) ya sadu da iyalinsa sakamakon wannan sha'awa? 


(3)- Shin, ita Zainab din ce tace da ita ya sadu ko kuma Shi (S. A. W. W) dinne da kansa ya basu labari alhali ya hane mu cewa haramun ne mutum ya biya buqatarsa da matarsa sannan yazo yana bayyanawa mutane alhali Allah ya rufa musu asirinsu ?


(4)- Shin, ko kuna nufin yana umartar mutane ne da alkhairi shi kuma yana mantawa da kansa? " SHIN ZA KU RIQA UMARTAR MUTANE NE DA ALKHAIRI KU KUMA KUNA MANTAWA DA KAWUKANKU ?"


(5)- Ko kuma kuna nufin yana fadin abinda shi ba ya aikatawa ne? " YA GIRMA GA ZAMA ABIN QYAMA A WAJEN ALLAH KUNA FADIN ABINDA BA KWA AIKATAWA ."


" KALMAR DA TAKE FITOWA DAGA BAKINSU TAYI GIRMA, BA KOMAI SUKE FADI BA FACE QARYA !"


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda. 


        (08126385470)


1st November, 2020/ 15th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post