Toh, bayan an shiga da ita din to can anjima haka, kusan karfe uku ko ma ukun, sai na hau online a facebook lite, ina hawa sai na ci karo da post din yayanta: Jamaluddeen kan Allah ya mata rasuwa.
A wannan lokacin shi ne kawai naga yayi post din, sai nake ganin abun kamar gizo-gizo, a lokacin muna zaune da mutane haka, sai naji zuciyata ta fara bugawa hawaye yana shirin fitowa, a wanan lokacin sai na yi maza na tafi daki,na shiga na turo. Zamana ke da wuya, sai na ji hawaye ya zo min, na so in daure hakan bai yuwu minba. Ban dai sauka a Facebook din ba, nan naga Yayanta Mallam Saifullahi shima yayi post, tare da hotonta, ban san lokacin da na fara ihu ba, ina kuka ji nake kamar zuciyata zata fashe, na dau lokaci ina kuka, domin tun daga lokacin da naga rasuwarta, sai da na kai karfe hudu, ina kuka ciki ina fadin "Allah ka gafarta mata" ina kuka dai ina fadin "Allah ka gafarta mata", can na saurara, na hau facebook naga ya cika da hotunanta, anan na ji na kara fashewa da kuka, domin ganin hotunan nan ya sa na tuna irin-rayuwarta da halin girma irin nata.
A wannan lokacin sai na fita na yi alwala, na yi sallar la'asar, na dan yi mata wasu addu'oi, bayan haka sai nace bari na kira Umma na mata ta'aziya, nan dai ban kiraba saboda nasan lokacin hankalinta yana tashe. A lokacin sai na Kira yayanta mu gaisa, na masa ta'aziya, nan na tambaya wana lokaci ne za ayi janazarta, ace gobe da karfe 8 na safe.
Bayan haka, na zo na fita na je wani wuri na raka wani, to na yi kokari dai ban bayyana halin da nake cikiba. Amma da ka ganni kasan ban cikin kwanciyar hankali. Nan dai na fara samun kiran abokan arziki suna ta'aziya,maza da mata. Ciki har da wanda mun dade rabon da mu gaisa.
Mu dawo, to na shiga daki dai na cigaba da kukana, ina rokon Allah ya mata rahma, na kai magriba ina daki, daga nan shima na fita na je na yi sallah, to bayan na dawo na zauna dai, to na ta mata addu'a, a lokacin na dau lokaci mai dama ina zaune ina mata du'a.
A zo dai, na kwanta amma ban samu da na yi bacciba, domin kawai rayuwarmu nake ta tunawa. A haka na kai kwana fiye da biyar kullum in na zauna zan kamo hotonta, to a wanan lokaci hawaye ke fita a idanu na.
Mu wayi garin Monday, na shirya da wuri, kan in je in samu sallar janazarta, na wuce ta gidan Hajiya, sai mu gaisa take cewa :" Ashe kana nan, ai na zata ka koma makarantar ne jiya", sai na ce: Ina nan ai. Sai ta ce, ashe Wannan yarinya Allah ya mata rasuwa. Na ce wallahi lokacinta ya yi, tasha wahala ta yi ciwo sosai. Nan sai Hajiya take cewa na tsaya mu tafi tare ta musu ta'aziya, dama itama zata saminaka yau din (akwai yarinyar aunty mu da suke asibiti), nan dai na ce ni da, zan tafi yanzu ne, ina son in samu sallar janazarta, sai ta ce to bari na yi na shirya mu tafi. Karshe dai ta ce dole na yi hakuri ba zan samu janazarba.
A lokacin sai babban Yayanmu ya shigo, su gaisa take basa labari, yanzu muke shiri zamu tafi saminka, kasan wanan yarinya da Jamilu ya ce da yana so, ta rasu. Ya ce Allah sarki, ai yarinyar mallam kabiru, mutumina ne sosai in mu hadu da shi,muna dadewa tare dashi, shima ya rasu ai. Nan dai ya ce ai ya kamata ku tafi a mota ne, nima an jima zan shiga saminaka sai in wuce in musu ta'aziya.
Nan har suke hira haka, Hajiya take cewa ai yarinyar ta so shi, to ta masa dan girma ne haka, kuma gashi zata yi aure kusa. Nan ya ce Allah sarki! Kilama ai ta girmesa, ko su zo sa'a daya. Sai na ce, sai dai sa'an dai.
Su gama, saboda jiran da na yima Umma ban samu sallar ba, sai bayan haka na samu baya an kaita mu tafi. To bayan da muje mun shiga cikin gidan mun yi gaisuwar ta'aziya ma yayunta da makusanta, bayan nan mun shiga cikin gidan, nanma dai mu musu ta'aziya. Da mu fito sai mu zauna wurin da ake amsar gaisuwar nan harabar gidan kenan.
Da mu zauna, mun dan dau wasu mintoci a wurin amsar gaisawar. A wannan lokacin na ji yayanta mallam Saifullahi yana bada labarin lokacin da jikinta yayi tsanani,har da lokacin da su kasance a asibiti. Lokacin jikina yayi sanyi sosai, a lokacin hawaye naji yana shirin fita, nan dai na daure. A lokacin ya bada labari sosai, wanda maimaita su zai tada min hankali. A lokacin na ji ciwo sosai.
Bayan haka dai, mu ta so zamu wuce, mu kara musu ta'aziya mu wuce. Na zo zan fita sai naga umma a kofan fita, a lokacin zan gaisheta kenan sai ta min magana "Sannunku fa" nan sai na durkusa na gaishe ta, na kara mata ta'aziya. To a wurin nan ma hawaye ya kusan sauka min, zuciyata tana ta bugawa. Saboda ganin yanda umma take son Khaleesat, da irin shakuwar da su yi, amma ta yi tawakkali, ta yi hakuri sosai (lokacin murmushi ma take), wanna ya sa na ji tausayi sosai. Nan dai na ce, zamu tafi. Ta yi godiya! Na ce ba komai umma.
Mutane da dama, sun yi ta'aziya ta WhatsApp da facebook, maza da mata, ni wasu ma ban sansuba. Haka dai na dinga samun ta'aziya. Kusan duk wanda ya santa gaskiya sai ya girgiza da mutuwarta, akwai wata yar Bauchi, ba sister ba ce ma, amma ta san Khaleesat a bakina sosai, domin duk san da ta kiran abun da take kirana da shi kenan "Angon Khaleesat" har wata rana take matsawa akan na mata number Khaleesat su gaisa, to gaskiya in dai zamu gaisa sai ta tambayen ya su Khaleesat. To ta ga a status na saka hoton Khaleesat, sai take cewa wanan ai Khaleesat ta rasu ne! Lokacin da na fada mata ta girgiza sosai (duk da bata taba ganintaba).
Akwai wani abokina, a lokacin muna zaune muna hira wata rana, sai nake basa labarin soyayyarmu, yake cewa:" Gaskiya kuna son junanku, ni ban taba ganin masoya masu tafiyar da soyayyarsu kan tsariba kamarku" a lokacin muna maganar sai Khaleesat ta min flashing, na kirata mu yi hira, sai yake cewa na bashi su gaisa. Sai na bashi, su gaisa sai yake cewa:" Ga abokina nan, amana mu baki, fatan zaki kula dashi, ki lallabasa kamar yadda uwa take kual da lallaba jaririnta ", sai take cewa:" karka damu, ai ya zama nawa, na zama na shi,mijina ne fa" su gama gaisawa. Shima ya girgiza sosai, yanda ya ban labari ya dade bai ji mutuwar da ta girgiza shi kamar na Khaleesat ba (shima bai santaba sai waya su taba yi).
Mutane da yawa sun ji mutuwarta (mutuwar muminai na girgiza mutane), dayake da ta rasu ban samu sukuni hakaba. Wasu ma basu saniba, sai daga baya, har haushi sun ji saboda ban fada musuba.
Akwai wani abokina, a mauludin nabi 2020, Khaleesat ta zo garinmu mun hadu, mun dadema. To lokacin tare dashi muke. To da na fada masa wallahi, ya kasa tsayuwa dole tsugunawa yayi, ya dade yana jinjinawa (sau daya ya taba ganinta).
A iya sanina, mutane da yawa, duk wanda ya ji rasuwar Khaleesat sai ya girgiza, ko da bai taba ganintaba. Balle ya santa.
Khaleesat a rayuwarta tana da kofa, na saurin sabo da ita, kuma tana da hakuri sosai, tana dadewa bata yi fushiba amma in ta yi,tana yi sosai, amma ko da ta yi in dai kana da matsayi gunta kana bata hakuri zata hakura. Ban mantawa akwai wani lokaci da ta ban labari, take cewa wata mata ta mata rashin mutumci, kuma zata sani sai ta ninka mata, a lokacin sai nake bata hakuri, take cewa ina dadewa kafin a gure ni, amma in a gure ni ban wucewa da wuri, gaskiya lokacin na fahimci abun da matan nan da ta yi mata ya bata mata rai sosai. Nan dai na ce, kina ji, ni dai na ce kibarta zai wuce. Fushi ba abun da yake jawowa sai dana sani. Sai take cewa:" Wallahi ta ci sa'a ",sai na yi dariya, na ce ai ni ban san kina da fushi haka ba, sai ta yi dariya.
A mu'amalarta da kawaye, tana da sake fuska. Sau da yawa, in mu yi waya takan bani labarin irin raha da suke. Akwai wata rana take cewa:" yau na je U/bawa, mun je karatu, sai ina zuwa sai su Fateema tun kafin na karisu, wai kaga amayar Jameel , sai na yi dariya na ce; ku fadi ku kara ", a wanna lokacin ne ma har ta min tayin in dinga zuwa to ban samu damaba.
Gaskiya tana da kokari, kan karatun Boko da addini, musamman na addini, take ban labari, har nake cewa ai baki wani samun hutu, har da dare suna karatun Qur'an haka.
Tana da damuwa da mutane sosai. In dai ta sanki, ta ganki ko baki gantaba zata miki magana. Ku gaisa. Gaskiya ita kam, muna kyautata zaton ta dace.
Iyaye, yayu, kannai, kowa da kowa ina godiya da addu'oinku, wadanda su kiran, da wadanda su turo da sako na ta'aziya,duk ina godiya, Allah ya amsa uzurinta, ya gafartawa sauran mamatanmu. Na gode.
Khairan in sha Allah Khaleesaty. Fee amanillah.